Ko cin fara da shinge zai iya maye gurbin naman kaza da na shanu?

    • Marubuci, The Conversation*
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
  • Lokacin karatu: Minti 4

A cikin shekaru goma da suka gabata, an yi ta muhawara kan maye gurbin nama da cin ƙwari irin waɗanda mutane ya kamata su ci. Ko da yake hakan na iya zama abin mamaki a wasu ƙasashe yayin da wannan zaɓin abinci mai gina jiki yana ƙara samun karɓuwa.

Wasu al'adun girke-girke na ƙasashe kamar Thailand, China da Mexico sun haɗa da su cikin girke-girken su tun ƙarni da dama da suka wuce.

Abin kore yunwa

Tun daga shekarar 2014, lokacin da hukumar abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta fitar da littafi game da cin ƙwari, lamarin ya sake ɗaukar hankalin duniya.

Wannan muhawara na da goyon baya daga bincike da dama da ke nuna cewa kiwon ƙwari na da ƙarancin illa ga muhalli fiye da kiwon shanu da alade da kaji.

Misali, domin samar da kilo ɗaya na naman kaza — wanda shi ne mafi ƙarancin gurɓata muhalli a cikin ukun — ana fitar da kilo 4.5 na hayakin CO₂ (wanda ke gurɓata iska). Amma kilo ɗaya na ƙwari irin su mealworm ko darkling beetle, na haifar da kilo 2.8 na iskar CO₂ ne kawai.

Bugu da ƙari, kiwon ƙwari na buƙatar ruwa da fili ƙalilan idan aka kwatanta da kiwon dabbobi. Misali, idan ana so a samar da kilo ɗaya na naman kaza, ana buƙatar fili mai girman mita 12.48, yayin da kuma za a buƙaci mita 3.07 ne kawai idan ana son a samar da kilo ɗaya na ƙwaro

Hakan na nufin cin kwari zai iya zama wata mafita ta rage yunwa a tsakanin al'umma da kuma rage kudin da ake kashewa wajen samar da abincin.

Rumbun sinadaran gina jiki

A faɗin duniya ana cin kimanin nau'i 2,250 na ƙwari da gizo-gizo, ciki har da buzuzu da zanzaro da malam buɗe mini littafi da ƙudan zuma.

A nahiyar Turai, doka ta ba da damar kiwon nau'ukan ƙwari huɗu domin samar da abinci ga al'umma: sun hada da tsutsar mealworm da fara da gyare da buzuzun gungura-kashi, waɗanda ke ƙunshe sinadaran gina jiki masu ɗimbin yawa.

Yayin da naman kaza da na alade da kuma naman kaza ke samar da sinadarin gina jiki kashi 24.1% da kashi 22.2% da kuma kashi 21%; mealworm na samar da kashi 53%, fara na da kashi 56.8%, gyare na da kashi 62.6% yayin da buzuzu ke da kashi 50.79%

To amma ƙwari nawa za ka ci kafin ya maye alfanun da kake samu daga nama? Duk da cewa lissafin ba abu ne mai sauƙi ba, amma za mu yi bayani.

Mutum mai nauyin kilo 70 na buƙatar ya ci giram 277 na naman shanu ko kuma giram 93 na busasshiyar fara a rana.

Wani misalin kuma shi ne mutum mai nauyin kilo 80 zai buƙaci ya ci giram 276 na naman kaza ko kuma giram 131 na ƙaguwa mai ƙugiya (lobster).

Amma yana da kyau a sani cewa akwai buƙatar haɗa nau'ukan abinci daban-daban (kamar ƴaƴan itace da hatsi da kifi) domin samun wasu sanadaran da jiki ke buƙata, kamar sanadarin samar da ƙarfi da kitse mai lafiya da sanadaran bitamin domin samun lafiya.

Abinci mai kyau da amfani

A ƙarshe, cike giɓin sinadarin gina jiki na protein ta hanyar ƙwari zai iya rage yawan abincin da muke buƙata.

Haka nan kuma akwai alfanu ga muhalli kasancewar ba a buƙatar makeken fili domin kiwon ƙwari kuma babu buƙatar kafa wasu manyan masana'antu sarrafawa.

Haka nan ya kamata a sani cewa ƙwari suna ɗauke da kashi 60% na kitse maras cutarwa, lamarin da ya za su iya zama zaɓi mai kyau ga masu barazanar kamuwa da lalurar zuciya.

Baya ga cewa masu cin ƙwari na samun wata gamsuwa ta kasancewa wani abinci na al'ada, sukan samar da abinci mai daɗin gaske.