Bambance-bambancen da ke tsakanin zaɓen Senegal da na Najeriya

    • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Yanzu dai ƙura ta lafa a fagen siyasar ƙasar Senegal bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 24 ga watan Maris.

Tuni hukumar kundin tsarin mulki ta ƙasar ta sanar da Bassirou Dimoaye Faye, matashi ɗan shekara 44, kuma ɗantakara na gamayyar jam’iyyun adawa a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Zan kawo muku uku daga cikin manyan bambance-bambancen da na gani tsakanin zaɓen Senegal na wannan shekarar da zaɓen shugaban Najeriya da aka gudanar a 2023.

Nasu ba irin namu ba ne

Zaɓen shugaban ƙasar Senegal ya gudana ne cikin kwanciyar hankali da lumana, ba a samu rahoton wata hatsaniya ko fasa akwati ko sayen ƙuri’a balle rasa rai ba.

Zan iya cewa a tsawon lokacin da na kwashe ina lura da yadda ake gudanar da zaɓe a ƙasata Najeriya zai yi wahala idan na taɓa ganin an yi zaɓe salin-alin kamar wannan.

Wannan na ɗaya daga cikin manyan bambance-bambancen da na gani a mako ɗaya da na kwashe a birnin Dakar domin ɗauko rahoto kan zaɓen shugaban ƙasar.

A Najeriya ga misali, a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, wani rahoto na Cibiyar bunƙasa demokuraɗiyya (CDD) mai taken ‘Nigeria’s 2023 Election Security Landscape’ ya bayyana yadda ƴan bangar siyasa suka riƙa tsangwama da cin zarafin masu kaɗa ƙuria a wurare daban-daban.

Alƙaluman rahoton sun nuna cewa an samu rikice-rikice a wurare 114 a faɗin Najeriya a ranar da aka gudanar da zaɓen.

Hakan ya haifar da asarar rayuka da jikkata mutane da dama yayin da jam’ian tsaro kuma suka kama wasu da dama.

Amma a zaɓen shugaban Senegal babu rahoto ko ɗaya na tashin hatsaniya a wani wuri a faɗin ƙasar balle a yi batun rasa rai ko kuma samu raunuka.

Samun tabbacin wanda ya yi nasara kafin hukuma ta sanar

Wani abu da ya so rikita masu bibiyar zaɓen daga ƙasashen waje, musamman ma waɗanda suka saba da zaɓuka irin na sauran ƙasashe kamar Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar Afirka, shi ne yadda aka samu tabbacin wanda ya lashe zaɓe kusan tun a cikin daren ranar da aka kammala kaɗa ƙuri’a.

Sa'o'i kaɗan bayan rufe rumfunan zaɓe ƴantakara kimanin 16 na jam’iyyun adawa suka kira Bassirou Faye suka taya shi murnar lashe zaɓen, sannan a yammacin ranar Litinin ɗantakarar jam’iyya mai mulki Amadou Ba da kuma shugaban ƙasar Macky Sall da kansa suka taya Bassirou Fayen murna.

Haka nan a ranar Talatar da daddare ne Bassirou Faye ya gabatar da jawabin amincewa da samun nasara tare da bayyana alƙiblar gwamnatinsa.

Duk waɗannan abubuwa sun faru ne kafin majalisar kundin tsarin mulkin ƙasar ta bayyana sakamako a hukumance.

Domin kuwa sai bayan kwana uku da yin zaɓe ne majalisar kundin tsarin mulkin ta bayyana ɗantakarar na adawa a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kimanin kashi 54 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Ta yaya al'ummar Senegal ke gane wanda ya yi nasara kafin hukuma ta sanar?

Wannan abu ne mai sauƙi a wurin da ake kamanta gaskiya, saboda a zahiri lokacin zaɓuka kowace jam’iyya na tura wakilanta zuwa dukkanin rumfunan zaɓe.

