Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Akpabio ya yi barazanar fitar da Oshiomhole daga zauren majalisar dattawa
An samu yamutsi a zauren Majalisar Dattijai yayin da aka samu saɓani tsakanin Shugaban Majalisar Godswill Akpabio da ɗanmajalisar mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole.
Sanatocin biyu sun shafe kusan minti 10 suna ta sa-in-sa, kamar yadda ƴanjarida suka bayyana har ma ta kai Akpabio ya gargaɗi Oshiomhole cewa za a yi amfani da dokar majalisa wajen fitar da shi daga zauren idan har yaƙi nuna ɗa'a.
Cacar bakin ta faru ne sakamakon wasu sauye-sauye da aka yi wa dokokin majalisar waɗanda suka shafi yadda za a zaɓi jagorori da shugabannin majalisar. Shugabannin majalisar su ne shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa yayin da jagororin suka haɗa da shugaban masu rinjaye na majalisar da mai tsawatarwa na majalisar da shugaban marasa rinjaye da sauran mataimaka.
Dokokin majlisar datawan na ɗauke da ƙa'idoji da suka shafi yadda ƴanmajalisar za su tafiyar da al'amuransu da tsarin zama a majalisar da kuma hukuncin da aka tanada ga sanatocin da suka saɓa doka.
Misali, a Maris ɗin 2025, majalisar ta dakatar da ɗaya daga cikin mambobinta, Natasha Akpoti-Uduaghan tsawon wata shida kan zargin saɓa dokar majalisar sakamakon ƙin zama a kujerar da aka tanadar mata.
Waɗanne sauye-sauye ne aka yi wa dokokin majalisar da ke janyo cece-kuce?
Bisa tsarin da aka saba, an ware matsayin shugaban majalisar ne ga sanatocin da suka daɗe majalisar, ba sabon-shiga ba, sa dai gyaran da aka yi wa dokokin ya ƙara wasu tanade-tanaden.
Manyan sauye-sauyen da sanatocin suka yi sun shafi doka ta huɗu da ta biyar na dokokin majalisar dattawan, lamarin da Adams Oshionhole ya ce da sake.
A cewar sauyin da aka yi wa doka ta huɗu, dole ne a yanzu a duba daɗewa da ƙwarewa wajen zaɓen shugabannin majalisar kamar;
- Tsoffin shugabannin majalisar dattawa
- Tsoffin mataimakan shugaban majalisar dattawa
- Tsoffin shugabannin majalisar dattawa
- Sanatocin da suka kammala aƙalla wa'adi ɗaya na tsawon shekara huɗu
- Sanatocin da suka taɓa zama ƴanmajalisar wakilai
- Sabbin sanatoci (idan har ba a samu wasu daga daɗaɗɗun ƴanmajalisar ba)
Misali, hakan na nufin bayan zaɓen 2027, idan Godswill Akpabio ya sake lashe zaɓe kuma ya ce zai yi takarar shugaban majalisar dattawa, dole a fara la'akari da shi kafin sauran ƴantakara.
Ita kuma doka ta biyar da aka yi wa gyara ta bayyana cewa kafin sanata ya cancanci neman riƙe wani muƙami a majalisar, dole sai wannan ɗantakarar ya kasance sanata tsawon aƙalla wa'adi biyu a jere kafin neman takarar.
Hakan na nufin sanatocin da ba sa cikin majalisa ta tara da ta 10 ba za su iya neman wani muƙami ba a majalisa ta 11.
Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Oyelola Ashiru, wanda ya yi magana a madadin shugaban masu rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele, ya kare sabbin sauye-sauyen inda ya ce za su taimaka wajen ƙara ƙarfafa tsare-tsaren majalisar da kuma inganta ayyukansu.
Ashiru ya kuma ce sashe na 60 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, ya bai wa majalisa ikon yin dokokin da za su tafiyar da al'amuransu na cikin gida har da ƙa'idojin da suka shafi zaɓen shugabanni da jagorori.
