FA ta kare matsayarta ta goyon bayan Kofin Duniya a Saudiyya

Asalin hoton, BBC Sport
Shugaban Hukumar FA ta ce babu wani abin ta da hankali cikin kare matakinta na goyon bayan buƙatar Saudiyya na karɓar baƙuncin Kofin Duniya na 2034
Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa ce ta tabbatar da amince wa Saudiyya ta karɓi baƙuncin gasar a ranar Laraba.
Wadanda za su shirya gasar sun ce suna maraba da kowa, sai dai ana ta sukar ƙasar da take haƙƙin ɗan adam, mata da kuma nuna wariya ga masu auren jinsi.
Hewitt ta shaida wa BBC cewa FA ta yi tambayoyi masu yawa gabanin amincewa da buƙatar Saudiyya.
"Ba wani mataki ba ne mai ta da hanakali, Ina ganin lamari ne da sai da aka yi zuzzurfan bincike a kai.
"Mun ɗauki lokaci mau yawa da hukumomin Saudiyya, mun fahimci yadda suke son karɓar baƙuncin gasar.
"Mun tambaye su abubuwa da dama sun ba mu lokaci sun nuna mana yadda suka ɗauki wannan shiri da muhimmanci, kuma a gani na mafi muhammanci shi ne za mu riƙa aiki da su tare nan da shekaru 10 masu zuwa domin tabbatar da sun cika alƙawuran da suka ɗauka," in ta.
FA ta zauna da hukumar kwallon ƙafa ta Saudiyya domin tattaunawa ɗaya bayan ɗaya kan buƙatarta ta neman karɓar baƙuncin.
Hukumar Kwallo Kafa ta Saudiyya ta tabbatar da cewa za ta samar da yanayi mai kyau ga duk wani baƙo da zai je kallon wasan - ciki har da magoya baya masu ra'ayin LGBTQ.
"Mun gamsu da amsar da suka ba mu, kuma wannan magana ce ta aiki tare," in ji Hewitt, wadda ta ce FA ce ta bai wa masu shirya gasar wadanda za su riƙa tuntuba.
"Gasar ba kawai akan ƙarbar baƙunci ake ba. Magana ce ta wadanda suka dade suna aiki domin hakan ta tabba."
Kofin Duniya na 2034 zai sama na biyu da za a yi a Gabas ta Tsakiya - an fara ne da Qatar a 2022.
Kimar Saudiyya ta taɓu a idon duniya tun bayan kisan da aka yi wa Jamal Khashoggi a 2018, Wani shahararren ɗan jarida da ke zama a Amurka wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnatin Saudi.











