Yadda zargin aikata lalata ke neman ɗaure Donald Trump

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaba Donald Trump ya musanta zarge-zargen da Stormy Daniels ta yi a kansa

Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin da ake masa na biyan wata tsohuwar ƴar wasan batsa Stormy Daniels kuɗi domin ta ɓoye mu'amalar da suka yi.

Ms Daniels ta yi iƙirarin cewa Mista Trump ya kwanta da ita, kuma ta karɓi kuɗi $130,000 daga hannun tsohon lauyansa kafin zaɓen 2016 domin kada ta fallas shi.

Daga baya an ɗaure lauyan, Michael Cohen, bisa wasu zarge-zarge.

Tsohon shugaban ƙasar ya musanta cewa ya yi lalata da Miss Daniels tun bayan zargin da aka yi masa a shekarar 2018.

'Mun yi mu'amala da mista Trump a ɗakin otal'

Miss Daniels, wadda ainihin sunanta Stephanie Clifford, ta bayyana wa manema labarai cewa ta haɗu da Mista Trump a lokacin wata gasar wasan golf a watan Yulin 2006.

Ta yi zargin cewa sun sadu sau ɗaya a ɗakin otal ɗin sa da ke bakin ruwa na Tahoe, wani wurin shakatawa tsakanin California da Nevada. Sai dai lauyan mista Trump ya musanta zargin a lokacin.

"Da alama bai damu da lamarin ba. Ya kasance mai girman kai," in ji Miss Daniels, yayin da take amsa tambayar da wata mai hira ta yi mata cewa ko Mista Trump ya ce ta yi shiru game da zargin yin lalata.

Mai ɗakin Mista Trump a lokacin, Melania Trump, ba ta halarci gasar ba kuma ta haihu a lokacin.

'Barazana da biyan kuɗi domin na yi shiru'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A 2016, kwanaki kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasar Amurka, miss Daniels ta ce lauyan mista Trump Michael Cohen ya biya ta $130,000 domin ta yi shiru da bakinta kan alaƙarsu da ita.

Ta ce ta karɓi kuɗin ne saboda tana tsoron abin da zai faru da iyalanta idan ta ki karɓa.

Miss Daniels ta ce an yi mata barazana daban-daban domin ta yi shiru.

A 2011, jim kaɗan bayan da ta amince ta tattauna da mujallar 'In Touch' kan zargin da take yi wa Trump, ta ce wani mutum da ba ta sani ba ya tunkaro ta da ƴarta a Las Vegas, inda ya faɗa mata cewa ta "rabu da Trump".

"Wannan yarinya kyakkyawa ce. Abin ba zai yi daɗi ba idan wani abu ya samu mahaifiyarta," in ji Daniels lokacin da take tuno abin da mutumin ya faɗa mata, a wata tattaunawa da gidan talabijin ɗin CBS a 2018.

Ba a saka tattaunawar da ta yi da mujallar ba har sai 2018.

Kafin a saka tattaunawar ta mintuna 60, kamfanin mai na Shell da ke da alaƙa da mista Cohen ya yi barazanar maka miss Daniels a kotu da bukatar biyan $20m, inda suka ce ta karya yarjejeniyar da suka amince da ita.

Miss Daniels ta faɗa wa CBS cewa tana cikin barazanar biyan miliyoyin dala idan ta yi magana a gidan talabijin, amma "abu mai muhimmanci ne a gare ni saboda na kare kaina".

Shin saɓa ka'ida ne biyan kuɗi don a ɓoye laifin mutum?

Babu wani batun saɓa wa ka'ida idan wani ya biya kuɗi domin kada a bayyana abin da ya aikata.

Sai dai tun da an biya kuɗin ne wata ɗaya kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, masu sukar mista Trump sun yi zargin cewa biyan kuɗin zai iya zama saɓa ka'idar yakin neman zaɓe.

A watan Agustan 2018, mista Cohen ya amsa laifin kauce wa biyan haraji da karya ka'idar kashe kuɗaɗe ta yakin neman zaɓe, da kuma biyan abokiyar Trump miss Daniels kuɗi.

Duk da cewa ya ce mista Trump ba shi da alaƙa da kuɗin da aka biya, daga baya mista Cohen ya faɗa cewa mista Trump ne ya ba shi izinin biyan kuɗaɗen da suka kai $130,000 domin a ɓoye mu'amalarsa da matar, kwanaki ƙalilan kafin gudanar da zaɓen 2016.

Ya kuma ce shugaban ƙasar ya sake biyan shi kuɗi daga baya.

Mista Trump ya ce ya sake biyan kuɗaɗe, wanda ba laifi ba ne, sai dai ya musanta yin jima'i da matar da kuma yin ba daidai ba ta ɓangaren shari'a.

Shin za a iya kama Trump?

A karshen mako, Mista Trump ya ce ya yi imanin za a kama shi ranar Talata.

Daga baya mai magana da yawunsa ya ce ba a sanar da su batun wata tuhuma da ake masa ba.

A farkon wannan shekarar ne, mai shigar da kara na birnin New York Alvin Bragg, ya kafa wani kwamitin alkalai da zai binciki ko akwai isassun shaidun da za su iya sa a gurfanar da tsohon shugaban ƙasar kan kuɗaɗen da aka biya miss Daniels.

Shi ne wanda zai yanke hukunci ko za a yi tuhuma ko a'a, idan an gabatar da shi.

Wani kwamitin lauyoyi na gudanar da wani zama na sirri, kuma mai gabatar da kara ya kafa shi ne domin tantance ko akwai isassun shaidun da za su iya sa a tuhumi Trump.

Idan aka gabatar da tuhume-tuhumen, zai zama shari'ar laifi ta farko da aka taɓa yi wa wani tsohon shugaban Amurka.

A shafinsa na sada zumunta, Truth Social, Mista Trump ya kira binciken da aka masa a matsayin bi-ta-da-kullin siyasa da tsarin shari'a da ke cike da cin hanci ke yi a kansa.