Yaran da suka koma gida bayan shekara 13 da bacewa

Asalin hoton, Naresh Paras
- Marubuci, Geeta Pandey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
A wata tsakar rana da bazara cikin watan Yunin 2010, wasu yara biyu suka fice daga gidansu a guje bayan da iyayensu suka dake su kan wani laifi da suka aikata.
Yaran biyu - Rakki mai shekara 11 da kaninta Bablu mai shekara bakwai - sun yanke shawarar tafiya gidan kakanninsu wadanda ke wata unguwa kusa da gidan nasu, to amma sai yaran suka bace a kan hanyarsu.
Lamarin da ya sa suka kwashe shekara 13 kafin su koma gida, ta hanyar taimakon kungiyoyin kare hakkin yara da mahaifiyarsu Neetu Kumari.
"Nakan ji kewar mahaifiyata a kowace rana," in ji Bablu wanda ya ya taso a gidan marayu. "A yanzu ina cikin murna na dawo gida cikin dangina."
Wani bidiyon da ya nuna lokacin da yaran suka sake haduwa da danginsu a watan Disamba ya nuna yadda Neetu ta tarbi 'ya'yanta tare da rungumar su da godiya ga Allah, ''na gode Allah da ya ba ni dama sake haduwa da 'ya'yana''.
Sannan Bablu ya rungumi Rakhi, wadda ta riga shi komawa gida da kwana biyu. Duk da cewa yaran na jin labarin juna a shekaraun baya, sun sake haduwa bayan sama da shekara 10.
Rabuwar
Bablu da Rakhi na zaune a arewacin birnin Agra tare da iyayensu Neetu Kumari da Santosh, wadanda ke aikin leburanci.
A ranar 16 ga watan Yunin 2010, Neetu, wadda ba ta samu aikin leburanci ba a ranar, ta huce fushinta kan 'yar tata Rakhi inda ta doke ta da itacen da take amfani da shi wajen girki.
Daga nan sai Rakhi da kaninta Bablu suka fice daga gidan bayan da mahaifiyar tasu ke ta fada.
"Mahaifina ma kan doke ni a wasu lokuta, idan ban yi karatu yadda yake so ba, don haka a lokacin da Rakhi ta ce min mu tafi wajen kakarmu mu zauna a can, sai kawai na yarda,'' in ji Bablu.
Bayan da suke bace, sai wani direba ya taimake su ya kai su tashar jirgin kasa.

Asalin hoton, Naresh Paras
A nan ne, yaran suka hau jirgin kasa, inda aka gan su tare da wata mata da ke aiki da gidauniyar tallafa wa kananan yara.
A lokacin da jirgin ya isa Meerut, birni mai nisan kilomita kusan 250 daga gidansu, sai matar ta damka su a hannun 'yansanda wadanda suka kai su wani gidan marayu na gwamnati.
"Mun gaya musu cewa muna son komawa gida, mun yi kokarin ba su labarin iyayenmu, to amma 'yansandan ko jami'an gidan marayun ba su nemi danginmu ba,'' in ji Bablu.
Shekara gudan bayan haka ne aka raba yaran da juna - Aka mayar da Rakhi wajen da yara mata ke zaune karkashin ikon wata kungiya mai zaman kanta da ke kusa da Delhi babban birnin kasar Indiya.
Shekaru bayan haka, aka sake mayar da Bablu zuwa wani gidan marayun shi ma na gwamnati a Lucknow, babban birnin jihar Uttar Pradesh.
Yaran sun sake haduwa da juna
A duk lokacin da wani babban jami'i, ko ma'aikatan jin kai, ko 'yanjarida suka ziyarci gidajen marayun, Bablu na gaya musu labarin 'yar’uwarsa Rakhi tare da fatan wata rana za su sake haduwa.
Amma a shekarar 2017, muradinsa ya cika, inda daya daga cikin masu kula da gidan ya kuduri aniyar taimaka masa a lokacin da ya gaya mata cewa akwai 'yar’uwarsa da aka kai gidan marayun da ake ajiya 'yanmata a wani wuri a kusa da birnin Delhi.
"Daga nan ta kira jami'an da ke kula da gidajen marayu na Noida da Greata Noida da ke kusa da Delhi, inda ta tambaye su ko akwai wata yarinya mai suna Rakhi, bayan kokarin da ta yi, sai ta gano min ita,'' in ji Bablu.
Daga nan ne yaran suka rika magana da juna ta wayoyin jami'an da ke kula da gidajen marayun.
"Ina kira ga gwamnati bai kamata a raba 'yan’uwan da ke zaune a gidajen marayu ba. Ya kamata a ajiye su waje guda. Bai dace a raba su ba,'' in ji shi.

