Bai kamata a cutar da yara ba a lokacin yaƙi - Mahaifin da ake garkuwa da ƴaƴansa

Doron, matar Yoni Asher da ƴarsa mai shekara 2, Raz da Aviv mai shekara 4 na cikin waɗanda mayaƙan Hamas suka ɗauke a harin da suka kai ranar 7 ga watan Oktoba

Asalin hoton, YONI ASHER

Bayanan hoto, Doron, matar Yoni Asher da ƴarsa mai shekara 2, Raz da Aviv mai shekara 4 na cikin waɗanda mayaƙan Hamas suka ɗauke a harin da suka kai ranar 7 ga watan Oktoba

Zaune a cikin lambun gidansa da ke yankin tsakiyar Isra'ila, Yoni Asher ya nuna min wani bidiyo daga cikin wayarsa.

Yaransa mata ƙanana su biyu ne a cikin bidiyon suna zaune a kan gado. Suna yin waƙar taya murnar zagayowar ranar haihuwa.

Raz wadda ita ce babba a cikinsu, mai dogon gashi, tana da shekara huɗu ne kacal da haihuwa.

Ƙanwarta mai suna Aviv, wadda ta fi kama da mahaifinsu tana da shekara biyu ne da haihuwa.

Yoni ya ce min "Sun yi min wannan waƙar ce a lokacin zagayowar ranar haihuwata a watan Juli."

Amma yanzu bayan wata huɗu, mahaifin nasu wanda yake da shekara 37 da haihuwa, shi kaɗai ne ya rage a cikin gida.

An sace yaran tare da mahaifiyarsu mai suna Doron, a ranar 7 ga watan Oktoba, sa'ilin da Hams ta kai hari kan Isra'ila.

Ana ganin cewa suna daga cikin mafiya ƙarancin shekaru a cikin mutane 240 da ake garkuwa da su a Gaza.

Yoni ya ce "Sun je hutu ne wajen kakarsu a garin Niz."

Mazaunin na ƴan Isra'ila na da tazarar mil biyu ne kacal daga Gaza.

Kuma yana daga cikin matsugunan Isra'ila da harin Hamas ya fi shafa, inda ake tunanin an kashe ko kuma yin garkuwa da aƙalla mutum guda cikin kowane mutane huɗu da ke rayuwa a garin.

Yoni ya ga matarsa da ƴaƴansa a cikin wani bidiyo a dandalin TikTok, zagaye da mayaƙan Hamas
Bayanan hoto, Yoni ya ga matarsa da ƴaƴansa a cikin wani bidiyo a dandalin TikTok, zagaye da mayaƙan Hamas
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar, Yoni ba ya tare da iyalan nasa. Yana gida, kimanin kilomita 100 daga inda iyalan nasa suke.

Yoni ya fara sanin cewa an kai hari kan iyalansa ne a wani bidiyo da ya gani a dandalin TikTok. Yoni ya nuna min bidiyon.

A cikin bidiyon mai tsawon daƙiƙa biyar, za a iya ganin mai ɗakinsa Doron sanye da kayan bacci, yayin da ake cusa su cikin wani amalanke na mayaƙan Hamas.

Za a iya ganin Raz, ita kuma sanye da riga ƴar-shara.

"Wannan hannun Aviv ce," in ji Yoniz, yayin da yake nuna yatsun wata yarinya da ake gani a cikin bidiyon tana ƙoƙarin taɓa mahaifiyarta.

A lokacin an kwashe kimanin mako uku ke nan Yoniz bai samu wani bayani ba daga iyalan nasa.

Ita kuwa kakarsu, Efrat Katz, an gano gawarta. Sai kuma abokin zaman ta, Gadi Mozes, an yi garkuwa da shi.

"Wannan babbar masifa ce," in ji Yoni. "Wannan shi ne ainihin bala'i."

"Ta yaya zan iya cin abinci bayan ban san mene ne iyalina suke ci ba? Ta yaya zan iya yin bacci tun da ban san wane hali suke ciki ba, zafi ne ko sanyi?"

A matsayinka na mahaifi, idan ka ga idan ka ga yaranka na tsalle-tsalle a kan gado za ka riƙa jin tsoron kada su faɗi su ji ciwo. Ka yi tunanin yadda nake ji a wanna hali da nake ciki. Komai ma tsoro yake ba ni."

A yanzu Yoni ba ya wani abu face tunanin abubuwan da suka faru a baya. Duk wani abu na cikin gidan na tuna masa abubuwan da suka faru a baya. Musamman hotunan yaransa da zane-zanen da suka yi da sawun hannuwansu a jikin bango.

Yoni ya ce "suna son yin zane. Raz ce ta zana min wannan," a lokacin da yake nuna wani zane da aka maƙala a jikin bango.

"Ta ce min wannan jarumi ne."

Aviv na da shekara 2 da haihuwa. Ita da ƴar'uwarta Raz mai shekara 4 na daga cikin waɗanda ake riƙe da su a Gaza

Asalin hoton, YONI ASHER

Bayanan hoto, Aviv na da shekara 2 da haihuwa. Ita da ƴar'uwarta Raz mai shekara 4 na daga cikin waɗanda ake riƙe da su a Gaza

Sai kuma kayan wasansu a cikin ɗakin girki.

"Kodayaushe suna son su ga suna wasan girki, su yi min girki."

In ji Yoni.

Ga kuma wasu ƙananan takalma da aka jera su a ƙusurwa da kuma litattafan makaranta.

Ya ce "dole na cire baturan kayan wasan nasu masu yin ƙara."

"Ƙananan yara ne masu ji da ƙarfi. Yadda nake da mata uku, ina da isassun waɗanda za su dame ni da surutu." Yoni ya faɗa inda yake murmushi da ƙyar.

An tambaye shi, ya yake ji game da wahalar da ake ciki a Gaza, inda a yanzu sojojin Isra'ila ke yin ruwan wuta tsawon kusan wata ɗaya, inda a yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe da raunata dubban yara?

"Yara, yara ne koda daga wace ƙasa suka fito" in ji shi.

"Ya kamata a cire yara a cikin wannan batu. Ba zan iya nuna ƙiyayya ga koda yaran maƙiyana ba ne. Me ya sa za ka nuna wa yara ƙiyayya?"

Me za ka ce game da bidiyon mutanen da ake garkuwa su da Hamas ta fitar?

Yoni ya ce "Abin babu daɗin kallo."

Yoni ya ce ƴaƴamsa na son zane-zane da kuma yi masa girki

Asalin hoton, YONI ASHER

Bayanan hoto, Yoni ya ce ƴaƴamsa na son zane-zane da kuma yi masa girki

"Su ne ake garkuwa da su. Su (Hamas) na amfani da su domin cin tunanin mutane da yaƙi."

Kasancewar Yoni na da shekara 37 da haihuwa, ba wannan ne karon farko da ya fuskanci rikicin da ake fama da shi tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa ba. Ya sha fuskantar yaƙin, iyayensa ma haka.

To amma a gare shi, ranar 7 ga watan Oktoba ita ce ta fi muni.

Ya ce "Ita ce ranar kisan kiyashi."

Ya ƙara da cewa "Na san wannan kalmar ta yi tsauri da yawa. Amma ita ce rana mafi muni da Yahudawa da kuma al'ummar Isra'ila suka taɓa gani."