Gayyatar Yariman Saudiyya zuwa jana'izar Sarauniya ta janyo ce-ce-ku-ce

Asalin hoton, Getty Images
Gayyatar da Birtaniya ta yi wa Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed Bin Salman zuwa jana'izar Sarauniya Elizabeth II ya janyo zanga-zanga daga masu rajin kare hakkin bil-adama.
Wani rahoto da hukumar leken asirin Amurka CIA ta fitar ya nuna cewa Yariman na Saudiyya na da hannu a kisa tare da daddatsa gawar ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya a 2018.
Yariman da gwamnatinsa sun musanta wannan zargin, amma har yanzu ƙasashen Yamma na kallon Yariman da wannan tabo, kuma tun lokacin da abin ya faru bai je Birtaniya ba.
Mai magana da yawun ofishin jakadanci Saudiyya a Birtaniya ya tabbatar cewa a ƙarshen wannan mako ne Yariman zai je Birtaniya, sai dai ba a san ko zai halarci jana'izar ba ranar Litinin.
Budurwar Jamal Khashoggi, Hatice Gengiz, ta ce gayyatar wani tabo ne ga Sarauniya Elizabeth II.
Ta yi kira ga hukumomin Birtaniya da su kama shi idan ya je kasar.
Ƙungiyar da ke matsa lamba mai suna Campaign Against the Arms Trade (CAAT) ta zargi Yariman da sarakunan yankn Gulf da yin amfani da mutuwar sarauniyar wajen ɓoye zarge-zargen da ake musu na take haƙƙoƙin bil adama.
Ƙungiyar ta ƙiyasta cewa tun bayan ɓarkewar mummunan yaƙi a Yemen, shekara takwas da ta gabata, Birtaniya ta sayarwa da ƙawancen da Saudiyya take jagoranta da ke yaƙi a can, makaman da ƙudinsu ya kai fiye da $23bn.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƴancin siyasa ya ragu sosai tun bayan da Mohammed Bn Salman ya zama yarima mai jiran gado a 2017, inda aka riƙa lafta wa masu sukar gwamnati hukuncin zama gidan gyaran hali, ko da kuwa wallafa bayani ne a shafukan sada zumunta.
A gefe guda kuma, yariman ya duƙufa wajen samar da ƴanci ta fuskar zamantakewa. An sake buɗe wuraren nishaɗi da gidajen sinima da aka daɗe da dakatar da su a Saudiyya saboda sun saɓa da addinin musulunci.
A yanzu, mata suna tuƙi bisa umarnin Yariman sannan Saudiya ta karɓi baƙuncin wasanni da dama na ƙasa da ƙasa da kuma tarukan waƙa har da kaɗe-kaɗen da DJ David Guetta ya gudanar.
Duk da irin sukar da ake yi wa Saudiyya kan tsare-tsarenta na kare haƙƙin bil adama, ƙasar ta ci gaba da zama babbar ƙawa ga Birtaniya a yankin Gulf inda ƙasashen yamma ke kallonta a matsayin kandagarki ga mamayar Iran.
Tana sayen makamai daga ƙasashen yamma, tana ɗaukar dubban mutane aiki, tana karɓar baƙuncin maniyyata aikin hajji duk shekara sannan tana taimakawa wajen daidaita farashin man fetur. Lamarin da a wani ɓangaren yake bayyana dalilan da suka sa , a mafi yawan lokuta, duniya ta yi ɗif da sukar yarima mai jiran gadon na Saudiyya.











