Faretin sojojin Kenya, da masu tseren mota cikin hotunan Afirka

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

Sojojin Kenya

Asalin hoton, Gerald Anderson / Getty Images

Bayanan hoto, A babban birnin Nairobi na Kenya, sojoojin ƙasar sun yi faretin girmamawa a ranar Talata domin tarbar Sarkin Netherlands, Willem-Alexander, wanda ya zo ziyarar aiki ta kwana uku
Buɗa-baki

Asalin hoton, Ahmed Mosaad / Getty Images

Bayanan hoto, Matasa a birnin Cairo na Masar suna shagalin buɗa-baki a ranar Asabar da ta gabata
Wasa da mota

Asalin hoton, Abdullah Doma / AFP

Bayanan hoto, Masu tseren mota a birnin Benghazi da ke gabashin Libya suna baje-kolin fasaharsu
Yara ƴan Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Christian Velcich / AFP

Bayanan hoto, Yara ƴan Afirka ta Kudu suna atisayen dambe a lokacin da ake gasar wasanni ta Johannesburg Interclub Development a garin Hillbrow
Tseren keke

Asalin hoton, Kim Ludbrook / EPA

Bayanan hoto, A ranar Alhamis da ta gabata ce aka fara gasar tseren keke ta Cape Winelands a ƙasar Afirka ta Kudu
Ƙura ta rufe mota

Asalin hoton, Massimo Bettiol / Getty Images

Bayanan hoto, Ƙura ta turnuƙe a lokacin da wata mota take gudu a gasar tseren motoci ta duniya da ake yi birnin Naivasha da ke arewa maso yammacin Kenya
Bikin Hindu

Asalin hoton, Gerald Anderson / Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Nairobi na Kenya, an gudanar da bikin Hindu wanda ake kira da bikin launuka a ranar Lahadin makon jiya.
Bikin kwalliya

Asalin hoton, Mohamed Messara / EPA

Bayanan hoto, Mahaifiya da ƴarta a wajen baje-kolin kayan ƙawa da aka yi a daƙin adana kayan tarihi na Bardo da ke birnin Tunis a ƙasar Tunisia.
Waɗanda ake zargi da ɓatar Joshlin Smith

Asalin hoton, Jaco Marais / Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin ce rana ta 11 da aka cigaba da sauraron shari'ar Joshlin Smith a Afirka ta Kudu. Nan waɗanda ake zargin ne suke zaune. Shari'a ce da ta ɗauki hankalin ƴan ƙasar tun bayan da yaron ɗan shekara shida ya ɓace
Gobarar Abuja

Asalin hoton, Afolabi Sotunde / EPA

Bayanan hoto, Wata mota da ta ƙone ƙurmus ke nan bayan wata babbar mota da ta fashe ta haifar da gobara a ranar Laraba a Abuja da ke Najeriya
Bikin kalankuwa a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Brenton Geach / Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka raƙashe a birnin Cape Town da ke Afirka ta Kudu a ranar Asabar da ta gabata
Kalankuwa

Asalin hoton, Esa Alexander / Reuters

Bayanan hoto, Wata ƴar rawa a kalankuwar birnin Cape Town ta ranar Asabar ɗin makon jiya
Sharon Chelimo

Asalin hoton, Quique Garcia / EPA

Bayanan hoto, Ƴar wasan tseren famfalaƙin Kenya, Sharon Chelimo tana zubar da hawayen farin ciki, bayan ta samu nasarar zama ta ɗaya a gasar tseren mata ta 2025 da aka yi a Barcelona a ranar Lahadin makon jiya