Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila
Isra'ila ta zargi Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, awanni bayan amincewa da yarjejeniyar wadda shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta.
Ministan tsaro na Isra'ila, Israel Katz ya ce dakarun Isra'ila za su "mayar da mummunan martani kan karya yarjejeniyar" ta hanyar kai "munanan hare-hare" kan Tehran.
Iran ta musanta cewa ta harba makamai masu linzami kan Isra'ila kuma dakarun ƙasar sun lashi takobin mayar da martani matuƙar Isra'ila ta ƙara kai musu hari.
Ga wasu abubuwa da muka sani kan yarjejeniyar ya zuwa yanzu.
Yaushe yarjejeniyar ta fara aiki?
Kimanin ƙarfe 5 na asubahin ranar Talata (agogon GMT) ne shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da sanarwar cewa yarjejeniyar ta fara aiki.
"Don Allah kada a karya ta" kamar yadda ya buƙata daga ɓangarorin biyu a shafinsa na sada zumunta na Truth.
Kimanin ƙarfe shida kuma na safiya (agogon GMT) Isra'ila ta tabbatar da cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar, bayan Iran ta nuna aniyar daina kai farmaki idan ita ma Isra'ila ta daina.
Sai dai sa'o'i bayan haka ne Isra'ila ta zargi Iran da ƙaddamar da hare-hare a cikin ƙasarta.
Tun farko Donald Trump ya ce "(sun) amince baki ɗaya" a wani bayani da ya wallafa jim kaɗan bayan ƙarfe 10 na dare a ranar Litini, wanda ya ce an kawo ƙarshen abin da ya kira "yaƙin kwana 12".
Hakan na zuwa ne bayan Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar a ranar Litinin, wani mataki da ta bayyana a matsayin ramuwar-gayya kan harin da Amurka ta kai a cibiyoyinta na nukiliya.
Ko yarjejeniyar ta wargaje?
Isra'ila ta zargi Iran da ƙaddamar da hari a cikin kasarta bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita wutar a ranar Talata.
Kafin fara aikin yarjejeniyar Iran da Isra'ila sun yi ta kai wa juna munanan hare-hare.
Rundunar Sojin Isra'ila (IDF) ta ce makamai masu linzami na Iran da dama ne suka fada cikinta a daren Talata. Masu aikin ceto sun ce hare-haren sun kashe mutum huɗu da rauna wasu mutum 22 a garin Beersheba.
A lokacin ne kafar talabijin ta gwamnatin Iran ta ce ƙasar ta harba "kashi na ƙarshe na makamai masu linzami" a kan Isra'ila.
A cikin daren na Talata kafar talabijin na gwamnatin Iran ya ruwaito cewa birnin Iran ya sha luguden wuta ta sama mafi muni tun bayan ɓarkewar yakin a ranar 13 ga watan Yuni, kuma mazauna birnin sun shaida wa sashen harshen Persia na BBC cewa sun ji ƙarar fashewa.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta lalata cibiyoyin harba makamai masu linzami a yammacin Iran, inda suka ce an riga an ɗana makaman domin harbawa zuwa cikin ƙasarta.
Iran ta ce an ƙara kashe wani masani kan nukiliya jim kadan kafin yarjejeniyar ta fara aiki. Babu tabbas kan adadin mutanen da aka kashe tun bayan ɓarkewar rikicin.
Kowa na yabon kansa?
Kafar yaɗa talabijin ta Iran IRINN ta sanar da cewa an tsagaita wuta tana mai cewa an tilasta wa Isra'ila bayan nasarar harin da Iran ta kai sansanin soji a Qatar.
A sanarwar da kafar ta karanta a ta ce Trump ne ya roƙi a tsagaita wuta bayan harin na Iran.
Sannan sanarwar ta yi jinjina ga dakarun juyin juya hali na Iran.
Ministan harakokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na X cewa Iran ta ci gaba da kai wa Isra'ila hari har zuwa karfe huɗu na safe.
Ya ce ƙarfe huɗu na safe ne wa'adin da aka ba Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare. A cewarsa "idan har Isra'ila ta yi haka, to ba mu da niyyar ci gaba da kai hare-hare.
Isra'ila har yanzu ba ta ce komi ba game da tsagaita wutar da Trump ya sanar, kuma ko bayan sanarwar Trump ta kai hare-hare ta sama cikin Iran.
Yadda Trump ya sanar da yarjejeniyar
Da safiyar Talata ne shugaban Amurka Donald Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran ta fara aiki.
Sai dai shugaban ya yi kira ga bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar
Donald Trump ya sanar da tsagaita buɗe wuta tsakanin Isra'ila da Iran a ranar Litinin da dare a shafinsa na sada zumunta.
Trump ya ce Iran za ta fara aiwatar da tsagaita wutar, daga baya kuma Isra'ila za ta dakatar da kai wa Iran hari.
Isra'ila dai ta ci gaba da kai hare-hare cikin Iran, kamar yadda ministan tsaronta ya bayyana, yayin da kuma Iran ta yi gargaɗi ga mazauna birnin Ramat Gan kusa da Tel Aviv su fice.
Shugaban na Amurka ya ce tsagaita wutar za ta fara aiki "nan da awa shida" tare da cewa nan da sa'a 24 "za a kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran.
Sai dai Isra'ila da Iran ba su tabbatar da cewa sun tsagaita wuta ba.
Babu tabbas ko rikicin tsakanin ɓangarorin biyu zai kawo ƙarshe, ko tsagaita wutar da Trump ya sanar za ta tabbata.
Shugaban Amurka ya kira sabon rikicin na Isra'ila da Iran da sunan "yaƙin kwana 12."
"Wannan yaƙi ne da za a iya shafe shekaru ana yi, wanda zai iya tarwatsa yankin gabas ta tsakiya, amma hakan ba ta faru ba, kuma ba za ta faru ba," kamar yadda Trump ya bayyana a shafinsa na sada zumunta.