Tsarin yi wa dokokin majalisar dattawa gyara ba kamar yadda ake yi na kundin tsarin mulkin ƙasa ba ne saboda ba ya buƙatar amincewar shugaban ƙasa kafin zama doka. Abin da kawai ake buƙata shi ne samun rinjaye kuma hakan ne zai sa a fara aiki da sauye-sauyen.
Me ya janyo sa-in-sa tsakanin Oshiomhole da Akpabio?
A ranar Laraba, bayan soma zaman majalisar dattawa, sai Akpabio ya fara karanto abubuwan da aka yi a zaman ranar da ta gabata da kuma abubuwan da ƴanmajalisar suka amince da su, sai dai a lokacin da ya kai ga batun sabbin sauye-sauyen ne Oshiomhole ya ɗaga hannu da nufin yana da magana.
Sai dai Akpabio nan da nan ya bayyana cewa lokacin da ya kamata ya yi tsokaci ya wuce amma Oshiomhole ya dage cewa sai ya bayyana abin da ke ransa.
Sanatoci kamar mai tsawatarwa na majalisa, Tahir Monguno, sun yi ƙoƙarin sa baki a lamarin amma Oshiomhole bai yi shiru ba - ya ci gaba da ɗaga murya.
A ƙarshe Akpabio ya gargaɗi sanatoci da su kasance sun nazarci dokokin majalisar kuma su kasance masu aiki da su.
"Babu sabon sanata a cikinmu. Idan ɗansanda ne kai, dole ne ka sa kayan sarki, idan kuma soja ne, dole ne ka sa kakin soja, idan kuma sanata ne kai, dole ka bi doka," in ji Akpabio.
"Ba wai kawai ka je gida ka cike fom ka tsaya takara ba, ka zo nan ba tare da sanin komai kan doka ba..., Don haka, don Allah Sanata Oshiomhole, a karo na ƙarshe, idan ka ci gaba da saɓa ƙa'ida, za mu yi amfani da waɗannan dokokin wajen fitar da kai daga zauren majalisar. Wannan ne gargaɗi na ƙarshe," Akpabio ya faɗa Oshiomhole kuma da alama gargaɗin ya yi aiki domin Sanata Oshiomhole ya daina magana har ma aka ci gaba da zaman majalisar.
Abin da mutane ke cewa kan sabbin dokokin majalisar dattawa
Dr. Chibuzor Okereke, masanin harkokin siyasa ya ce ba za a iya aiwatar da sabbin dokokin ba saboda a cewar shi, abin da kawai ake buƙata a ranar zaɓen jagororin majalisar dattawa shi ne ɗanmajalisa ɗaya ya zaɓi wani kuma a samu goyon bayan zaɓin daga wajen wani sanatan.
A cewar doka ta 4 (3) ta dokar majalisar dattawa, 'ba a muhawara ko tambayoyi ko ɗaga ƙafa yayin zaɓen jagororin majalisa' don haka babu wani ƙudiri da zai ƙalubalanci cancantar ɗantakara," in ji Okereke yayin wata hira ta talabijin.
Wasu mutane da suka yi tsokaci kan batun a shafukansu na sada zumunta sun ce sabbin dokokin da alama na neman toshe wa gwamnan Imo Hope Uzodinma dama wanda ake raɗe-raɗin cewa yana hangen kujerar majalisar dattawa.
Uzodinma ya taɓa yin sanata inda ya wakilci Imo ta yamma tsakanin 2011 zuwa 2019 kuma tuni ya samu fom ɗin tsayawa takarar sanata a 2027 lokacin da wa'adinsa ya zo ƙarshe a matsayin gwamna.
Wani mai amfani da shafin X @Ifedayo_Johnson, ya ce, ba zai yiwu dokokin majalisa su rinjayi kundin tsarin mulkin ƙasa ba wanda sashe na 59 ke cewa "za a samu shugaba da mataimakin shugaban majalisa waɗanda ƴan'uwansu ƴanmajalisa suka zaɓa".
"Zaɓen daɗaɗɗun ƴanmajalisa a matsayin shugaban majalisar dattawa wata al'ada ce kawai. Kowa na iya neman kujerar," in ji shi.