Tarihin soyayyar Davido da amaryarsa Chioma

Asalin hoton, INSTAGRAM/DAVIDO ADELEKE
Duk da cewa a Talatar nan ne ake bukin fitaccen mawaƙin Najeriya David Adeleke, wanda mutane suka fi sani da Davido da budurusa Chioma, abin da mutane ba su sani ba shi ne dama tuni masoyan biyu sun yi aurensu shekara guda da ta gabata.
Amma Davido a hukumance ya sanar a wannan lokaci cewa bikin nasu zai kasance a ranar Talata 25 ga watan Yunin 2024. Fitar da hotunan aurensu a shafukan sada zumunta da Intanet ya ja hankali da tayar da ƙurar sambarka da ce-ce-ku-ce.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
A watan Maris na 2023, Davido ya sanar a lokacin zantawa da manema labarai kan sakin kudin wakarsa na Timelss cewa tuni ya auri Chioma.
Sun yi auren ne a lokacin da ya dakatar da wakoki domin makokin ɗansa na farko Ifeanyi, wanda ya rasu a Nuwamban 2022.
Wannan soyayya ta Davido da Chioma an jima ana yin ta, kuma tun lokacin da ta ke da cikin ɗansa na farko da ya rasu ya gabatar da niyyar aurenta inda aka yi musu baiko a Satumban 2019.
Sai dai abubuwa sun sauya lokacin da yaron ke shekara guda a duniya. Amma a 2022, Davido ya sanar da cewa sun soma shirye-shiryen gagarumin bikinsu da zai rikita kowa a ƙasar.
Amma wani abin mamaki sai aka karkare da auren sirri.
'Chioma ce mace ta farko da na yarda na bai wa amanar yarana'

Asalin hoton, INSTAGRAM/DAVIDO ADELEKE
Daga 2018, lokacin da Davido ya bayyana Chioma a matsayin budurwarsa da yake ƙauna a wakarsa ta Assurance, Davido bai taba wasa da damarsa ko ya yi wani abu na aibata ko sukar alakarsu ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wata tattaunawa da aka yi da shi a 2023, mawakin ya ce, ya san Chioma kusan shekaru 20 da suka wuce a shekarunsu na farko a jami'a.
Ya ce ta zama tamkar wani sashe na jikinsa kuma aurenta ne shawara mafi alheri da ya taba yankewa a rayuwarsa.
A cewar Davido, tun 2013 suke tare. Sai dai ba kowa ya san alaƙarsu ba har sai a watan Afrilun 2018, lokacin da Davido ya sanar da labarin a shafukan sada zumunta lokacin da ya saya mata motar alfarma a lokacin murnar zagayowar ranar haihuwarta, sannan ya fada wa duniya cewa ita ce tabbas a gare shi a wakarsa ta, Assurance.
Bayan wata ɗaya da wannan sanarwar, Chioma wadda sunanta na asali, Chioma Avril Rowland, ta je shafinta ta goge duk wani abu nasu da yarjejeniyar wani aikin girkin da ya samo mata.
A Yanzu haka shafinta na YouTube, The Chef Chi Show na da mabiya sama da 21,000 da kuma hotunan bidiyo 24.
A watan Agustan 2019, Davido ya sanar da cewa sun yi tafiya a karon farko tare zuwa Cotonou.
A Satumba, 2019, Davido ya sanar da cewa sun yi baiko tun kafin batun shirin aurensa a wannan watan.
Sun haifi ɗansu na farko da Chioma, na uku kuma ga Davido.
Masoyan sun rinka haifar da muhawara a shekarar farko bayan samun ɗansu, ita kuma Chioma ta kaddamar da nata sana'ar ciki har da shirin gabatar da girke-girken abinci.
Sannan ta haska a hotunan bidiyo da dama na mawaki Davido, kamar a Disamban 2018, a wakar Wonder Woman da kuma a watan Maris lokacin da aka haska ta a wakar 1 Milli.
Davido ya yi amfani da damar wajen nuna irin soyayyar da yake yi wa matarsa, inda akwai baitin da yake ambatar "Chioma ita kadai ce macen da zan iya bar wa yarana, kuma na samu kwanciyar hankali."
Sai dai sun tsinci kansu cikin wani tasku a Nuwamban 2022, sakamakon mutuwar ɗansu Ifeanyi ƙasa da wata ɗaya bayan shagalin cikarsa shekara uku a duniya, inda yaron ya nutse a cikin ruwa.
Tun daga wannan lokaci aka daina jin ɗuriyar Davido da masoyiyarsa na tsawon lokaci, akwai ma lokacin da ya ce ya daina wallafa rayuwarsa a shafukan sada zumunta.
A wannan lokacin, Chioma ita ma ta daina wallafa komai a shafinta.
A Disamba 2022, masoyan biyu sun je wani taro a karon farko bayan abin da ya faru a Qatar inda David ya yi waka a lokacin buɗe gasar cin kofin duniya.
Sannan a Oktoban 2023, kusan shekara ɗaya bayan mutuwar ɗansu na farko, mawakin ya sanar da cewa Allah ya ba su ƴan tagwaye, Chioma ta haihu a Amurka.
Wane ne Davido?

Asalin hoton, Getty Images
Mawaƙi ne ɗan Najeriya, kuma tun shekara ta 2010 yake wakoki.
An haife shi a ranar 21 ga watan Nuwamban 1992, mawakin da aka haifa a Amurka yana cikin fitattu da suka shahara a ciki da wajen kasar.
A shekara ta 2020 mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe kambin mawakin Afrobeats. An bayyana shi a matsayin mawakin Afirka mafi shahara.
Tun da ya yi fice a duniya, Davido ya lashe kyautuka da dama, ciki har da kyautar BET da MTV. Ya kuma yi waka da fitattun mawaƙa da dama.
A 2008, ya shiga cikin jeren 'yan Afirka 30 'yan kasa da shekaru 30 da ke kan ganiyarsu wanda mujallar Forbes ke wallafawa.
A 2024, Davido ya lashe kyautar Grammy ta farko na kundin wakokinsa Timelss. Ya kuma lashe mawakin Afirka da ya fi taka rawar gani, da kyautar mawakan duniya ta Global Music Album da kuma Global Music Performance
Ya yi wakoki da mawakan Amurka irin su Chris Brown da Nicki Minaj da sauransu.
Wace ce Chioma?

Asalin hoton, INSTAGRAM/DAVIDO ADELEKE
Chioma Avril Rowland, da mutane suka sani kuma suke kira Chef Chi ta yi fice ne sakamakon soyayyarsu da Davido.
Davido ya nuna ta a idon duniya a Satumban 2019.
Duk da dai ya bayar da labarin cewa a farkon shekarar suka soma soyayya bayan ya je wani taro na ƴan'uwa.
Amma a wannan lokaci, abin da ya fi bayar da mamaki shi ne lokacin da Davido ya ba ta kyautar motar alfarma Porshe a bikin zagoyarwar ranar haihuwarta, inda ta cika shekara 23. Wannan kyauta ta rikita mutane a shafukan intanet.
A wannan ranar kuma, Ya fitar da wakar Assurance wadda baitukan da kalmomi suka kasance kan budurwarsa Chioma, kuma ya haska ta a bidiyon.
Wakar ta ja hankali sosai, inda a ranar farko sama da mutum miliyan daya suka kalli waƙar.
Soyayyar Chioma da Davido ta bambanta da ta sauran matan da suka haifa masa yara.
Shafin Chioma na Instagram na nuna cewa ita gwanar girki ce kuma tana harkar kayan kawa.










