Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Goodluck Jonathan zai iya tasiri idan ya tsaya takara a zaben 2027?
Yayin da siyasa a Najeriya ke ci gaba da ɗaukar sabon salo, masana a harkokin siyasa a ƙasar sun fara tsokaci bayan fitar wata sanarwa daga tsohon shugaban ƙasar Goodluck Ebele Jonathan ta yiwuwar tsayawa takara a zaɓen 2027 da ke tafe.
Ɗimbin magoya bayan tsohon shugaban na Najeriya ne dai suka kai masa ziyara a gidansa ranar Alhamis, inda Jonathan ya ce zai yi tuntuɓa kafin yanke hukuncin ko zai tsaya ko ba zai shiga takarar shugabancin ƙasar ba.
Yanzu haka dai a iya cewa ta bayyana ƙarara, dangane da batun zawarcin da aka daɗe ana yi wa tsohon shugaban Najeriyar, Dokta Goodluck Jonathan, don ya fito takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ke tafe.
Domin kuwa takanas ta Kano, wasu matasa daga cikin ɗimbin magoya bayansa suka kai masa goron gayyata har gida, suna neman ya fito ya gwada sa'arshi sai dai ya nuna musu cewar fitowa takarar ba abun wasa ba ne.
"Kun nemi in fito takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ke tafe, ita fa takarar muƙamin shugaban ƙasa ba wasa ba ne. Amma dai na ji abin da kuka faɗa, kuma zan yi tuntuɓa game da haka"
Me masana ke cewa?
Masana harkokin siyasa a Najeriya irinsu Dakta Ibrahim Baba Sha-tambaya, malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, na da ra'ayin cewar Goodluck Jonathan na da damar shiga neman takarar shugabancin ƙasar kamar kowanne ɗan Najeriya, saboda yana da wa'adi guda na damar sake tsayawa takarar shugaban ƙasar.
'Wa'adi ɗaya kawai ya yi a kan mulki, in za ka tuna bai yi nasara ba a wa'adi na biyu da ya sake tsayawa, wanda hakan ya ba shi dama kai tsaye wajen ganin shiga wannan takarar. Idan ƴan Najeriya suka bashi goyan baya ya iya kayar da gwamantin APC.
Saboda irin hoɓɓasar da ya yi a lokacin da ya fadi zaɓe ya karɓi faɗuwar ya janyo masa kwarjini a Najeriya, da ma sauran ƙasashen duniya, wanda hakan yasa ake kallon takarar ta sa za ta kasance babbar barazana ga jam'iyya mai Mulki da ma ɗan takarar tata.' In ji Dakta Ibrahim Baba Sha-tambaya.
Masanin ya ce abu ne mai wuya a ce zai futo takarar shugabancin na Najeriya, sai dai hakan ya danganta da irin mahimmanci da girman waɗanda ke kira gare shi ya fito, wanda sune kaɗai za su sa shi shiga takarar.
Abun jira a gani dai shi ne yadda tuntuɓar da tsohon shugaban Najeriyar ya ce zai yi za ta kaya, duk da cewar wasu na ganin abu ne mai kamar wuya ya fiuto ya sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar.