Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama mai kamfanin Crypto na FTX a ƙasar Bahamas
'Yan sandan Bahamas sun kama Sam Bankman-Fried, mutumin da ya kafa kamfanin hada-hadar kirifto amma jarinsa ya karye wato FTX, in ji atoni janar na ƙasar.
Bahamas ta ce ta karɓi sanarwa a hukumance daga Amurka kan tuhume-tuhumen aikata laifi da ake yi wa Mr Bankman-Fried.
A watan jiya ne kamfanin FTX ya gabatar da takardun karyewar jari a Amurka, abin da ya sa masu hada-hadar kirifto da yawa a kamfaninsa suka kasa janye kuɗaɗensu.
Shi ne kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na biyu mafi girma a duniya, inda yake cinikin kwabban kirifto na kimanin dala biliyan goma a kullum.
"Tun farko da yamma ne, hukumomin Bahamas suka kama Samuel Bankman-Fried bisa roƙon da Gwamnatin Amurka ta yi, dangane da wata tuhuma da Lardin Kudancin New York ya shigar. Muna sa ran miƙa rufaffiyar takardar tuhumar da safe kuma a lokacin za mu yi ƙarin bayani," a cewar wani saƙon tuwita daga ofishin Lauyan Amurka a Manhattan.
A jerin hirarraki da ganin da aka yi masa cikin bainar jama'a a 'yan makonnin nan, Mista Bankman-Fried ya amsa cewa an tafka kura-kurai a kamfaninsa amma ya nemi nesanta kansa daga zarge-zargen gudanar da haramtattun harkoki.
"Ban taɓa yunƙurin aikata almundahana ba," ya faɗa a wani taron jaridar New York Times a ƙarshen watan jiya.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne kamfanin FTX ya shigar da takardun karyewar jari don samun kariya a ɗaya daga cikin karayar jari mafi girma a hada-hadar kuɗin kirifto, bayan masu hada-hada sun cire dala biliyan 6 daga kamfanin a cikin kwana 3 kuma abokin hamayyarsa Binance ya yi watsi da wata yarjejeniyar ceto FTX.