Kuma akan ƙirga ƙuri’a a kowace rumfa bayan rufe kaɗa ƙuri’a, saboda haka kowace jam’iyya na iya sanin yawan kuri’un da ta samu da kuma yawan na jam’iyyun hamayya daga wakilanta.

Kuma kasancewar yadda ake iya samun bayanai cikin sauri a wannan zamani, za mu iya fahimtar cewa abu ne mai sauƙi a tattara waɗannan alƙaluma cikin lokaci ƙalilan bayan kammala zaɓe.

Abin da ya faru ke nan a wannan zaɓe da ya gudana a Senegal.

Sai dai a zahiri hakan ba abu ne mai yiwuwa ba a wauraren da ba a kamanta gaskiya, ko wuraren da ake yin maguɗi ko kuma inda ake fasa akwatuna har ma a soke zaɓuka.

Idan muka kwatanta da zaɓen shugaban Najeriya na 2023, rahoton CDD ya nuna cewa kashi 25 cikin 100 na rikice-rikicen da aka samu lokacin zaɓen shugaban ƙasa ya ƙunshi lalatawa da farfasa akwatin zaɓe da tarwatsa rumfar zaɓe, kuma hakan ta faru a kimanin rumfunan zaɓe 2000, mafi yawanci a kudancin ƙasar.

Irin wannan lamari kan dagula al’amura ta yadda wakilan jam’iyyu ba za su iya tattara alƙaluma na ƙuri’un da aka kaɗa a kowace rumfar zaɓe ba, balle har jam’iyyu ko kuma ƙungiyoyi na masu sanya ido su iya tattara yawan ƙuri’un da aka kaɗa.

Hasali ma sau da yawa jam’iyyu kan yi zargi a wasu lokutan cewa wasu alƙaluma da ake gabatarwa a cibiyar tattara sakamakon zaɓe kan sha bamban da alƙaluman da aka samu a rumfunan zaɓe, saboda haka sukan yi zargin an sauya alƙaluman ne a kan hanyar isar da sakamakon zuwa babban ofishin tattara sakamako.

Idan har ana samun irin haka ta yaya za a san wanda ya lashe zaɓe kafin hukumar zaɓe ta bayyana?

Amma abin da na lura a zaɓen Senegal shi ne akwai yarda da juna da amana, kuma sun amince cewar ba za su yi wani abu da zai kawo tangarɗa ba, saboda haka nan babu wani da ya yi yunƙurin yin murɗiya ta hanyar hana yin zaɓe ko kuma sauya alƙaluman ƙuri’un da aka kaɗa.

Wannan ne ya sanya lissafin kusan dukkanin jam’iyyun da suka shiga zaɓen shugaban ƙasar ya zo ɗaya, kuma suka amince da sakamakon tun kafin a sanar a hukumance.

Waɗanda ba su yi nasara ba sun sani, kuma sun amince da shan kaye, sannan wanda ya yi nasara ya amince da nasararsa.

Yawan al'umma da girman ƙasa

Kasancewar Najeriya ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya yawan al'umma a duniya ya sanya abtun shiryawa da aiwatar da zaɓe ke zama mai matuƙar wahala.

Wani abun da ke ƙara sarƙaƙiya wajen shirya zaɓukan na Najeriya kuma shi ne zagon ƙasa da wasu ɓata-gari ke yi ta hanyar ƙulla hanyoyin yin maguɗi.

Yayin da Najeriya ke da yawan al'umma sama da miliyan 200, Senegal na da yawan al'umma ne kimanin miliyan 18, wanda hakan ke nuna cewa Najeriya ta lunka Senegal kimanin sau 10.

Haka nan yayin da Najeriya ke da girman ƙasa da ta kai murabba'in kilomita 923,768, ita kuwa Senegal na da girman murabba'in kilomita 196,722 kacal.

Yanayin girman ƙasar da Najeriya ke da shi kan janyo tsaiko wurin tattara sakamakon zaɓuka.

Hargitsin zaɓe a Senegal

Duk da cewa an gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Senegal na wannan shekara salin-alin, haka ba ya na nufin cewa dukkanin zaɓen da aka gudana a ƙasar tun bayan samun yancin kai a haka ya gudana ba.

