United ta sanyawa Sancho farashi, Bayern da Ajax na nazarin Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United tana son aƙalla kashi 75% na fam miliyan 75 da ta biya Borussia Dortmund kan ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 24, idan har kulob ɗin na Bundesliga na buƙatar sake sayen ɗan wasan (Sun)
Bayern Munich da Ajax na ci gaba da nazari kan Erik Ten Hag, mai shekara 54, yayin da suke sa ran cewa za a kore shi a matsayin kocin Manchester United a ƙarshen kakar bana. (Mirror)
RB Leipzig ta gabatarwa ɗan wasan gaban Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 20, sabuwar kwantiragin shekara ɗaya, duk da cewa anan alaƙanta shi da komawa Arsenal(Fabrizio Romano)
Kocin Tottenham Ange Postecoglou zai ba da fifiko wajen siyan sabon ɗan wasan gaba yayin da yake shirin yi wa tawagar ƴan wasansa garambawul. (Mirror)
Ipswich ta ce tana yin duk mai yiwuwa don ci gaba da riƙe kocinta Kieran McKenna a yayin da Brighton da Chelsea da Manchester United ke zawarcinsa. (Talk)
Kocin Chelsea, Mauricio Pochettino ya ce zai yi farin cikin rike kashi80 zuwa 85 cikin ɗari na 'yan wasansa a kakar wasa mai zuwa. (football.london)
West Ham nadaf da daukar ɗan wasan baya Luis Brown mai shekara 18 daga Arsenal (Caught Offside)
Chelsea ba ta kusa cimma sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Ingila mai shekara 24, Conor Gallagher ba, wanda ake alaƙanta shi da Aston Villa da Tottenham, kuma Blues za ta iya sayar da shi domin gujewa saɓa dokokin kasuwancin Premier. (Express)
Golan Sifaniya David Raya ya ce bai yi wata tattaunawa da Arsenal kan kwantiragin zaman dindindin ba daga Brentford. (Express)
Rahotanni daga ƙasar Argentina na cewa ɗan wasan tsakiya Alexis Mac Allister mai shekara 25 farashin fam miliyan 60 a kwantiraginsa da Liverpool. (Mirror)











