Cutar ƙyanda da sankarau na yaduwa a wasu jihohin Najeriya

Masana lafiya a Najeriya na gargadi kan bazuwar cutar sankarau da ƙyanda a wasu sassan kasar, wadda ake alakantawa da yanayin zafin da ake ciki da ke kara ta'azzara lamarin.

Bayanai na cewa a wasu jihohin Najeriyar mutane da dama sun rasa rayukansu sanadiyar cutar sankarau.

Bazuwar cutar na ɗarsa fargaba a zukatan al'ummar da cutukan suka bulla a yankunansu.

Jihohi kamar Kano da Jigawa da Yobe na daga cikin wadanda aka bayyana cutukan sankarau da ƙyanda sun bulla.

Farfesa Isa sadiq Abubukar daraktan cibiyar binciken cutuka masu yaduwa a jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce cutukan ba su da alaka da lokacin zafi, inda ya ce tun kafin lokacin ake kamuwa da cutar.

Ya kuma ce alamun cutar sankarau na farawa ne daga zazzabi, da ciwon kai ka na wuyan mutum na kagewa yadda da ƙyar ya ke juyawa.

''Idan cutar ta yi kamari ta kan janyo rashin gani da kyau, da rashin ji a wasu lokutan ma har takan kai ga mutum ya zama gurgu.''

Y yin da ita kuma cutar kyanda yawanci ta fi kama kananan yara, ''yaro zai fara da mura da zazzabi, idan tafiya ta mika ko haske yaro bai cika son gani ba.

"Kuraje kanana kan feso a jikin yaro, idan ba a dauki matakin gaggauta zuwa asibiti da magani ba takan shafi dukkan gabban yaro da amai da gudawa da rashin cin abinci,'' in ji Farfesa Isa Sadiq.

Masana lafiya dai sun ce ana iya daukar cutar sankarau ta hanyar numfashi, ko iska ta kada inda aka zubar da yawu ana iya daukarta.

Farfesa Isa ya ce akwai hanyoyin da ya kamata mutane su bi domin kare kansu daga wadannan cutukan.

''A tabbatar an yi allurar rigakafin sankarau da ƙyanda, wadda dama ana yi wa yara idan sun kai watanni tara da haihuwa, da kiyaye matakan tsafta kamar wankin hannu da tsaftace muhalli, da nesanta kai daga wadanda suka kamu da cutukan, da bude tagogi lokacin kwanciya bacci, da rage cunkuso lokacin kwanciya barci.''