Yadda Hisba ta kama matasan da ke musayar matansu na aure a Bauchi

Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar Hisba da ke Azare a ƙaramar hukumar Katagum ta jihar Bauchi ta ce ta kama da tsare wasu mutum bakwai da ake zargi da musayar matansu na aure a tsakaninsu.

Kwamandan rundunar Hisba a yankin, Malam Ridwan Muhammad Khairan wanda ya shaida wa BBC ya ce sun yi kamun ne bisa zargin mutanen da aikata laifin da ba a taɓa ji ko ganin irinsa ba.

Hisba ta ce aikin matasan ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci da ta taskace kowacce mace ga namiji guda.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum a Bauchi sun yaba da samamen da Hisbar ta ƙaddamar har ta kama mutanen kasancewar idan aka bar al'amarin haka to zai iya kai wa ga yaɗuwa.

Dalilin da'awar musayar mata

Mutanen guda bakwai da Hisba ta kama kangararrun mambobin wata ƙungiya ne mai suna Wuddadu.

An dai ce masu musayar matan sun ɗabbaƙa fahimtar tasu bisa dogaro da mafarkin da ɗaya daga cikinsu ya yi dangane da musayar matan nasu.

"Ɗaya daga cikinsu mai suna Muhammad Awwal ya tabbatar mana da cewa ya samo wannan fahimta ne daga mafarki, inda ya ce wai ya yi mafarki ne annabi kuma wannan ya sa suka lallami matansu wajen aikata wannan aiki," in ji Malam Ridwani Muhammad Khairan, shugaban hukumar Hisba na shiyyar Katagum a jihar ta Bauchi.

Yadda asiri ya tonu

Malam Ridwani Muhammad Khairan, shugaban hukumar Hisba na shiyyar Katagum a jihar ta Bauchi a wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya shaida cewa al'amarin masu musayar matan ya kwashe shekaru biyu yana faruwa a garin na Azare ba tare da samun labari ba.

Sai dai kuma ya shaida wa BBC cewa da dubunsu ta cika sai daya daga cikin matan da ake musayar ta tona asiri.

"Daya daga cikin matan ce ta ce ita ba za ta iya wannan maguzancin ba shi ya sa ta fice daga cikinsu," wanda hakan ne ya sa asiri ya fara tonuwa.

Daga nan ne kuma sai wasu jagororin ƙungiyar Wuddadu suka samu bayani inda suka gargaɗi mutanen bakwai cewa hakan ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci da kuma na ƙungiyar amma suka ƙi dainawa.

"Akwai wata ƙungiya da ake kira Ƙuddadu sun yi cincirindo suka zo suka same ni cewa akwai wasu mutane a cikinsu da suka fito da wata da'awa wadda ba a gamsu da ita ba....mun kuma gayyato mutanen muka zauna da su kuma suka tabbatar min da abin da ake zargin nasu..," in ji

Wace ƙungiya ce Wuddadu?

Ana kiran wannan ƙungiya ne da Wuddadun Nabiy wadda wani ɓangare ne na mabiya ɗariƙar Sufanci ta Tijjaniyya da ta gina kusanci da ubangiji ta hanyar gyaran ruhi da tsantseni.

Kamar sauran ƙungiyoyin Musulunci, ita ma Wuddadu ta fahimci cewa a cikinsu akwai wadanda suka wuce gona da iri kuma ƙungiyar ta ga wajibcin taka musu burki.

"Da farko shugaban ƙungiyar ta Wuddadu ne ya fara jan hankalin ɓatagarin cikin nasu masu wannan yaɗa fasadi amma suka ƙi ji. Wannan ya sa jagororin ƙungiyar suka garzaya zuwa ga Hisba inda suka sanar da ita abin da ke faruwa," kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito.