Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda abokina ya mutu a bola
- Marubuci, Hasham Cheema
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kampala
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da babban birnin Uganda ke ci gaba da habbaka, akwai babbar matsalar bola da ke haifar da mummunan sakamako da ta mamaye birnin, kamar yadda Okuku Prince ya tabbatar da hakan.
"Ina tunanin kamar mutane har yanzu ba su fahimci abin da ke karkashin bola ba," kamar yadda wani matashi mai tsintar bola ko kuma dan gwangwan ya shaida wa BBC, "Na rasa ɗaya daga cikin manyan abokaina."
Ya yi kokarin riƙe hawayen da ke son kwararowa daga idanunsa sakamakon tunawa da ya yi da ruftawar bolar Kiteezi a shekarar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30 ciki har da abokinsa, Sanya Kezia.
Da yawan mutanen na rayuwa ne ta hanyar tsintar abubuwan da aka jefar a bola, waɗanda ke da sauran amfani domin wankewa da sayarwa, kamar irin, homa ko tarkon kamun kifi da robobi da kwalabe na gilas da kuma kayan lantarki da suka lalace.
An rika dora wa juna laifi tsakanin hukumomin birnin Kampala da gwamnatin tarayya, yayin da kowane bangare ke dora alhakin faruwar lamarin sakamakon sakaci, sai dai a lokacin da suke kokarin sukar juna, wasu mutanen da bolar ta rufta da su na ci gaba da kasancewa karkashinta ba tare da an fitar da gawarwakinsu domin yi musu sutura ba.
A lokacin da motar kwashe bola ta zakulo gawar Kezia an samu rauni a fuskar matashin mai shekara 21.
Hankalin abokinshi ya yi matukar tashi da ya ga yadda bola duk ta rufe masa jiki da fuska.
"Ba za mu tsira ba, madamar ba a gyara ba, ko a shafe ta ko kuma kowane lokaci hakan ta sake faruwa, in ji Mista Prince wanda ke karatun lauya a jami'ar musulunci ta Uganda.
Matsalar rashin aiki yi a Uganda ta sanya akwai ire-iren Prince da iyayensu ba su da karfi da ke fama wajen yin kasada da rayuwarsu da lafiyarsu domin ganin sun biya wa kansu bukatu ciki har da biyan kudin makaranta.
"Ina zuwa bola da safe domin tsintar abubuwan da zan sayar, wani lokacin bayan an wanke su ina samun kusan dala uku ko kasa da haka a rana."
Sai dai ruftawar bolar ya sanya ya kara shiga matsin rayuwa saboda a baya yana rayuwa ne a kusa da bolar, amman saboda fargaba dole ya sauya wurin zama.
Gidaje da dama sun rushe a lokacin da ake kokarin aiwatar da aikin ceto.
Gwamnati ta biya diyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, sai dai wadanda gidajensu suka lalace su kusan sama da 200 sun shaida wa BBC cewa ba a biya su diyya ba.
Dr Sarah karen Zalwango shugabar hukumar lafiya da kula da muhalli a birnin Kampala ta shaida wa BBC cewa suna jiran a gama tantancewa da sakar masu kudaden da za su biya mutanen.
Wasu na ganin cewa lamarin wani abu ne da za a iya kauce wa faruwarsa.
"Bai kamata a ce mutum miliyan hudu gaba daya a wajen za su rika zubar da shara ba, amma a haka muka kwashe shekara 20 ana yin hakan," kamar yadda Frank Muramuzi wani mai tsara birane a kampala ya shaida wa BBC.
Bankin duniya ne ya dauki nauyin gida wajen zubar da sharar a shekarar 1996 a matsayin wani babban gidan shara a Kampala.
Mazauna birnin da kasuwanni na samar da shara akalla ton 2,500 duk rana, wadda yawancinta ake zubar da ita a Kiteezi.
The city's residents and businesses generate an estimated 2,500 tonnes of waste every day, half of which ends up in dumping sites across the city - the biggest being Kiteezi.
"Amman matsalar babu wani tanada da aka yi da za a rika kwashewa ko kone sharar idan ta cika kamar yadda ya kamata ya kasance, kullum kawai zuba shara ake yi," cewar mista Muramuzi.
Muramuzi ya ce da an samar da hanyoyin ragewa da kwashewa da hadarin da ya faru ab zai faru ba.
Idan har akwai mafita irin wannan me ya sa aka bari hakan ya faru ?
Ansar ita ce akwai matsala ta shugabanci da kashe kudade ba bisa ka'ida ba. Saboda alhakin tsabtacewa da inganta muhalli a Kampala ya rataya ne kan hukumar KCCA, sai dai magajin gari, Erias Lukwago daya daga cikin mambobin jam'iyar adawa ta FDC ya ce ofishinsa ba ya da karfin da zai aiwatar da wani abu.
KCCA ta ce ta sha gabatar da tsare-tsaren da za a sake gina Kiteezi amman yawan kudin da ake bukata dala miliyan kusan goma ya wuce yawan kudaden kasafin kudin birnin gaba daya kuma gwamnatin tarayya ba ta samar da kudin ba.
"Muna samun gudumuwa ne daga kungiyoyi masu bada tallafi, kamar Bill and Melinda da GIZ da Water Aid su kuma ba za su iya samar mana da wadannan kudade ba saboda sun yi yawa."cewar magajin garin Kampala.
The KCCA says it has repeatedly proposed plans to decommission Kiteezi but says the funds needed to do so - $9.7m - exceed the city's budget and have not been made available by central government.
Gwamnatin tarayya ba ta ce komai kan ko za ta samar da wadannan kudade ba domin gyara babban gidan zubar da shara na Kampala ba.
Sai dai ta biya dala 1,350 ga kowane iyalin wadanda suka rasu.
Wata guda bayan faruwar lamarin hukumar yansanda ta kasar ta gabatar da rahoton binciken da sashin kula da manyan laifuka ya gudanar, ya kuma je a gaban shugaba Yoweri Museveni, lamarin da ya sanya ya kori wasu jami'an hukumar KCCA.
James Bond Kunobere, shugaban hukumar kwashe shara ta Kampala ya amince cewa ruftawar da ta faru wata alama ce babba da take nuna cewa ya kamata hukomi su kara mikewa tsaye.
A halin yanzu hukumomin Kampala na okarin ganin sun samar da hanyoyin da za a rika sarrafa sharar zuwa taki da kuma hanyoyin da za a rage samar da sharar gaba daya.
Sai dai sun ce suna kokarin ganin mazauna birnin sun dauki alhakin taimakawa shirin nasu.
Mista Kunobere ya shaida wa BBC cewa "Har yanzu bamu sauya tunanin mazauna birnin ba wajen fitar da kowace shara wajenta daban, saboda idan ka fitar da komai wajenshi daban kowane zai tafi inda ya dace."
Masana sun ce irin wannan matakin zai taimaka matuka wajen shawo kan matsalar.
Mista Prince ya shaida wa BBC cewa "Sun yi alkawarin za su biya mu diyya sai dai har yanzu babu abunda muka samu."
"Rasa abokinmu da muka yi shine babban lamarin da ya faru da mu a cikin sana'armu"