Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da Majalisar Dattawan Najeriya ta cimma a zamanta kan dokar zaɓe
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da aika sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe kai-tsaye ta na'ura.
Majalisar ta kuma ce aika sakamakon kai-tsaye ta na'ura zai kasance hanyar farko ta aika sakamakon, amma idan an samu matsalar intanet, INEC za ta yi amfani da takarda a rubuce wajen aika sakamakon kamar yadda aka saba yi a baya.
Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da ƙudirin a lokacin zaman gaggawa da majalisa ta yi kan dokar, yayin da shugaban majalisar ya Godswill Akpabio ya amince da ƙudirin bayan amincewar sauran ƴanmajalisar.
Daga nan ne kuma majalisar ta kafa kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki da majalisar wakilai don tsefe dokokin kamar yadda tsarin amincewa da dokoki ya tanadar.
Majalisar ta kira zaman gaggawar ne bayan da ƙungiyoyin fararen hula da jam'iyyun hamayya suka mamaye harabar majalisar dattawan a ranar Litinin domin gudanar da zanga-zanga don nuna adawarsu kan ƙin amincewa da majalisar ta yi na wajabta aikata sakamakon zaɓe ta na'ura kai tsaye daga kowace rumfar zaɓe.
Tun da farko Majalisar Wakilan ƙasar ta amince ta duka ƙudurorin gyaran dokar zaɓen ba tare da ƙebe kowane ba.
To sai dai a nata ɓangare majalisar dattawan ta keɓe sashen da ya yi magana kan wajabta aika sakamakon kowace rumfa kai-tsaye ta na'ura ta yadda kowane ɗan ƙasa zai gan shi daga duk inda yake.
Majalisar ta kafa hujja da rashin ingantaccen intanet da rashin tsaro a wasu ƙauyukan ƙasar a matsayin dalilinsu na rashin wajabta aikata sakamakon zaɓen kai-tsaye ta na'ura.
Me ya rage a yanzu?
Abin da ya rage yanzu shi ne zaman da kwamitocin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da wakilai za su yi domin kammala tsafe dokokin, sannan su koma majalisun domin gabatar da abin da suka cimma don aminc ewar ƙarshe ta majalisar.
Daga nan kuma sai a aika wa shugaban ƙasa domin sanya hannu kan dokokin domin fara aiki da su.
Yayin da yake bayyana mambobin kwamitin Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya ce ana buƙatar kwamitin ya fara aiki cikin gaggawa tare da takwararansa na Majalisar Wakilai domin tabbatar da abubuwan da ake buƙata.
''Idan kun yi aikin cikin gaggawa hakan zai bai wa shugaban ƙasa damar sanya hannu kan doikar cikin wannan wata na Fabrairun da muke ciki'', a cewar Shugaban majalisar dattawan.
Mambobin kwamitin sun haɗa da Sanata Simon Bako Lalong a matsayin shugaban kwamitin.
Mambobin sunm haɗa da: Sanator Mohammed Tahir Monguno da Sanata Adamu Aliero da Sanator Orji Uzor Kalu da Sanator Abba Moro.
Sauran sun haɗa da: Sanator Asuquo Ekpenyong da Sanator Aminu Iya Abbas da Sanator Tokunbo Abiru da Sanator Niyi Adegbonmire da Sanator Jibrin Isah da Sanator Ipalibo Banigo da kuma Sanata Onyekachi Nwebonyi.
Me ake nufi da aika sakamako ta na'ura?
An kwashe gomman shekaru ana zargin tafka maguɗi a zaɓukan Najeriya, musamman lokacin tattara sakamakon zaɓe.
A lokacin zaɓe galibi zaɓuka kan tafi yadda ya kamata a rumfunan zaɓe, to amma galibi matsalar kan taso ne idan aka bar rumfunan zaɓe aka tafi cibiyar tattara sakamako, haka ma cibiyar tattara sakamako kan zama wata matattarar maguɗi kamar yadda wasu ke zargi.
Domin magance wannan matsala, a zaɓen 2023 hukumar INEC ta gabatar da na'urorin fasahar zamani, kamar ta BVAS da ke tantance masu kaɗa ƙuri'a, da kuma buɗe shafin tattara sakamako da ake kira iReV.
Manufar hakan shi ne idan aka kammala tattara sakamakon zaɓen sai a aika shi cikin wannan shafi da kowa zai iya gani.
Aika sakamakon zaɓen ta na'ura zai bayar da dama a aika sakamakon zaɓen da aka tattara a kowace rumfa zuwa cikin wannan shafi, wanda kuma kowa zai iya gani daga ko'ina idan ya shiga shafin.
Ana ganin hakan zai rage matsalolin da ke tasowa a cibiyar tattara sakamakon zaɓe.
To sai dai babu wata dokar ƙasa da ta wajabta aiki da waɗannan na'urori ya sa amfani da su bai zama tilas ba, wannan matsala ta rashin wajibcin doka a kan na'urorin ya haifar da manyan matsaloli a zaɓukan 2023.
Ga mafi yawan ƴan Najeriya, matsalar fasaha da aka samu a zaɓukan baya, ko zaɓin amfani da su, ya zama wata alama ta gazawar tsarin zaɓukan ƙasar.
Masu suka na zargin cewa barin 'aika sakamakon zaɓe ta na'ura' a matsayin zaɓi, ya bai wa wasu ƴansiyasa damar samun ƙarfin iko maimakon masu zaɓe.
A ranar Litinin ne majalisar ta kira zaman gaggawa cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 8 ga watan Fabrairu, wadda aka rarraba wa sanatoci wanda magatakardar majalisar dattawa, Emmanuel Odo ya sanya hannu a takardar.
A cikin wasiƙar, Odo ya ce ya ɗauki matakin ne bisa umarnin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Duk da cewa an yi gyare-gyare da dama a cikin dokar, hankalin jama'a ya fi karkata ne kan wani sashe da ya haifar da ce-ce-ku-ce, wato ƙin amincewa da wajabcin tura sakamakon zaɓe ta hanyar na'ura daga rumfunan kaɗa ƙuri'a yadda mutane za su iya gani.