Hasali ma ko gabanin zaɓen na wannan shekara an yi ta fargabar cewa za a iya samun tashin-tashina, ganin cewa shigaba Macky Sall ya yi yunkurin dage lokacin zaben, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a fadin kasar.

Sannan a shekara ta 1988 zaɓen shugaban ƙasar ya bar baya da ƙura bayan da matasa suka yi zargin shugaban ƙasar na wancan lokaci Abdou Diouf da yin maguɗi.

Sakamakon da ya fara fitowa bayan zaben na shekarar 1988 ya nuna cewa shugaba Abdou Diouf ne ya lashe zaɓen da kashi 80 cikin 100 na ƙuri’ar da aka kaɗa a larduna 21, inda yake gaban babban abokin hamayyarsa Abdoulaye Wade, sannan kuma an ƙi sakin kashi 50 cikin 100 na sakamkon zaɓe daga yankuna masu yawan masu kaɗa ƙuri’a irin su Dakar da Theis.

A wancan lokaci dubun-dubatar matasa ne suka suka bijire wa jam’ian tsaro, suka fita kana titunan birnin Dakar suna zanga-zanga, suka sanya shinge a kan tituna tare da jifar jami’an tsaro da duwatsu da kwalabe.

Sanadiyyar haka ne gwamnati ta kafa dokar ta-ɓaci, tare da haramta duk wata zanga-zanga, da rufe jami’o’i da makarantu har illa ma sa Allahu.

An kama mutane da dama sannan wasu da dama sun samu raunuku, adadin da ba a iya tantancewa ba.

Haka nan ma an taɓa samun wata hatsaniyar siyasar a shekara ta 1993.

Wane darasi ƙasashen Afirka za su koya daga zaɓen Senegal?

Ina ganin darasi na farko shi ne mu duba me ya sa zaɓen ya gudana cikin lumana? Kasancewar manyan abubuwan da ke yamutsa lamurran zaɓe a ƙasashen Afirka su ne tashe-tashen hankula da kuma maguɗi.

Jiki magayi

A lokacin da nake mamakin yadda zaɓen na shugaban Senegal ya tafi salin-alin na tambayi abokin aikina Hamet Fall na sashen BBC Afrique, wanda ofishinsu yake a Dakar cewa me ya sa zaɓen ya kasance haka? Sai ya ce min:

“Hargitsin siyasa da aka samu a baya wanda ya haifar da asarar dukiyar gwamnati da ta mutane masu zaman kansu ya tsorata al’ummar Senegal. Ba su shirya sake dagula zaman lafiyar da aka samu a yanzu ba sai dai idan akwai wani dalili mai ƙwari.”

Wannan na nufin cewa mutanen Senegal ne suka yi wa kansu faɗa, sun gane cewa babu alfanu a tayar da hargitsi wanda ke haifar da asarar dukiya da rayuka.

Kuma hakan na nufin cewa kowace al’umma idan ta ga dama za ta iya yi wa kanta fada domin samun sauyi nagari.

Martaba zaɓin al'umma

Yadda kowa ya yi na’am da sakamakon zaben ya nuna cewa sakamakon ya yi daidai da zabin al’umma.

Wannan ya taimaka wajen dakile duk wani yunkuri na tashin-tashina.

Idan aka yi la’akari da abin da ya faru a bayan zaben shugaban kasar na 1988, mutane sun yi bore ne saboda sun fahimci cewa sakamakon zaben bai yi daidai da zabin da suka yi ba.

A wannan karo babu wata alama da ta nuna cewa an yi kokarin murde zaben daga bangaren gwamnati duk kuwa da cewa akwai zazzafar adawa tsakanin shugaba Sall da kuma jam’iyyun adawa, abin da ya kai ga cewa an garkame jagoran adawa na kasar Ousman Sonko da shi dan takarar jam’iyyun hamayya kuma zababben shugaban kasa na yanzu Bassirou Diomaye Faye.