Wace jam'iyya ce NDC kuma wane tasiri za ta yi a 2027?

Lokacin karatu: Minti 5

Masu lura da al'amuran siyasa a Najeriya na ci gaba da aza ayar tambayar ko tsoffin ƴantakarar shugaban Najeriya biyu a zaɓen 2023, ƙarƙashin jam'iyyun LP da NNPP, Peter Obi da Sanata Rabi'u Kwankwaso za su iya kafa gwamnati a 2027 ƙarƙashin sabuwar jam'iyar NDC da suka shiga.

NDC ta kasance jam'iyya ta shida da Kwankwaso ya shiga tun daga 1999 zuwa yanzu, yayin da ta kasance ta biyar da Peter Obi ya shiga tun 2003.

A ƙarshen makon da ya gabata ne tsoffin gwamnonin jihohin Anambra da Kanon suka sanar da komawa jam'iyyar NDC bayan fitar sui daga ADC.

Yayin da wa'adin zaɓukan ditar da gwani ke ƙara ƙaratowa, ƴansiyasar biyu na ƙoƙarin samun jam'iyyar da za su yi takarar 2027 a cikinta.

Shun shiga NDC tare da magoya bayansu, da ke fatan goya musu baya a zaɓen 2027.

Sai dai tambayar da masana siyasa ke ci gaba da yi har yanzu shi ne ko ƴansiyasar biyu za su iya fuskantar APC mai mulki a zaɓen 2027 da wannan sabuwar jam'iyyar da suka shiga.

Jam'iyyar NDC

Nigerian Democratic Congress (NDC) na ɗaya daga cikin jam'iyyun siyasa biyu da INEC ta yi wa rajista a baya-bayan nan.

Abin da hakan ke nufi shi ne an yi wa jam'iyyar rajista a 2026 a hukumance.

A watan Fabrairun 2026 ne INEC ta miƙa wa NDC takarkar shaidar zama jam'iyya.

Bayanan da ke shafin jam'iyyar na intanet, sun nuna cewa tana da rassa a ƙananan hukumomin Najeriya 774, yayin da fiye da mutum miliyan ɗaya suka yi rajista da jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar na ƙasa shi ne Sanata Moses Cleopas, haka kuma jam'iyyar na da mambobin kwamitin zartaswa.

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Henry Seriake Dickson ne ya kafa jam'iyyar.

Yanzu haka Dickson, ne ɗan majalisar tattawa mai wakiltar Bayelsa ta Yamma.

A cewar Seriake Dickson, tun a 2017 ya fara yunƙurin yi wa NDC rajista, amma yunƙurin nasa ya gamu da cikas, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

Daga baya a 2025, Dickson ya sake yunƙurin yi wa jam'iyyar tasa rajista, lokacin da INEC ta ƙara wa'adin yi wa jam'iyyu rajista.

Ƙungiyoyi 171 ne suka aika buƙatun neman rajistar zama jam'iyya a wancan lokacin.

Daga baya NDC ta samu wasiƙa daga INEC cewa alamar jam'iyyar na yatsu biyu, ya yi kama da na da jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya.

Nan take NDC ta shigar da INEC ƙara gaban kotu kan batun, inda kotu ta ce alamomin jam'iyyun biyu ba su yi kama ba, don haka INEC ta yi mata rajista.

Waɗanne fitattun ƴansiyasa ne a NDC?

A matsayinta na sabuwar jam'iyya NDC, ba ta da fitattun ƴansiyasa a cikinta, in ban da shugabanta na ƙasa, sai waɗannan jiga-jigan da a yanzu suka shigeta.

To amma ya zuwa yanzu jam'iyyar ta samu wasu fitattun ƴansiyasa da suka shiga cikinta.

Daga ciki akwai

  • Tsohuwar ƴartakarar gwamnan jihar Adamawa Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani, gabanin shigar su Kwankwaso.
  • Sanata Kabiru Marafa, tsohon sanatan Zamfara ta Tsakiya.
  • Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
  • Rabiu Kwakwanso, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP.
  • Sai ƴan jamalisar wakilai na tarayya 16 da suka sanar da sauya sheƙa daga ADC zuwa NDC a ranar Talata.

Wace dama Obi da Kwankwaso ke da ita a NDC?

