Matsalar tsaro za ta haifar da yunwar da ba a taɓa gani ba a arewacin Najeriya - MDD

Asalin hoton, OTHERS
Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargadin cewa karuwar hare-hare da taɓarɓarewar tsaro a arewacin Najeriya na haifar da yunwa a matakin da ba a taɓa gani ba.
Bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa kusan mutane miliyan 35 za su fuskanci rashin abinci mai tsanani a lokacin fari na 2026, mafi girma da aka taba samu a Najeriya kuma mafi girma a nahiyar Afirka baki ɗaya.
Bayanan shirin abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa, ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun tsananta kai hare-harensu a wannan shekara ta 2025.
A watan da ya gabata kaɗai, an ruwaito cewa, ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda ke da alaƙa da al-Qaeda, ta kai hare-harenta na farko a Najeriya.
A lokaci guda, ita ma ƙungiyar ISWAP na faɗaɗa tasirinta a arewacin Najeriyar da yankin Sahel.
Daga cikin hare-haren da ƙungiyoyin suka kai a baya-bayan nan, sun haɗa da kwanton-ɓaunar da suka yi wa dakarun sojin Najeriya a jihar Borno, har ma suka halaka wani janar, da waɗanda aka kai makarantu har ma aka sace ɗaruruwan ɗalibai.
''Masu ɗauke da makamai sun zama babbar barazana ga zaman lafiya a Najeriya, kuma illolinsu na wuce iyakokin kasar," in ji David Stevenson, Daraktan shirin a Najeriya.
Ya ƙara da cewa: ''Jama'a na fuskantar matsin lamba daga hare-haren da ake kaiwa abin da ke haifar da yunwa, domin a yankuna da dama fargaba na hana manoma zuwa gona don noma abinci, ga shi kuma buƙata na karuwa''.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shirin ya ƙara da cewa al'ummar arewacin ƙasar ne suka fi fuskantar tasirin rashin tsaron daga shekaru goma zuwa yanzu, inda manoma a karkara ba sa iya zuwa gonakinsu.
Ya ƙara da cewa kusan mutane miliyan shida ne ke fama da rashin abinci a yankunan da rikici ya shafa a jihohin Borno, da Adamawa, da Yobe.
Hasashen ya nuna cewa mutum kimanin dubu goma sha biyar a Borno kaɗai za su gamu da matsananciyar yunwa ta innanaha, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don ceton rayuwarsu.
A gefe guda kuma dama tuni yara na cikin wani mummunan yanayi na fama da tamowa a musamman a Sokoto, da Katsina da Yobe, da Zamfara, inda rashin abinci mai gina jiki ya fi yawa.
A yanzu dai kusan mutane miliyan ɗaya ne ke dogaro da taimakon abinci daga Majalisar Ɗinkin Duniya.
Kuma suk da haka, ƙarancin kuɗaɗe ya tilasta wa hukumar rage wasu shirye-shiryen a watan Yuli, wanda ya shafi yara sama da 300,000.
A wuraren da asibitoci suka daina aiki kuwa, rahoton na WFP ya ce matsalar rashin abinci mai gina jiki ta taɓarɓare daga mataki ma "mai tsanani" zuwa mataki "mai matuƙar haɗari" a zango na uku na wannan shekara.











