Wasa da wuta, da bikin nuna al'adu cikin hotunan Afirka

    • Marubuci, Danai Nesta Kupemba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Zaɓaɓɓun hotuna masu ƙayatarwa na wannan mako daga faɗin nahiyar Afirka da ma wasu wuraren:

Wata matashiya da ta halarci bikin da ake kira gaɗa

Asalin hoton, Tiksa Negeri / Reuters

Bayanan hoto, Wata matashiya da ta halarci bikin da ake kira gada, wanda ake kwashe mako guda ana bukukuwa domin canja shugaban ƙabilar Borana na garin Arero da ke ƙasar Habasha wanda ake yi duk bayan shekara takwas.
Masu tseren keke

Asalin hoton, Brenton Geach / Getty Images

Bayanan hoto, Haka ma dai a ranar ce aka yi tseren keke na gasar tseren birnin Cape Town na shekara-shekara
Masu wasa da wuta

Asalin hoton, Marvellous Durowaiye / Reuters

Bayanan hoto, Masu wasa da wuta suna nishaɗantar masu kallo a ranar rufe gasar damben zamani na Ecowas wanda aka yi a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja a ranar Asabar 8 ga watan Maris
Buɗa-baki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu ƴan Sudan suna shirin buɗa-baki a ranar Juma'ar da ta gabata
Ƴan Baye

Asalin hoton, Zohra Bensemra / Reuters

Bayanan hoto, A birnin Touba mai daraja a Senegal, ƴan ƙungiyar Baye sun yi taron ibada domin watan Ramadan a ranar Juma'a da ta gabata, wato ranar 7 ga watan Maris
Mai aski

Asalin hoton, Donwilson Odhiambo / Getty Image

Bayanan hoto, Wani mai aski yana yi wa fitaccen mai zane Coster Ojwang aski cikin natsuwa a lokacin da ake sake buɗe shagon askin Barber Yao shop a birnin Nairobi na Kenya
Rawar India

Asalin hoton, Kim Ludbrook / EPA

Bayanan hoto, Masu bikin nuna al'adun Hindu a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu suna rawar India a ranar Lahadi, 9 ga watan Maris na bana
Durban

Asalin hoton, Rajesh Jantilal / AFP

Bayanan hoto, Nan kuma birnin Durban ne a dai ƙasar ta Afirka ta Kudu, inda wata yarinya take wasa da kaloli duk dai a cikin bikin nuna al'adun na India wanda aka yi a ranar Alhamis 13 ga Maris
Barkwanci

Asalin hoton, Seyllou / AFP

Bayanan hoto, Ɗan wasan barkwanci na Senegal yana wasan kwaikwayo daga littafin L'Aventure Ambiguë - game da wani yaro da ya bar asalinsa - wanda Cheikh Hamidou Kane ya rubuta a birnin Dakar.
Bisau

Asalin hoton, Samba Balde / AFP

Bayanan hoto, Ƴan ƙungiyar Netos de Bandim ta ƙasar Guinea-Bissau suna wucewa a taron nuna al'adu a ranar Juma'a 7 ga watan Maris wanda aka yi a birnin Bisau