Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda miyagun mafarke-mafarke ke rage tsawon rai
- Marubuci, Timothée Hearn
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, The Conversation*
- Lokacin karatu: Minti 3
Farkawa bayan yin mugun mafarki zai sa zuciyarka ta riƙa bugawa cikin sauri, sai dai ba wannan ne kadai tasirin mugun mafraki ba.
Manya waɗanda suka balaga da ke yin miyagun mafarke-mafarke, sun fi shiga haɗarin mutuwa da wuri har sau uku kafin shekara 75, idan aka kwatanta da waɗanda ba sa yin irin waɗannan mafarke-mafarke.
Wannan bincike - wanda ba a gama gudanar da shi ba - ya fito ne daga masu bincike waɗanda suka tattara bayanai da bincike guda huɗu da aka gudanar a Amurka, a kan mutane sama da 4,000 waɗanda shekarunsu suka kama daga 26 zuwa 74.
A farko, waɗanda aka gudanar da binciken a kansu sun ruwaito yadda mugun mafarki ke katse musu barci a yawan lokuta. A tsawon shekara 18, masu binciken sun tattara bayanai kan mutanen da suka mutu da wuri - sun kai 227.
Duk da cewa sun bayyana cewa akwai abubuwa da ke barazana kan haka da suka haɗa da shekaru, da lalurar kwakwalwa, da shan taba da kuma ƙiba, sun gano cewa mutanen da suke yin mugun mafarki a kowane mako sun fi fuskantar barazanar mutuwa sama da nunƙi uku - wata barazana da ke da alaƙa da yawan shan taba.
Tawagar masu binciken ta kuma yi duba kan shekarun mutane ta hanyar amfani da ƙwayoyin halitta. Binciken ya gano cewa mutanen da ke yin muggan mafarke-mafarke daban-daban kan nuna alamun tsufa fiye da tsararrakinsu masu shekaru ɗaya.
Yadda abin ke faruwa
Mafarki na faruwa ne lokacin da mutum yake barci, lokacin ƙwaƙwalwa na cigaba da aiki, amma jijiyoyi na hutawa.
Lokacin da mutum yake kwance domin rage gajiya, wasu ƙwayoyi za su tashi don yin aiki.
Yawan gajiya na yin tasiri ga jiki. Yana sa jini ya hau, abin da kuma ke janyo lokacin tsufa da wuri ta hanyar cire abubuwan da ke garkuwa ga jiki.
Haka kuma, mugun mafarki na sa mutum ya farka nan take abin da ke katse barcinsa, wani lokaci kuma da jiki ke gyara kansa da kuma cire datti a cikin ƙwayoyin halitta.
Waɗannan abubuwa biyu - tarin gajiya da kuma rashin barci - mai yiwuwa suna cikin abubuwan da suka fi janyo mutuwa da wuri.
Batun cewa muggan mafarke-mafarke na da illa ga lafiya dai ba sabon abu ba ne.
Bincike da aka yi a baya - ya nuna cewa waɗanda suka balaga da ke yin mafarki a kowane mako sun fi hatsarin kamuwa da cutar mantuwa da sauran su, shekaru da dama kafin a fara ganin alamomin.
Ƙaruwar hujjoji sun nuna cewa cutar kwakwalwa na shafar ɓangaren kwakwalwa da ke yin mafarki. Don haka yawan yin mafarki zai iya zama alama ce ta matsalar kwakwalwa.
Mugun mafarki dai ba sabon abu ba ne. Kusan kashi 5 na mutanen da suka balaga sun ruwaito yin mugun mafarki aƙalla sau ɗaya cikin mako, sannan kashi 12.5 a wata ɗaya.
Saboda ba sabon abu ba ne kuma ana iya magance su, sabon binciken ya nuna cewa mugun mafarki wani ɓangare ne da zai iya shafar lafiyar al'umma.
Kafin a karkare kan wannan batu, akwai muhimmanci a duba wasu abubuwa.
Binciken ya dogara ne da rahoton mafarkin waɗanda aka yi bincike a kansu, abin da zai yi wuya a iya bambance tsakanin mugun mafarki da kuma na gaske.
Yawancin mutanen sun fito ne daga Amurka, don haka ba za a iya amfani da rahoton kan kowa ba.
Idan wasu binciken za su iya tabbatar da abin da aka gano a wannan bincike, to likitoci za su fara tambayar marasa lafiya kan mugun mafarki da suka yi yayin duba lafiyarsu - domin ganin ko jininsu bai hau ba.
Akwai abubuwan da za a iya yi wajen dakatar da yin mugun mafarki.
Yawan amfani da su, zai samar da wata babbar dama na ƙara tsawon rayuwa yayin da ake samun isasshen barci mai inganci.