Da gaske ne akwai baƙin halittu a wata duniya?

...

Asalin hoton, getty images

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta fitar da wani rahoto a ranar Alhamis da ta gabata a kan ko da gaske akwai baƙin halittu a sararin samaniya?

Jama'a da yawa a duk faɗin duniya sun yi ta sa rai kan wannan rahoto da aka daɗe ana jira.

Sai dai a ƙarshe, ba a samu wani gamsasshen bayani ba a cikin rahoton.

Wato ba su samu wata shaida ta kasancewar baƙin halittu a duniya ba; Amma kuma, NASA ba za ta iya kawar da yiwuwar hakan ba.

Bayan tsawon shekara guda na gwaje-gwaje da bincike, rahoton mai shafuka 36 da NASA ta fitar, yawancinsu cike suke da batutuwan fasaha da kimiyya iri-iri.

Ana alaƙanta baƙin halittun da wasu abubuwa da aka gani suna shawagi a sararrin samaniya waɗanda ba a san ko mene ne ba (UFO).

Ma'ana motsin abubuwan da wasu lokuta ake da'awar ana ganin su a sararin samaniya.

Mutane da dama sun dade suna sha'awar sanin labarin waɗannan baƙin halittu.

Wasu ma sun ce a zahiri sun ga wasu ababen hawa waɗanda suke zargi na baƙin halittu ne.

Akwai mutane da dama mutane a duniya waɗanda suka yi imani da wanzuwar waɗannan baƙin halittu duk da cewa babu hujja.

..

Asalin hoton, getty images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Waɗannan baƙin halittun dai suna fitowa a yawancin wasannin bidiyo da kuma fina-finai.

Wadannan baƙin halittu, hukumar NASA na kiran su UAPs ko 'Unidentified Anomalous Phenomena' a turance.

Hukumar ta NASA dai ta dauki hayar wata tawagar masu bincike ta musamman a bara domin nemo bayani game da waɗannan baƙin halittu, ko da gaske akwai rayuwa a wasu duniyoyi baya ga duniyarmu ko babu ta hanyar kimiyya.

Tawagar mai mambobi 16 ta fara binciken daga watan Oktoban bara kuma sakamakon binciken na cikin wannan rahoton.

Shafi na karshe na rahoton ya bayyana cewa, babu wata hujja da za ta tabbatar da cewa binciken na NASA na ƙunshe da baƙin halittun sai dai waɗannan halittun sun yi tafiya a cikin duniyarmu kamin mu zo nan.

Amma Shugaban Hukumar, NASA Bill Nelson ya yarda cewa za a iya samun wasu duniyoyi masu kama da duniyarmu a cikin biliyoyin duniyoyi da taurari.

"Idan aka tambaye ni ko akwai wasu da ke rayuwa wata duniya dabban da ta mutane, zan ce eh," in ji Nelson. Ya yi alkawarin cewa za su bayyana a fili nan gaba.

Nicola Fox, mataimakiyar shugaban Hukumar NASA ta Ofishin Jakadancin Kimiyya, ta ce: "Baƙin halittu na ɗaya daga cikin manyan abubuwa masu wahalar fahimta a sararin Subuhana."

"Kuma babban dalilin hakan shi ne rashin samun isassun bayanai game da su."

Koda yake akwai rahotannin ganin waɗannan baƙin halittun, Fox ya ce da gaske babu isassun bayanai a kimiyyance da za su nuna inda suke ko daga inda suka fito.

Rahotanni sun ce ana iya bayyana yawancin baƙin halittun, amma ana samun wasu da ba na mutum ba ko na halitta.

Fox ya sanar da cewa NASA ta dauki sabon daraktan bincike kan baƙin halittu.

"Zai samar da cikakken bayanan da za su taimaka wajen tantance bayanai a kan su nan gaba," in ji shi, duk da cewa ba a bayyana sunansa ba saboda dalilai na tsaro.

Wannan sabon daraktan zai tattara da yin nazarin bayanai tare da taimakon ƙirƙirarriyar basira da na'urori.

Wakilin BBC Sam Cabral ya yi wa kwamitin NASA tambayoyi game da wasu hotuna da ake zargin baƙin halittu ne da aka gabatar ga hukumomin Mexico a makon da ya gabata.

Jamie Mawson, masani ta fannin baƙin halittu kwanan nan ya bayyana a gaban Majalisa don gabatar da gawarwakin wasu baƙin halittu guda biyu.

Ya yi iƙirarin cewa an gano gawarwakin biyu a Cusco, Peru a cikin 2017, kuma hanyar tantance shekarun abubuwa ta hanyar kimiyya ta 'radiocarbon' ta nuna cewa sun rayu aƙalla shekaru 1,800.

Abubuwan da aka gabatar wa hukukomin Mexico a matsayin baƙin halittu da suka wanzu a duniya.

Asalin hoton, getty images

Bayanan hoto, Abubuwan da aka gabatar wa hukukomin Mexico a matsayin baƙin halittu da suka wanzu a duniya.

Masana kimiyya, sun nuna shakku sosai game da sahihancin wannan samfurin, domin a baya Mawson ya yi iƙirarin samuwar wasu baƙin halittu wanda aka yi watsi da su.

Wani masanin kimiyya a NASA, David Spurzel ya shaida wa BBC cewa: "Bari mu fitar da wadannan samfuran ga masana kimiyya na duniya domin mu iya gwada su mu san ainihin su mene ne."

Wani batu da aka tattauna a taron manema labarai na NASA a wannan Alhamis din da ta gabata shi ne kan sabon daraktan bincike kan baƙin halittu.

Har yanzu ba a bayyana ko wane ne shi ba, NASA ba ta fayyace komai ba game da aikinsa da albashinsa ba, musamman lokacin da NASA ta ce za su bayyana komai game da binciken baƙin halittu ga duk duniya kuma hakan ya haifar da tambayoyi.

Amma wani dalili mai yiwuwa na rashin bayyana ko wane ne sabon daraktan, na iya zama cewa NASA na son kare shi daga kunyatarwar jama'a.

Dokta Daniel Evans, mataimakin jami'i a NASA, na ɓangaren binciken, ya ce kwamitinsu kan baƙin halittu za su iya fuskantar barazana inda ya yi kira ga NASA da ta dauki lafiyar ‘yan tawagarsu da muhimmanci.

Rahoton ya ce ƙiƙirarriyar basira da na'urori masu koyo su ne kayan aiki mafi mahimmanci wajen gano baƙin halittu.

Ya kuma ce sanar da mutane game da baƙin halittu wani muhimmin al'amari ne.

Hukumar ta NASA ta ce babban kalubalen da ke tattare da wannan bincike shi ne rashin samun bayanai, wanda suke so domin mutane da ba masana kimiyya ba su fahimci komai game da lamarin.

..

Asalin hoton, Getty Images