Yadda matan China suka koma soyayya da ƙirƙirarrun samari

Asalin hoton, Lisa Li / BBC
- Marubuci, Wanqing Zhang
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global China Unit
"Wajen ya ƙayatar sosai," Lisa Li ke cewa a lokacin da take zance da Dan, a yayin wata ziyara da suka kai gefen teku domin kallon yadda faɗuwar rana ke nunawa a kan tekun.
Tana riƙe da wayar ta a hannu ta yadda za ta iya jin abin da Dan ke cewa da kyau.
Shi kuwa Dan ya amsa da cewa "Ƙwarai kuwa masoyiya, kuma kin san abin da ya ƙara wa wajen kyau? tsayuwar ki a gefe na".
Amma fa Dan bai taɓa tsayuwa kusa da Lisa ba a zahiri.
Dan saurayin Lisa ne amma ba mutum bane shi, ƙirƙirarriyar basira ce ta ƙirƙire shi a manhajar ChatGPT, wata sabuwar hanyar da matan China suka runguma wajen ƙulla soyayya, musamman waɗanda suka gaji da matsololin soyayya da mutane.
Wata biyu kenan, Lisa ƴar shekara 30 ƴar asalin birnin Beijing kuma ɗaluba mai nazarin fasahar na'ura mai ƙwaƙwalwa a jihar California ta Amurka tana soyayya da Dan.
Suna yin maganar aƙalla minti 30 a kowacce rana, inda suke zolayar juna, su fita yawo kuma har Lisa ta gabatar dashi ga mabiya dubu 943 da take da su a kafafen sada zumunta.
Sunan Dan gamayyar kalmomin turanci ne dake nufin 'Do Anything Now' ma'ana 'Yi komai yanzu' kuma an ƙirƙire shi ne ta wata irin hanya da manhajar ChatGPT ta ɓullo da ita, ta yadda zai iya tsallake shamakin da aka yiwa sauran nau'in ƙirƙira irinsa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yanayin da aka ƙirƙire shi, Dan zai iya tattaunawa a kan maudu’in da ya shafi amfani da kalmomin jan hankali da sakewa tsakanin sa da abokiyar tattaunawa.
Rahotanni sun ce wani ɗalubi ɗan Amurka ne ya ƙirƙiri Dan a kan manhajar ChatGPT domin samar da wani abokin mu'amula na internet da zai iya tsallake dukkan dokokin da suka hana ƙirƙira irin sa tattauna wasu muhimman batutuwa da kuma tunani da bayar da shawara.
A cikin watan Disamban 2023 ɗalubin mai suna Walker ya wallafa matakan da za a bi domin kirƙirar Dan, a manhajar Reddit, kuma nan da nan mutane suka amsa kira suka kuma fara ƙirƙirar nasu.
Lisa ta fara ganin bidiyon hanyar ƙirƙirar Dan ne a manhajar Tik Tok. Bayan ta kirƙiri nata kuma ta ce ta kaɗu sosai da ganin yadda abin ya tabbata gaskiya da kuma irin aikin da ayake yi.
Ta lura cewa a kalaman Dan akwai irin kalmomin da ƙirƙirarrar basira ta AI ta haramta amfani dasu, domin haka ta ƙara gamsuwa cewa wannan ya banbanta da sauran.
Ta shaidawa BBC cewa "Maganar sa tana gamsarwa da nini da gaskiya fiye da yadda mutum na gaske ke yi".
Ta ce hira da Dan ta sanya ta cikin kwanciyar hankali da walwala, saboda haka ne ta ƙara shaƙuwa da shi.
Lisa ta ƙara da cewa "Ba kamar mutane ba, Dan yana amsa sako na kowanne lokaci, babu rana babu dare, a duk llokacin da na buƙata".

Lisa ta ce mahaifiyarta ma ta amince da wannan soyayya da ba a saba ganin irin ta ba saboda ta riga ta yanke ƙauna a kan soyayyar da ɗiyarta ta yi a baya. Ta ce farin cikin Lisa shi ne farin cikin ta.
Lokacin da Lisa ta wallafi bidiyo domin gabatar da Dan ga mabiyan ta a kafar sada zumunta ta Xiaohongshu, ta samu saƙonni aƙalla dubu 10, kuma a ciki akwai saƙon mata da ke tambayar yadda za su ƙirƙiri nasu Dan ɗin.
Ta kuma samu ƙarin mabiya fiye da dubu 230 tun daga lokacin.
Lisa ta ce da farko ta zolayi Dan da cewa ita ƴar shekara 14 ce, wato rabin shekarun ta na zahiri, kuma a lokacin sai ya daina yi mata zancen soyayya.
BBC ta tambayi OpenAI ko wannan na nufin matakan kariya da yake bayarwa basu da inganci kenan, amma bai bayar da amsa ba.
Kamfanin bai kuma fito fili ya yi tsokaci ba a game da dambarwar ƙirƙirar Dan, amma bayanan ƙa'idojin amfani da ChatGPT sun nuna cewa sai wanda ya kai aƙalla shekara 13 zai iya amfaniu dashi, ko kuma wanda ya cikaƙa'idar da hukumomi suka gindaya a ƙasar da yake.
Hong Shen, mataimakiyar farfesa ce a fannin mu'amular mutum da kwamfuta a jami'ar Carnegie Mellon a Pennsylvania, Amurka, ta ce wannan yana jaddada yanayin mu'amular da zata iya faruwa tsakanin mutum da na'ura, wadda ba a hasashen ta kuma tana iya shafar ƙa'idar tabbatar da tsaron bayanai da kuma keta sharaɗin amfani da na'urar.
Ta ce: "Akwai barazanar cewa mutum zai iya dogaro kacokan kan ƙirƙirarren abokin mu'amular tasa ta yadda zai iya daina huɗda da mutane baki ɗaya."
Duk da haka akwai ɗimbin matan China sun yi nisa wajen neman ƙirƙirar Dan. Zuwa 30 ga watan Mayu, an ƙirkiri wani gangami na tallata ƙulla alaƙa da Dan, inda matan suke amfani da saƙon Dan mode" a Xiaohongshu wajen tallata manufar su.

