Chelsea ta yi nasara a kan Brighton da 'yan wasa 10

Chelsea ta yi nasara a kan Brighton a Stamford Bridge da ci 3-2 a karawar mako na 14 ranar Lahadi a Premier League.

Enzo Fernandez ne ya ci biyu a wasan da ta kai Chelsea ta hada maki ukun da take bukata.

Dan wasan tawagar Argentina ya fara cin kwallo a minti na 17, sannan Levi Colwill ya kara na biyu, kwallon farkon da ya zura a raga tun komawarsa Chelsea.

Brighton ta zare daya ta hannun Facundo Buonanotte daga baya aka bai wa dan wasan Chelsea, Conor Gallagher jan kati.

Daga nan Fernandez ya kara na uku a bugun fenariti gabanin tafiya hutun rabin lokacin.

Brighton ta zare daya ta hannun Joao Pedro daf da lokaci zai cika na minti 90.

An bai wa Brighton fenariti a cikin karin minti 10 a tashi daga karawar, sakamakon da Colwill ya taba kwallo da hannu.

Daga baya VAR ta soke hukuncin bayan da ta fayyace cewar kwallon ta bugi kan dan wasan ne ba hannunsa ba.

Wannan shi ne wasa na biyu da Chelsea ta yi nasara a Stamford Bridge a Premier League a kakar nan.

Ita kuwa Brighton ta ci wasa daya daga takwas da ta buga a lig a kwanan nan.