Yadda APC ta fara faɗawa tarkon rikici a jihar Kano

Lokacin karatu: Minti 3

Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf.

An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan 'ya'yan jam'iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar.

Shugabancin APC ne ya ba da umarnin gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a wani mataki na ɗinke duk wata ɓaraka gabanin babban zaɓen jam'iyyar da ke tafe.

Dama dai tun da farko masana siyasa a Najeriya sun yi hasashen samun rikici a tsakanin ƴaƴan jam'iyyar APC musamman bayan shigowar gwamna Abba Kabir Yusuf.

Rahotanni na cewa an samu musayar yawu da cecekuce a yayin taron masu ruwa da tsaki a matakin kananan hukumomi.

Na baya-bayan nan shi ne taruka biyu da aka yi a karamar hukumar Kano Municipal inda ɓangaren da ke biyayya ga tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ƙarƙashin jagorancin Muntari Ishaq Yakasai da Baffa Babba Dan Agundi da Injiniya Sagir Koki, suka yi nasu taron.

Kodayake koda BBC ta tuntuni Baffa Babba Dan Agundi, kan dalilin yin nasu taron, ya shaida ma ta cewa ba shi da masaniya a kan taron, sannan kuma duk wanda ke da ruwa da tsaki a jam'iyyarsu ta APC an gayyace shi sai dai wanda bai samu halarta ba.

Ya ce," Mu ba mu da matsala duk wanda zai kira taro don haɗin kan jam'iyya za mu je sai dai idan ba a sanar da mu ba."

A bangare guda kuma, bangaren da ke biyayya ga sanata Barau Jibril, karkashin jagorancin Salisu Maje Ahmed Gwangwazo, wato Alhajin Baba da sauran kusoshi, su ma sun gudanar da nasu taron.

Alhaji Hamza Darma ya shaida wa BBC cewa, su suna ganin a Municipal, wanda ya fi matsayi shi ne danmajalisar wakilai na karamar hukuma wato Injiniya Sagir Koki, "don haka shi ne idan ya kira taro kowa zai je," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa," Muna so a rinka bin tsari don ba ma rigima da kowa, kuma ai shi injiyan ma taron wancan bangaren ya je don ko da na ce masa kada ya je cewa ya yi ai gayyatarsa aka yi don haka shi so yake a ɗinke duk wata ɓaraka a zama tsintsiya madaurinki daya."

Taron da aka yi a kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da Tofa, shi ne aka fara samun hatsaniya.

Akwai bayanan da ke cewa a karamar hukumar Danbatta ma an samu rashin jituwa.

Wasu bayanai sun ce gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da umarnin gudanar da taruka a kananan hukumomin jihar tun ranar da ya koma jam'iyyar APC.

Masana siyasa a Najeriya irinsu Malam Kabiru Sufi na ganin irin ruguguwar da ake yi wa APC, za a kai gaɓar da jam'iyyar za ta fashe.

"Duk wani rikici na ɓoye zai fito saboda yawan da aka yi wa jam'iyyar da kuma haɗuwa gida ɗaya da aka yi tsakanin waɗanda ba sa ga maciji wanda zai jefa jam'iyyar cikin rikici.

Masanin ya ce za a iya ɗaukar dogon lokacin kafin abubuwa su tafi daidai a APC a Kano musamman tsakanin ɓangarori biyu da suka daɗe suna caccakar juna.