Ku San Malamanku tare da Malam Ahmad Tijjani Ibrahimu Mushaddidu

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Malam Ahmad Tijjani Ibrahimu Mushaddidu

An haifi Malam Ahmad Tijjani Ibrahimu Mushaddidu a garin Jos na jihar Filato.

Ya fara karatun Alkur’ani a wajen Malam Isa wani Bafulatani mazaunin layin Dan maraya a nan birnin Jos.

Bayan an kwana biyu, sai ya kai ni wajen Malam Yusuf Sarki Babale, amma wannan makarantar dare ce, inda na yi karatu wajen su Malam Umar Limamin ‘yan Doka.

“Daga nan tsakanin shekara takwas zuwa tara sai Malam Sarki ya dauke ni cak, ya mayar da ni jihar Kano domin karatu wurin Sheikh Haruna Rasheed, wanda ya Halifanci Sheikh Dan Almajiri.

Anan Makarantar Madinatul Ahbab na shekara 11 nan na yi saukar Al-Kur’ani da haddar sama da Izifi 40, daga baya na gyara Tilawa ta, aka bani shaidar zama Hafizin AlKur’ani,’’ in ji malamin.

A dai birnin Kano, yana yin karatun zaure a hannun Malam Fadhlu dan-Almajiri da ya koya musu littafan addini kamar Risala, Ta’alimi da su Hayatul Islam, da Durusul Diniyya wanda Malam Inuwa Shalan da Malam Inuwa Atta suke koyar da su.

Shi kuwa Malam Lawan shugaban makarantar yana koyar da su haruffan Hausa suna iya karanta jaridu kamar AlFijir da hausar Ajami da Boko da saueransu.

Bayan dawowarsa daga karatu ya roki babban malamin ya ba shi izinin fara karantawar addini a birnin Jos.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya samu gired 2 na makarantar boko, ya yi karatu sosai sai suka wuce kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato. Daga shekarar 1996 zuwa 1999 anan ya samu shaidar kammala karatun koyarwa na NCE.

Mahaifina ya koyar dani Tafsirul Jalalaini, muna karatu sosai bayan makaranta.

Sannan babban Limamin jihar fulato har zuwa yau, Sheikh Malam Lawal Adam wanda Malamina Mushaddidu ya tur ani wajensa da cewa shi ya aikoni domin na yi karatu a hannunsa, hakan kuwa aka yi na yi karatu mai inganci a hannunsa.

Musbahul Salih, anan na karanta shi. Na karanta Yakutatul Fareeda, akan Ahkamul Darikatul Tijjaniyya.

"Idan akwai wani abu da ya bani wuya a lokacin da na ke karatu, bai wuce rashin iya karata Suratul Rahman ba, kasancewa akwai ‘’Fabi’ayyi Alaa I’rabbikuma tukazziban’’ da yawa a ciki, ta kan rikitani, amma a hankali cikin ikon Allah sai komai ya daidaita,’’ in ji Malamin.

Surar da yake samun nishadi idan yana karantawa ita ce ‘Izawaka’. Sukan je wanka Alhamis da Juma’a a rafi a nan Fagge.

Malamin yana da ‘ya’ya 10, sai kuma uku da Allah ya yi wa rasuwa.

Lokacin da aka nada Malam Mushaddidu a matsayin na’ibin Limamin masallacin Jos, har ya rubuta huɗuba 50, da aka tattarawa wuri guda aka kuma wallafa.