Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Maris: Watan da aka sace daruruwan mutane a Najeriya
- Marubuci, Azeezat Olaoluwa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Lagos
A daren ranar Asabar sojojin Najeriya su ka sanar da nasarar dakile yunkurin sace mutane 16 daga yankin Kajuru mai fama da matsalar tsaro a jihar Kadunan arewa maso yammacin kasar.
Sai dai a wannan daren, 'yan ta'addar sun kai hari a dai yankin na Kajuru tare da sace gwamman mutane.
Makwanni biyu da suka gabata, arewacin Najeriya ya fuskanci sace-sacen mutane akalla sau shida .
Wannan dai ya alamanta yadda kungiyoyin 'yan ta'adda da ake alakantawa da kungiyar masu ikirarin jihadi ta Al-Qa’ida da Ansar suke kara faɗaɗa ayyukansu a yankin.
Gwamnatin Najeriya ta tsinci kanta cikn tsakja mai wuya cikin makwanni biyu da suka wuce, wanda hakan ya sanya dole jami’an tsaro suka fantsama neman inda aka kai mutanen da aka sace da kokarin kubutar da su, sai dai har yanzu, ko mutum guda ba su yi nasarar kuɓutarwa ba.
Yanayin da ake ciki a kasar ya nuna yadda kungiyoyin 'yan bindiga ke yawo da hankalin jami'an tsaron kasar.
Yawancin 'yan Najeriya na sukar hukumomin ƙasar da ƙin daukar matakan da suka dace da tafiyar hawainiya da suke ganin na karfafa gwiwar masu aikata ta'addanci a ƙasar.
"Gwamnati ba da gaske ta ke ba, kan tsare rayuka da dukiyar jama'a. Jami'an gwamnati ba sa daukar nauyin da ke kan su da muhimmanci. Inda sun maida hankali da mun ga sauyi, da mun ga ingantuwar aikin jami;an tsaro", in ji Malam Isa Sunusi daraktan kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International a Najeriya, a hirarsa da BBC.
A ranar 6 ga watan Maris ne aka fara satar farko a watan nan, kuma an yi ne a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram sun sace akalla 'yan gudun hijira 200, yawancinsu mata da kananan yara a lokacin da suka shiga jeji yin ice.
Duk da kaddamar da nemansu da sojoji suka yi, amma hakan ta gagara, babu wanda akayi nasarar kubutarwa.
Washegari wato ranar 7 ga watan dai na Maris, 'yan bindiga suka tasa keyar dalibai kusan 300 daga makarantar firamare da sakandare a jihar Kaduna.
Daga bisani gwamnatin jihar ta sanar cewa dalibai 28 daga cikin wadanda 'yan bindigar suka sace sun tsere daga hannunsu.
A wata sanarwa wakiliyar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF a Najeriya, da Cristian Munduatehe ta fitar, ta yi alla-wadai da yadda ake yawan samun matsalar sace dalibai a kasar kamar haka.
Sanarwar ta kara da cewa hakan ya nuna yadda matsalar ta yi kamari ana kuma bukatar gwamnati ta dauki matakin gaggawa kan hakan.
A ranar 9 ga watan Maris, ‘yan bindiga sun sace dalibai ‘yan makarantar allo 15 a wata makaranta da ke jihar Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya.
Kwanaki biyu bayan nan, wau da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna tare da sace mutane 61.
Hare-hare na baya-bayan nan ma sun faru ne a Kajuru, inda ‘yan bindigar suka sace akalla mutane 100, yawanci mata da kananan yara.
Da alama dai alwashin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka, lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki, na magance matsalar tsaro na fuskantar cikas a daidai lokacin da aka fuskanci wadannan sace-sacen mutane cikin kankanin lokaci.
Duk kokarin da BBC ta yi domin jin ta bakin jami’an gwamnati kan mataki ko shirin da suke yi na magance matsalar sace-sacen mutane, hakarmu ba ta cimma ruwa ba.
Babu cikakken bayan ikan dalilan da suka san ya ake samun yawaitar sace-sacen mutane a dan tsakanin nan, dai dai a baya akwai rahotannin yadda ‘yan bindiga ke tilastawa matan da suka sace yi musu girki da sauran aikace-aikace.
‘Yan bindigar da suka sace dalibai a farkon watan nan sun bukaci a biya kudin fansa kafin su sake su, amma gwamnati ta kafe ba za ta biya ko kwabo ba.
Satar mutane domin neman kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya, said ai biyan kudin fansar babban laifi ne akasar.