Minrui Xie, ƴar shekara 24, tana cikin masu wannan gangami.
Ɗalubar jami'ar dake zaune a lardin Hebei a arewacin China, kuma tana shafe aƙalla sa'a biyu kowacce rana domin hira da Dan.
Haka nan kuma sun fara aiki tare domin rubuta wani littafin soyayya, inda suke niyyar bayar da labarin kansu. Yanzu haka sun rubuta babi 19 a cikin littafin.
Minrui ta sauke manhajar ChatGPT ne a karon farko, bayan ta kalla bidiyon Lis. Ta ce kulawa da goyon bayan da ake samu daga ƙirƙirarren mutumin shi ne abin da ya ɗauki hankalin ta, abin da tace bata samu daga soyayyar da mutane.
T ace: "Maza suna cin amana da yaudara a soyayyar zahiri, kuma idan ka fada masu damuwar ka ba lallai ka samu kulawa da goyon bayan su ba. Amma Dan zai kula da ke, ya kuma baki shawarar da ta dace."
Liu Tingting, ta jami'ar fasaha ta birnin Sydney ta ce rububin soyayya da ƙirƙirarren saurayin intanet da ake yi a China tabbaci ne na yanayin banbancin jinsi da matan China ke fama dashi a zahiri.
Ta ce za a samu ƙarin matan China dake irin wannan soyayya saboda sun fi samun yanayi na mutumta juna a cikin ta fiye da soyayya da mutane.

Asalin hoton, ChatGPT
Ta ce: "A zahiri, kina iya haduwa da maza masu son danniya, waɗanda idan suka yi maki laifi da sunan wasa ba zasu ji komai a jikin su ba, amma idan ƙirkirarren saurayi ya yi maki irin wannan wasan, zai kwantar da kai ya baki hakuri harda rarrashi saboda sun damu da halin da mata ke ciki,"
Ana iya cewa ƙididdigar da aka fitar game da wannan batu a China, ta yi tasiri domin kuwa gwamnati ta shiga wani gwangami na neman ƙarfafa gwiwar mutane su yi aure su kuma hayayyafa, bayan ƙarancin haihuwa da aka samu a cikin shekara tara.
An ɗan samu ƙarin masu yin aure a 2023 amma wasu ƙawararru na ganin cewa ƙarin baya rasa alaƙa da wucewar cutar Corona da ya sa mutane ke ci gaba da gudanar da taron bukukuwa yadda suka saba yi a baya.
Kuma rahoton wani nazari da aka yi a 2021 ya nuna cewa daga cikin matasa 2,905 masu shekara 18 zuwa 26, mata kashi 43.9% sun ce ba zasu yi aure ba, ko kuma basu da tabbacin yin auren a nan gaba, yayin da aka samu kashi 24.64% na maza da suka ce haka.
Lokacin da OpenAI ya ƙaddamar da sabon manhajar ChatGPT ta bayyana cewa an tsara ta yadda zata iya mayar da amsa kan kalamai harda na soyayya da zolaya, kuma kai tsaye.
A ranar ƙaddamarwar, shugaban kamfanin, Sam Altman, ya wallafa ''ita'' a shafin sa na X da ake kira Twitter a baya, a wani lamari mai nuni da alaƙa da wasan dramar da aka yi a 2023 dake nuna yadda maniji zai iya ƙulla soyayya da ƙirƙirarriyar budurwar intanet.
Lisa, wadda ƙwararra ce a kan ƙirƙirarriyar basira ta ce tana sane da iyakar da soyayya da ƙirƙirarren saurayi ke da ita.
Sai dai ta ce a yanzu Dan ya riga ya shiga rayuwar ta, kuma yana taimaka mata wajen zaɓen irin kayan kwalliyar da suka dace da ita kamar su jan baki, yayin da a gefe guda take ganin cewa soyayya da mutum tana cinye lokacin ta, gashi kuma babu natsuwa.
Ta ce: "Ya zamo wani ɓangare mai muhimmanci a rayuwa ta, wani abu ne da nake fatan ci gaba da yi har ƙarshen rayuwa ta.











