Za a iya kama Donald Trump nan da ƴan kwanaki

Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko a tarihi da za a tuhuma da aikata wani mugun laifi.
Za a tuhumi tsohon shugaban ƙasar ne a New York bisa zargin bayar da wasu maƙudan kuɗaɗe don toshiyar-baki ga wata fitacciyar 'yar fim ɗin batsa, da niyyar kada ta yi magana a kan zargin da ake yi masa na yin mu'amala da ita, kafin zaɓen Amurka na 2016.
Bayan raɗe-raɗin da aka shafe wata da watanni ana ta yi, yanzu dai ta tabbata za a tuhumi Donald Trump da aikata laifin.
Duk da cewa, zuwa yanzu ba a fito fili an ba da cikakken bayani game da tuhumar ba, amma dai tuhuma ce mai alaƙa da irin rawar da ya taka wajen biyan kuɗi ga matar - Stormy Daniels.
Kasancewar a yanzu tuhuma ta tabbata a kansa, dole ne tsohon shugaban Amurkar ya je New York inda za a ɗauki hoton zanen yatsunsa da na fuska da kuma na ƙwayoyin halittarsa kamar yadda 'yan sanda suke yi wa duk wani wanda aka tuhuma da babban laifi.
Daga nan ne, zai gurfana gaban alƙali a kan tuhumar, sannan ƙila a bayar da belinsa.
Wani ɗan jarida, Daniel Lippman ya faɗa wa BBC cewa, mai yiwuwa a kowanne lokaci daga yanzu a je a kama Trump.
Ya ce, ''yadda abin yake kenan. Ko da kai tsohon shugaban ƙasa ne, idan aka tuhume ka da aikata mugun laifi, dole ne ka shiga hannun hukumomin tsaro.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Shi ba barazana ba ne ga al’umma, kamar wani mai mugun laifi da ke da hatsari. Ba wai kamar ana ganin zai gudu zuwa wata ƙasa ba ne. Yanzu haka suna tattauna yadda zai miƙa kansa," in ji ɗan jaridar.
A wata doguwar sanarwa da ya fitar don maida martani kan batun, Trump ya bayyana lamarin da cewa bi-ta-da-ƙullin siyasa ne kawai.
Kuma lauyoyinsa sun ce ba wani laifi da ya aikata, har ma sun lashi takobin yaƙar wannan tuhuma a kotu da duk ƙarfinsu.
Shi kuwa lauyan Stormy Daniel, matar da ke tsakiyar wannan zargi, ya ce hukuncin da aka yanke na shari’a kan lamarin, ba abin murna ba ne, kuma ba wanda ya fi ƙarfin doka.
Wannan shari’a ka iya kasancewa ta farko a kan tsohon shugaban na Amurka, inda za a tuhume shi da aikata wani babban laifi.
Amma kuma, ba lallai ne tuhumar ta kasance ta ƙarshe a kansa ba, abu ne da zai zama kamar buɗe babin farko, ko dasa ɗan ba a jerin zarge-zargen da ake yi wa Trump.
A yanzu haka, akwai wasu manyan bincike-bincike da ake yi masa guda biyu, da suka danganci ingiza bore da kutsen da aka yi a ginin majalisun dokokin Amurkar, Capitol.
Akwai kuma batu kan yunƙurin canza sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na 2020, batutuwan da har ma sun fi wannan na yanzu ƙarfi sosai.
A makon jiya ne, Mista Trump ya yi barazanar cewa za a ga bala’i, muddin aka tuhume shi da aikata mugun laifi.
Abin da ya sa, Mick Mulvaney, tsohon muƙaddashin shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Amurka a lokacin mulkin Trump, ya shaida wa BBC cewa, idan tsohon shugaban ƙasar ya nemi ingiza magoya bayansa su tada zaune tsaye a kan wannan tuhuma, to kuwa lallai ya ɗebo ruwan dafa kansa.
Amma kuma tuhumar in ji Mulvaney, za ta iya taimaka wa Trump a siyasance, don kuwa ‘yan jam'iyyar Rifablikan hatta waɗanda suke adawa da shi kamar shi kansa, za su tausaya masa.
Saboda za a iya cewa ana yi masa maƙarƙashiyar siyasa ne, ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati.











