'Ni ma mutum ce kamar kowa' - Mai HIV da ke wayar da kan masu cutar

Asalin hoton, Getty Images
Laraba (ba sunata na gaskiya ba) wata matashiya ce da ke zaune a Kaduna wadda tun tana ƙarama aka gano tana ɗauke da cutar HIV, amma duk da haka, ta dalilin samun ƙwarin gwiwa da ta yi daga iyayenta, sai ta ci gaba da rayuwa "kamar kowane ɗan'adam a duniya," domin cika burinta na rayuwa.
Cuta mai karya garkuwar jiki wadda ake kira HIV ko AIDS, cuta ce da take jefa masu ita cikin damuwa, lamarin da ke yin mummunan tasiri ga lafiyarsu.
A wata hira da BBC Hausa, ta ce an gano tana da cutar ne shekaru 15 da suka gabata, bayan ta taka allura a wata hanya kusa da gidansu da ake zubar da shara.
"Na ji zafi a ƙafa amma ban duba sosai ba, daga baya na fara zazzaɓi da rashin lafiya, aka kai ni asibiti, daga nan ne aka gano cewa ina da HIV," in ji ta.
Ta ce lokacin da aka faɗa mata tana ɗauke da cutar, ta shiga damuwa saboda irin kallon da ake yi wa masu cutar, da "irin wariya da tsangwamar da ake musu. A lokacin ana kallon cutar tamkar hukuncin kisa ne," in ji ta.
Ta ce matuƙar mai cutar na shan magani, za su kai matakin da take yanzu, na wanda 'ba za a ga a cutar a jikinsu ba, kuma ba za su yaɗa ta ba'.

Asalin hoton, Getty Images
Rayuwa kamar kowa
Sai dai duk da hakan iyayenta da danginta sun nuna mata ƙauna da goyon baya, suka karɓe ta hannu bibbiyu, lamarin da ya ba ta ƙwarin gwiwa har ta ci gaba da karatu da kuma samun nasarori a rayuwa.
"Soyayyar iyayena da ƴan'uwana ta sa ban karaya ba. Na ci gaba da rayuwa kamar kowanne ɗan'adam. Ni ma mutum ce kamar kowa."
Bayan shan wahala da cutar a tsawon shekaru, yanzu haka matashiyar tana aiki tare da ƙungiyoyi da dama da suka haɗa da Society for Family Health (SFH) da Integrated Health Programs, inda take jagorantar ayyukan wayar da kan mutane masu cutar HIV.
"Ina so ne masu cutar su fahimci cewa akwai mafita, kuma za su iya rayuwa mai kyau kamar kowa idan suna shan magani yadda ya kamata."
Ta ce yanzu ta kai wani matakin da likitoci ke kira "undetectable" wato ƙwayar cutar ta ragu har ba za a iya ganinta cikin jini ba. "Wannan na nufin ba zan yaɗa cutar ga wani ba muddin na ci gaba da shan magani yadda ya kamata."
'Muna samun magani'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A game da fargabar da ake yi cewa ba a samun magani saboda janyewar tallafi daga ƙasar Amurka, Binta ta ce wannan wani tsaiko ne da aka samu na ɗan lokaci, amma yanzu tsaikon ya kau.
"Lallai an samu tsaikon maganin tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu (2025) a baya, sakamakon rage tallafin da gwamnatin Amurka ta yi a ɓangaren lafiya. Amma a lokacin gwamnatin Najeriya ta yi ƙoƙarin ci gaba da sayen maganin. Sannan daga baya kuma masu bayar da agajin sun ci gaba," in ji ta.
Sai dai ta ce yanzu suna samun maganin ba tare da wata matsala ba, inda ta ce akwai magunguna da sauran kayayyakin kariya da aka daina samun tallafinsu.
"Akwai magungunan da ake kira Pre-Exposure Prophylaxis wato PrEP, idan mutum ya sha suna bayar da kariya daga kamuwa da cutar HIV, sai kuma sauran kayan kariya da su ma ba a samu. Amma magani kuwa kwanan nan ma na je na karɓo," in ji ta.
Sauran magungunan da ta ce ana samu, akwai gwajin cutar da magunguna da kayan kare yaɗa cutar tsakanin uwa zuwa ga ɗa.
Shawarata ga masu HIV
Matashiyar ta yi kira ga masu ɗauke da cutar da kada su karaya ko su ɗauki kansu a matsayin marasa amfani.
"Ba a rubuta cutar a fuska. Duk wanda ke da cutar na iya cimma burinsa, amma sai ya kiyaye zuwa asibiti da shan magani."
Ta kuma bukaci gwamnati ta ƙara kaimi wajen wayar da kan jama'a ta hanyar samar da cikakken bayani kan hanyoyin kamuwa da cutar da kuma hanyoyin kariya.
Ta ce tana burin kafa wata babbar cibiya da za ta mayar da hankali kan kula da yara da matasa masu ɗauke da cutar HIV, tare da ba su ilimi da shawarwari da goyon baya domin su samu saukin rayuwa.
"Ina fatan gwamnati da ƙungiyoyi za su tallafa wajen ganin wannan burin ya zama gaskiya. Domin akwai ɗimbin matasa da ke buƙatar a ƙarfafa musu gwiwa domin su yi rayuwa mai kyau," in ji ta.
Kamuwa da HIV a lokacin ƙuruciya
Laraba ta ce ta kamu da cutar ne tana da shekara 12 a duniya, inda ta ce da farko ba ta ma san me ya faru ba, sai daga bisani.
Ta ce, "Na kamu da cutar ne a wani lungu da muke bi idan za mu tafi gida. A hanyar ana zubar da bola, watarana sai na taka allura. Amma sai ban damu ba duk da na ɗan ji ƙaiƙayi, daga baya sai na fara zazzaɓi har aka kai ni asibiti. Sai daga baya ne likita ya gane cewa na kamu da cutar."











