Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace ce Latifa al-Droubi - Uwargidan shugaban riƙo na Siriya?
A watan Fabarairu ne Shugaban riƙo a Siriya, Ahmed al-Sharaa, ya je Turkiyya domin ganawa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan kuma a karon farko, ya kasance tare da mai ɗakinsa.
Duk da cewa uwargidan shugaban riƙon ba ta yi wani jawabi ba bayan ganawa da takwararta ta Turkiyya, an ga hoton da suka ɗauka tare ya karaɗe shafukan sada zumunta. Amma wace ce Latifa al-Droubi?
Sabuwar Siriya
Wata uku ne tun bayan da ƙungiyar HTS mai kishin musulunci ta ƙwace iko da birnin Damascus, lamarin da ya tilasta wa Bashar al-Assad da iyalinsa tserewa zuwa Moscow.
A lokacin, hankalin mutane ya karkata ga shugaban ƴantawaye Mohammed al-Jolani: matakinsa na watsar da sunan da aka san shi a baya inda ake kiran sa da ainahin sunansa na yanka - Ahmed al-Sharaa - da kuma naɗinsa a matsayin shugaban riƙo na Siriya.
A farkon watan Fabarairu, a bulaguronsa na farko zuwa wata ƙasa a matsayin shugaban Siriya, Sharaa ya je Saudiyya inda ya gana da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman domin tattauna alaƙa tsakanin ƙasashen biyu. Sai dai kafofin yaɗa labarai da shafukan sada zumunta sun karkata hankalinsu ga matar da take tare da Sharaa a lokacin ibadar Umrah - mai ɗakinsa Latifa al-Droubi (wadda aka sani da Latifa al-Sharaa).
Bayan nan kuma, shugaban riƙon na Siriya ya je Ankara domin tattaunawa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan. A wanan karon, Droubi na kasancewa tare da mijinta a taruka.
Asali mai tushe
Babu wani bayani kan tarihin Droubi a hukumance. Sai dai bayan ganinta a taruka, kafofin yaɗa labarai a ƙasashen Larabawa sun fitar da wasu bayanai game da asalinta da kuma rayuwarta.
Misali, jaridar Okaz ta Saudiyya ta ba da rahoton cewa dangin Droubi sanannu ne kuma masu aƙidar Sunnah da ke zaune a birnin Al-Qaryatayn da ke Lardin Homs na Siriya sannan kuma ta haifa wa Sharaa yara uku.
Okaz ta ambato wasu majiyoyi waɗanda ba na hukuma ba da ke cewa Droubi ta yi digiri na biyu a harshen Larabci da adabi.
Uwargidan shugaban ta fito daga ahalin da suka yi suna a kan addinin musulunci, har da Sheikh Abdul Ghaffar al-Droubi - wani makarancin Qur'ani a Siriya wanda ya rasu a 2009.
Al-Monitor, ɗaya daga cikin fitattun kafofin yaɗa labarai a Amurka da ke mayar da hankali kan al'amuran da suka shafi Gabas ta Tsakiya, ta bayyana cewa "tsatson iyalan Droubi ya samo asali ne daga Daular Usmaniyya lokacin da ɗaya daga cikin kakanninta, Alaa al-Droubi, ya riƙe muƙamin jakadan Daular Usmaniyya tare da zama Firaiministan Siriya na biyu a shekarar 1920, sai dai an yi masa kisan gilla kwanaki 26 bayan karɓar mulki."
Bayan juyin mulkin da aka yi a Siriya cikin 1970, ƴan aƙidar Alawi - wanda wani ɓangare ne na ɗariƙar Shi'a - sun nuna wa ƴan Sunni wariya waɗanda suka jagoranci ƙasar tsawon ƙarni da dama. A yanzu waɗannan iyalai na farfaɗowa, in ji mai nazari Cedric Labrousse da La Repubblica ta ruwaito.
Labrousse ya kuma shaida wa jaridar - duk da cewa bai bayyana majiyoyinsa ba - cewa Droubi ta haɗu da Sharaa a Damascus a lokacin da suke karatu a jami'a. Ya ce da alamu sun yi aure a 2013 lokacin da yake shugabantar Jabhat al-Nusra kuma tana zama tare da shi a ɓoye a yaƙin basasa.
Labrousse ya kuma rubuta a shafin X cewa: "Mace ce mai nuna irin yanayin dangin da ta fito masu tasiri da mutunta jama'a." Ya ƙara da cewa shi ma Sharaa ya fito ne daga tsatson iyali masu girmama jama'a.
