Ba zan yi tazarce ba - Shugaban Senegal

Shugaban Senegal Macky Sall, ya ce ba zai nemi takara a wani wa'adi na uku ba, matakin da ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da aka ta yi game da anniyarsa ta sake neman tazarce a zaɓen ƙasar na 2024.

Tsarin mulkin Senegal ya bai wa mutum damar takarar shugaban ƙasa sau biyu ne kacal.

Jagoran 'yan adawa Ousmane Sonko, ya buƙaci 'yan ƙasar su fita su yi zanga-zanga matuƙar Mista Sall ya bayyana anniyar yin tazarce a karo na uku.

An kashe aƙalla mutum goma sha shida cikin watan jiya lokacin wata zanga-zanga da ta ɓarke bayan yanke hukuncin shekara biyu a gidan yari ga Mista Sonko.

Magoya-bayansa na cewa ana yi masa bi-ta-da-ƙullin siyasa ne.

Me ya janyo raɗe-raɗin?

Me ya sa aka yi tunanin Macky Sall wanda aka zaɓa a 2012 da kuma a karo na biyu a 2019, zai sake tsayawa takara?

Wannan ita ce tambayar da ta kasance a kusan bakin kowa tsawon watanni.

Haka kuma shi da kansa ya taka muhimiyar rawa wajan jefa al'ummar ƙasar cikin zulumi a hirarrakin da ya yi da kafofin yaɗa labarai a baya.

To sai dai, a jawabin da ya yi wa al'ummar ƙasar da aka nuna a kafar talbijin ranar Litinin da dare Shugaba Macky Sall ya fito fili ya sanar da shawarar da ya yanke wadda ya ce, za ta bai wa mutane da dama mamaki musamman magoya bayansa.

Ya ce "bayan na ɗauki tsawon lokaci ina nazari a yanzu shawarar da na yanke ita ce ba zan tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa na 25 ga watan Fabrairun baɗi ba, duk da yake tsarin mulki ya ba ni damar yin haka".

"Na san shawarar da na yanke ta ƙin tsayawa takara za ta bai wa mutane da dama mamaki waɗanda na san cewa suna alfahari da ni kuma akwai aminci tsakaninmu."

Neman haɗin-kai

Shugaba Sall ya jaddada buƙatar ganin al'ummar Senegal sun haɗa kai, kuma ya nuna alhini a kan mutum 16 da suka rasu a zanga-zangar baya-bayan nan, yana cewa muradinsa shi ne kare mulkin dimokraɗiyyar ƙasar da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

To sai dai yayin da 'yan ƙasar da dama ke jinjina masa game da shawarar da ya yanke, wasu kuwa cewa suka yi, ya yi hakan ne domin kauce wa mummunan sakamako.

Aminata Toure, tsohuwar firaminista a gwamnatinsa wadda yanzu ta koma ɓangaren 'yan adawa ta ce: "Duk da yake ba a makara ba amma kamata ya yi a ce ya mutunta tsarin mulki".

Tun lokacin da aka sake zaɓarsa a 2019 ne ya kamata ce ya sanar da matsayinsa, in ji ta.

Ta ƙara da cewa, da ya yi haka tun farko da Senega ba ta tsinci kanta a cikin halin da take ciki ba yanzu.

"Idan ba a manta ba mun rasa mutum 16 kuma ya zaman dole ga kwamitin bincike da aka dora alhaki ya faɗa mana wadanda suka shirya harin da sauransu."

A 2016 ne Shugaba Macy Sall ya sake fasalin tsarin mulkin Senegal. A cikin sauye-sauyen da aka yi wa kundin, duk wani shugaba ba zai tsaya takara fiye da sau biyu a jere ba.