A lokacin zaɓukan 2023, Peter Obi ƙarƙashin jam'iyyar LP ya samu ƙuri'a kimanin miliyan 6.1, inda ya zo na uku a zaɓen, yayin da Kwakwanso ta samu ƙuri'a miliyan 1.4, ya kuma zo na huɗu, inda duka suka sha kaye a hannun Shugaba Tinubu na APC.

Da dama cikin masana siyasa na ganin haɗuwarsu da Atiku a ADC zai ƙara wa ƴan hamayyar ƙarfi yayin da ake tunkarar zaɓukan 2027.

Amma sai shari'ar rikicin shugabanci da ake ciki a ADC ta tilasta wa Obi da Kwankwaso ficewa zuwa NDC, sai dai ba a sani ba ko za su samu tikitin takarar 2027.

To amma wasu masana siyasar na ganin yawan sauya sheƙar da ƴansiyasar biyu ke yi, ka iya rage musu yawan magoya baya.

Jam'iyyun da Kwankwaso ya shiga daga 1999

Sanata Rabiu Kwankwaso na daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP a 1998, inda kuma ya tsaya mata takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen 1999, ya kuma yi nasara.

Kwankwaso ya sake tsayawa takarar gwamnan Kano domin neman wa'adin mulki na biyu a 2011, inda kuma ya yi nasara.

Sai dai a ƙarshen mulkin nasa, Kwankwaso ya samu saɓani da gwamnatin tarayya ta wancan lokacin ƙarƙashin Jonathan, lamarin da ya sa shi da wasu gwamnoni suka kafa ƙungiyar sabuwar PDP, tsagin Sanaka Kawu Baraje, daga baya kuma ya shiga APC.

Ya tsaya takarar sanatan Kano ta tsakiya a 2015 ƙarƙashin APC, ya kuma yi nasara.

Sai dai a shekarar 2018 ya sake komawa PDP bayan ficewa daga APC saboda saɓani da gwamnan Kano na wancan lokaci, Abdullahi Ganduje.

Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, amma ya yi rashin nasara a zaɓen fitar da gwani.

A ranar 30 ga watan Maris ɗin 2022, tsohon gwamnan na jihar Kano ya shiga jam'iyyar NNPP, kwana guda bayan ficewarsa daga PDP.

Jagoran kwankwasiyyar ya kuma tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, sai dai bai yi nasara ba.

Duk da rashin nasarar da ya yi, jam'iyyarsa ta NNPP ta samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano mafi yawan jama'a a arewacin ƙasar.

Shekara huɗu bayan komawarsa NNPP, Sanata Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar tare da shiga haɗakar ADC a ranar 29 ga watan Maris 2026.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga NNPP ne la'akari da halin da siyasar Najeriya ke ciki, wanda ke bukatar haɗin kai.

Sai dai kimanin wata biyu bayan komawarsa ADC, Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar tare da shiga NDC a ranar 3 ga watan Mayun 2026.

Jam'iyyun da Peter Obi ya shiga daga 1999 zuwa yau

Peter Obi ya shiga jam'iyyar AFGA, a farkon kafa ta a 2002, inda ya samu zarafin tsaya mata takarar gwamnan jihar Anambara da ke kudu maso gabashin Najeriya a 2003.

Ya kuma yi nasara, amma sai da aka tafka shari'a a kotu, lamarin da ya sa sai a 2006 a fara mulkinsa, sannan ya ƙare wa'adinsa na biyu a shekarar 2014.

A ranar 7 ga watan Oktoban 2017 ne tsohon gwamnan ya fice daga AFGA zuwa PDP.

A zaɓen 2019 Obi ya yi takara da Atiku a PDP a matsayin mataimaki, sai dai sun sha kaye a hannun Marigayi Muhammadu Buhari.

Sai kuma a shekarar 2022, Peter Obi ya fita daga PDP ya shiga LP, tare da tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023, sai dai bai yi nasara ba.

A ranar 31 ga watan Disambar shekara mai ƙarewa ne Peter Obi ya sanar da shiga jam'iyyar ADC a hukumance bayan kwashe watanni ana tattaunawa tsakanin jiga-jiganb adawar ƙasar.

Sai kuma a ranar Lahadi 3 ga watan Mayu, tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar ya koma jam'iyyar NDC bayan ficewarsa daga ADC.