Yadda masu cutar HIV ke cikin zulumi bayan zabtare tallafin Amurka

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Mayeni Jones
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg
- Lokacin karatu: Minti 4
Gugu ta saba karɓar maganinta na yaƙi da cutar sida ko kuma HIV daga wani asibitin gidauniyar USAID da ke ƙwaryar birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Amma daga lokacin da Shugaban Amurka Trump ya dakatar da kuɗaɗen tallafi a farkon shekarar nan, ita da sauran dubban masu fama da cutar a ƙasar sun faɗa cikin zulumi nan take.
Gugu ta ɗan yi sa'a saboda asibitin da take karɓar maganin da ke rage mata raɗaɗin ciwon ya kira ta kafin ya rufe.
"Ina ɗaya daga cikin mutanen da suka samu cikakken maganin a dunƙule. Nakan karɓi maganin wata uku ne. Amma kafin asibitin nawa ya rufe, sun ba ni na wata uku."
Maganinta na ARV zai ƙare a watan Satumba, inda ta tsara za ta koma asibitin unguwarsu na gwamnati domin ci gaba da karɓa a can.
Wata tsohuwar mai zaman kanta mai shekara 54, wadda muka ɓoye sunanta, ta gano tana ɗauke da cutar HIV bayan ta tuba daga yawon bariki.
Shekara 10 da suka wuce ta sha fama da tari mai zafi a ƙirji, inda ta dinga tunanin tarin fuka ne kawai. Wani likita ya ce mata lalurar ƙirji ce kuma ya ba ta magani.
Bayan ta kasa jin sauƙi, sai ta wuce zuwa wani asibiti domin a yi mata gwajin cutar HIV.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Zuwa lokacin na riga na yi imanin ina ɗauke da cutar, kuma abin da na faɗa wa malamar jinya kenan." Tun daga lokacin ne kuma ta fara shan maganin antiretrovirals (ARVs).
Yanzu tana aiki ne a matsayin mai shirya ayyuka da watan ƙungiya mai zaman kanta.
"Mukan taimaka wa masu zaman kansu da ke da ciki samun maganin ARV domin tabbatar da cewa ba su yara da HIV ba. Muna kuma kai musu ziyara har gida domin tabbatar da suna shan maganin a kan lokaci."
Akasarin mata masu zaman kansu a Afirka ta Kudu sun dogara ne da asibitocin USAID da gwamnatin Amurka ke ɗaukar nauyi domin samun maganinsu da kuma kulawar lafiya.
Cikin wani rahoto da ake ƙoƙarin fitarwa, hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke yaƙi da yaɗuwar HIV/AIDS ba ta keɓance Amurka kawai ba wajen kokawa kan janye tallafin da ake bayarwa.
A cewarta: "Masu kamuwa da cutar HIV sun ragu da kashi 40 cikin 100 tun daga 2010, kuma an kare yara miliyan 4.4 daga kamuwa da cutar tun daga shekarar 2000. An tseratar da sama da mutum miliyan 26," a cewar UNAIDS.
Ta ce za a iya samun ƙarin masu kamuwa da cutar miliyan shida, da kuma mace-mace miliyan huɗu nan da 2029 idan ba a ɗauki mataki yanzu ba.
Gugu na ganin da yawa daga cikin mata masu zaman kansu ba za su iya komawa asibitocin gwamnati domin karɓar magani ba.
"Matsalar komawa asibitocin gwamnati ita ce ɓata lokaci. Kafin mutum ya samu abin da yake nema a wuraren, sai ya je tun ƙarfe 4 ko 5 na dare kuma zai iya shafe tsawon ranar a kan layi. Lokaci na da muhimmanci sosai a wajen masu zaman kansu," in ji Gugu.
A cewar MDD, katse tallafi kan HIV da Amurka ta yi zai iya dawo da hannun agogo baya game da nasarorin da aka samu a yaƙi da yaɗuwar cutar.
Masana kimiyya na Birtaniya sun faɗa a mujallar The Lancet cewa ƙiyasi ya nuna tallafin na USAID ya magance mace-mace da kashi 65 cikin 100, ko kuma na mutum miliyan 25.5 a tsawon shekara 20 da suka gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon Shugaban Amurka George W Bush ya ƙaddamar da wani shiri mai girma domin yaƙar HIV/Aids a 2003, yana mai cewa zai taimaka wa Amurka cimma muradunta.
Shirin da aka yi wa laƙabi da President's Emergency Plan for Aids Relief (Pepfar), ya jawo kashe dala biliyan 100 a fadin duniya, wanda shi ne adadi mafi yawa da wata ƙasa ta ware kan yaƙi da wata cuta.
Akwai masu cutar HIV kusan miliyan 7.7 a Afirka ta Kudu, adadi mafi girma kenan a fadin duniya, a cewar alƙaluman UNAIDS.
Kusan miliyan 5.9 daga cikinsu na samun maganin antiretroviral, wanda aka samu raguwa da kashi 66 cikin 100 na mutane da ke mutuwa tun 2010, in ji hukumar.
"Ina ganin za mu fuskanci ƙaruwar maus kamuwa da HIV, da tarin fuka, da sauran wasu cutukan da ke yaɗuwa," kamar yadda Farfesa Lynn Morris, wanda mataimakin shugaban Jami'ar Wits ne a Johannesburg, ya shaida wa BBC.
"Kuma za mu iya ganin koma-baya a ci gaban da aka samu. Mun ɗauki hanyar magnce wasu daga cikin matsalolin nan."
Afirka na cikin na gaba-gaba wajen yin bincike a kan cutar ta HIV. Akasarin magungunan da aka samar na rage kaifin cutar, sun samo asali ne daga can.

A wani ɗakin gwaji na Jami'ar Wits, wata tawagar masana kimiyya na aikin lalubo rigakafin HIV.
Wani ɓangare ne na rukunin ɗakunan gwaji na Brilliant Consortium da ke aiki a ƙasashe takwas na Afirka domin samar da rigakafin HIV.
Wani mai shirin zama Farfesa Abdullahi Ely ya faɗa wa BBC cewa: "Muna yin gwajin wani rigakafi kafin mu fara gwada shi a kan mutane domin ganin yadda zai yi aiki.
"Mun tsara yin gwajin a Afirka bisa abin da 'yan Afirka suka samar saboda muna son binciken ya amfani mutanenmu."
Amma katsae tallafin na Amurka ya jefa su cikin rashin tabbas.
"Lokacin da aka dakatar da aiki, dole muka ajiye komai. Wasu ne kawai daga cikinmu ne kawai suka samu ƙarin kuɗi don ci gaba da aikin. Hakan ya mayar da mu baya," in ji Farfesa Ely.
A watan Yuni, jami'o'i sun nemi gwamnatin ƙasar ta ba su tallafin biliyan 4.6 na kudin Afirka ta Kudu rand a cikin shekara uku domin cike giɓin da suka samu.
"Muna ta yekuwar neman agaji saboda Afirka ta Kudu ce kan gaba wajen binciken HIV. Hakan zai yi tasiri sosai a kan bincken da ake yi a fadin dunya," a cewar Dr Phethiwe Matutu, shugabar jami'o'in Afirka ta Kudu.