Fitaccen ɗanjarida a Siriya kuma mai shirya fina-finai, Waed al-Khateeb, ya yi tsokaci kan hotunan farko na Droubi ta hanyar rubutu a shafukan sada zumunta inda ya ce: "Rigarta da Hijabinta ya yi kama da babbar riga da hijabin gama-garin matan Siriya - waɗanda ba a san su ba - kuma ba sa samun wakilci a muƙaman gwamnati."
Ayyuka ga al'umma
Wani muhimmin abu game da tarihin Droubi ya bayyana a lokacin ganawar da mijinta ya yi da wata tawagar al'ummar matan Siriya mazauna Amurka a Damascus a ƙarshen watan Janairu.
A cewar kafofin yaɗa labaran Siriya, taron yana ƙunshe da manufofi: sabuwar gwamnatin Siriya na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da al'umomin ƙasar mazauna ƙasar waje yayin da kuma take burin bayyana tsarin buɗaɗɗiyar gwamnati.
Cikin sama da wata biyu da suka gabata, Sharaa ya yi hira da ƴanjarida daga kafafen watsa labarai na duniya, har da BBC, inda ya yi magana game da yadda ya ajiye aƙidarsa ta Jihadi ya kuma nemi ya kawar da fargabar da ake na yiwuwar gwamnatinsa ta ƙaƙaba takunkumi kan hakƙoƙin mata a ƙasar. Ya kuma yi alƙawarin ba zai muzgunawa ƴan Alawi ba waɗanda suke mara wa Bashar al-Assad baya, duk da a baya-bayan nan, lamura na nuna cewa ba lalle ba ne ya samu ikon hana faruwar hakan.
A wannan ganawa ce shugaban riƙo na Siriya ya gabatar da mai ɗakinsa ga tawagar.
Dakta Abdul Hafiz Sharaf, mamba a ƙungiyar ƙawancen Airiya da Amurka don tabbatar da zaman lafiya, wanda ya halarci taron, ya bayyana Droubi a matsayin matashiya mai mutunta jama'a wadda ke sanya hijabi amma ba niƙabi ba sannan kuma tana yin shiga ta al'adar Siriyawa.
Makoma
Tsohuwar mai ɗakin shugaban Siriya, Asma al-Assad da Droubi da alama suna kamanceceniya a wasu ɗabi'unsu. Dukkansu ƴan Sunni ne daga Homs kuma duk ƴaƴansu uku.
"Assad ta fara ne a ƙarƙashin inuwar mijinta, daga baya ne kuma danginta da makusantanta suka mayar da hankali kan harkokin tattalin arzikida kuma samun tasiri a ƙasar," in ji ƙwararriyr mai sharhi kan Gabas ta Tsakiya, Marianna Belenkaya, a wata hira da BBC. Ta bayyana cewa tuni aka soma tattaunawa game da dangantakarta da Droubi. "Akwai raɗe-raɗi cewa an naɗa mijin ƴar'uwarta a matsayin gwamnan Damascus," in ji ta.
Sai dai ita sabuwar uwargidan shugaban ƙasa ba fitacciya ba ce. Duk da bayyana a taruka uku, har yanzu ba ta yi magana a bainar jama'a ba.
"A yanzu, zai yi wuya a iya bayyana yadda mutane ke kallonta. Amma a bayyane take ƙarara cewa za a tallata ta tare da nuna ta a cikin jama'a saboda Sharaa yana son ya nuna kansa a matsayin shugaba mai sauraron jama'a ba mai tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci ba," in ji Belenkaya.
Wani mai sharhi kan Gabas ta Tsakiya, Ruslan Suleimanov yana da ra'ayi na daban: "Sharaa na nuna matarsa saboda yanayin da ke buƙatar hakan - janye takunkuman da aka ƙaƙaba wa Siriya da kuma cire HTS daga jerin ƙungiyoyin ta'addanci. Sai dai da zarar jami'an sabuwar gwamnati sun samu yardar ƙasashen duniya, babu buƙatar nuna ta..."
Ya tuna lokacin da HTS ta karɓe iko da Lardin Idlib, ba a ga Droubi. Kamar yadda ƴan ƙungiyar ke yi a lokacin, iyalan shugabannin HTS ba sa bayyana gaban jama'a.
Amma idan Droubi ta samu gagarumar rawar da za ta taka a Siriya da kuma ƙasashen duniya, tana da misalai da dama da za ta yi la'akari da su daga ƙasashen Larabawa. Belenkaya ta ce Sheikh Moza - matar tsohon Sarkin Qatar kuma mahaifiyar sarkin ƙasar na yanzu - wadda ta yi karatu a ƙasashen yamma, ta bayar da gudummawa sosai ga ci gaban Qatar." Ta kuma yi ƙarin haske kan Noura Al-Saud, ƴar'uwar sarkin Saudiyya na farko, wadda ita ce mai ba shi shawara.