Asalin hoton, Naresh Paras
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A lokacin da 'yan’uwan suka hadu, ko suka yi magana ta waya, zancensu ba ya wuce yadda za su gano iyayensu, to sai dai Rakhi ta fara yanke kauna.
"Shekara 13 fa ba wasa ba ne, don haka ba na tunanin za mu sake haduwa da iyayenmu," abin da take fada min ke nan a duk lokacin da muka yi magana.
To amma shi Bablu bai yanke kauna ba. "Na yi matukar farin cikin samun Rakhi kuma ina cike da fatan cewa wata rana za mu gano iyayenmu,'' in ji shi.
A daya daga wuraren da ya zauna, Bablu ya ce masu kula da gidajen da kuma yaran da suka girme shi sukan doke shi. Ya ce sau biyu yana yunkurin guduwa, to amma sai yake fargabar watakila a sake kamo shi.
A nata bangare, Rakhi, ta ce a inda ta tashi ta samu kulawa daga kungiyar da ke kula da su. Na tambaye ta ko akwai bambancin kulawa tsakanin inda take da kuma gida.
"Na yi imanin cewa duk abin da ya faru mukaddari ne, kuma watakila hakan ya faru ne don na samu ingantacciyar rayuwa a waje,'' kamar yadda take fada min.
"Ni ba 'yarsu ba ce amma suna kula da ni yadda ya kamata. Babu wanda ya taba duka na a cikinsu, suna kula da ni yadda ya dace, ina zuwa makaranta mai kyau, da ingantaccen asibiti da sauran abubuwan more rayuwa," in ji ta.
Dan gwagwarmayar da ya sake hada iyalan
A ranar 20 ga watan Dismba, Bablu ya kira Naresh Paras wani dan gwagwarmayar kare hakkin yara dan Agra da a yanzu ke zaune a Bengaluru inda yake aiki.
"Ka sada iyalai da dama da danginsu, don Allah ko za ka taimaka mana mu ma ka samo mana danginmu?" Bablu ya roke shi.
Mista Paras, wanda ke aiki da kananan yara tun 2007, ya ce wannan ba aiki ne mai sauki ba.
Yaran sun manta sunan mahaifinsu, don haka sunan da aka yi musu rajista a gidan kula da marayun ba na mahaifinsu ba ne. Ba su san sunan jiha balle gundumarsu ba.
Abin da aka rubuta musu agidajen marayun shi ne sun zo daga Bilaspur wani birni a jihar Chattisgarh da ke tsakiyar Indiya. Don haka kiran da mista Paras ya yi wa 'yansandan Bilaspur bai samu wani bayani ba.

Asalin hoton, Naresh Paras
Burin yaran ya fara tabbata ne a lokacin da Bablu ya tuna cewa ya taba ganin wani jirgin kasa na wasa a wajen tashar jirgin da suka hau.
"Ai kuwa na san cewa a tashar jirgi ta Agra ce," in ji Mista Paras.
Bayan duba bayanan 'yansandan birnin, sai ya gano ofishin 'yansandan da mahaifin yaran ya kai rahoton bacewarsu a watan Yunin 2010.
Amma alokacin da ya je gidan su, sai ya gano cewa gidan da suke zaune a lokacin na haya ne kuma yanzu sun tashi.
Daga nan ne Rakhi ta fada masa cewa ta tuna sunan mahaifiyarsu Neetu kuma tana da tabon kuna a wuyanta.
Lamarin da ya sa mista Paras ya je inda masu aikin leburanci ke taruwa a birnin Agra a kowace safiya cike da fatan samun aiki. Sai dai bai samu Neetu ba, amma wasu leburorin da ke wurin sun shaida masa cewa sun san ta, kuma za su fada mata sakonsa.
Da jin labarin an samu 'ya'yanta, sai Neetu Kumari ta nufi ofishin 'yansanda, inda aka tuntubi mista Paras.
Sake haduwa bayan shekara 13
A lokacin da Mista Paras ya ziyarci Neetu, ta nuna masa hotunan yaran tare da kwafin takardar korafin da suka kai wa 'yansanda.
A lokacin da ya hada ta da su ta kiran bidiyo, duka suna gane junansu.
Neetu Kumari ta gaya wa mista Paras cewa "ta yi da-na-sanin dukan Rakhi" da kuma irin kokarin da ta yi wajen neman yaran.

Asalin hoton, Naresh Paras
"Na karbi rancen kudi na je Patna (babban birnin jihar Bihar) bayan da aka ce min an gan su suna bara a kan titi a can. Na je wuraren bauta, da masallatai, da coci-coci, inda na rika biyan kudi ana min addu'a don su dawo gida'', in ji ta.
A lokacin da take rungume da 'ya'yanta cikin shauki da murna Neetu ta ce yanzu za ta sake sabuwar rayuwa.
Rakhi ta ce sai ta ji kamar a ''shirin fim" saboda ba ta taba tunanin sake ganin mahaifiyarta ba. "Na yi matukar farin ciki," in ji ta.











