Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rwanda ta harbo jirgin saman yaki na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo
Gwamnatin Rwanda ta ce "ta dauki matakin kariya" a kan jirgin saman yaki na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo wanda ya shigo sararrin samaniyarta babu izini.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wani jirgin yaki da aka harbo lokaci ya sauko kasa-kasa a tsakanin garuruwan Goma na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Gisenyi na Rwanda.
Wasu hotunan sun nuna jirgin saman - kirar tarrayar sobiyet mai suna Sukhoi-25 ana zuba masa ruwa domin kashe wutar da ke ci a kusa da filin jirgin sama na Goma.
A wata sanarwa, ma'aikatar yada labarai ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta yi Allawadai da lamarin sannan ta musanta cewa jirgin yakin ya shiga sararin samaniyar kasar Rwanda.
A cewarta, gwamnatin kasar "ba za ta bari lamarin ya wuce haka nan ba" kuma "tana da 'yancin kare kanta".
"Gwamnati na kallon harin na Rwanda a matsayin takalar fada da gangan kuma tamkar neman yaki ne".
Rwanda ta ce wannan ne karo na uku da jirgin yakin Congo ke shiga sararrin samaniyarta kuma ta bukaci makwabciyarta ta daina neman fada.
A watan Nuwamban bara, wani jirgin yaki na Congo ya sauka a filin jirgin sama na Gisenyi a Rwanda, inda hukumomin Congo din suka ce ya sauka ne bisa kuskure.
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta zargi Rwanda da goyon bayan 'yan tawayen M23, zargin da Rwandar ta sha musantawa.
Lamarin na baya-bayannan na kara janyo zaman dar-dar a tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna.