Yadda ƙudurin dokar haraji zai shafi rayuwar talakan Najeriya

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Makonni bayan miƙa wasu kudurori huɗu da ke da nufin yin garambawul ga tsarin harajin Najeriya ga majalisar mokokin ƙasar da Shugaba Bola Tinubu ya yi, har yanzu wannan batu na ci gaba da haifar da cecekuce a majalisar da ma ɓangarorin ƙasar baki ɗaya game da manufar waɗannan kudurorin.

Wasu dai sun bayyana fargabar cewa kudurorin na iya jawo ƙarin haraji ta yadda za su ƙara dora wa ƴan ƙasar nauyi.

Ra’ayoyin ƴan Najeriya dai sun bambanta kan wannan lamari, inda da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan abin da wannan kuduri ke nufi, amma wasu kuma sun zabi su jira cikakken bayani kafin su yi tsokaci a kai.

Amma babban abin da ya fi ci wa talakan Najeriya tuwo a ƙwarya shi ne: ta yaya wadannan sauye-sauyen za su shafi rayuwarsu?

Haraji kan kuɗaɗen da mutane ke samu

Daya daga cikin abubuwan da ke janyo cecekuce a kudurin dokar shi ne batun harajin da ake cirewa daga kuɗin da mutum ke samu wato Personal Income Tax a Turance.

A sabon ƙudurin dokar, an sake fasalin harajin da ake cirewa daga aljihun jama’a inda gwamnatin tarayya ta yi iƙirarin cewa za a ɗauke nauyin haraji daga kan masu ƙaramin ƙarfi.

Ƙudurin dokar dokar ya ce ba za a buƙaci mutanen da ke samun kudaden da suka yi kasa da naira 800,000 a shekara su biya haraji kan wadannan kudaden ba, har sai kuɗn da ake samu a shekara ya kai milaiyan 2.2 kafin ya fara biyan harajin kashi 15 cikin 100 a kai.

A wani ɓangaren kuma, dokar ta ƙara kason harajin da waɗanda kuɗadensu suka zarta wannan adadin za su biya, kamar yadda Dr Zaid Abubakar, shugaban hukumar tattara kuɗaden shiga ta jihar Kano ya yi bayani.

''Harajin an yi shi ne kamar yadda ake cewa a Turance 'progressive', ma'ana yayin da kuɗin da kake samu ke ƙaruwa haka ma kason harajin da kake biya ke ƙara yawa, amma da gaske masu ƙaramin ƙarfi za su samu sauki ta wannan ɓangaren''.

Dr Zaid ya ƙara da cewa, a wani ɓanagren kuma wannan dokar na iya sanya mutane su fara ɓoye asalin kuɗaɗen da suke samu domin su guje wa biyan haraji a kai.

"Ganin haka, ba kowa ne zai iya bayyana ainihin kuɗin da yake samu ba, wasu za su fara ɓoye-ɓoye, suna rage kuɗin da suke samu a shekara, sai dai idan gwamnati ba ta ɓullo da wata hanyar gano irin waɗannan bayanan ba, wannan na ɗaya daga cikin illolin da dokar za ta iya haifarwa'' in ji shi.

Harajin VAT

Wataƙila ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke cikin tanade-tanade da yawa na wannan kuduri shi ne abin da ya shafi harajin VAT, wanda shi ne harajin da ake sanyawa a kan kayayyakin da aka sarrafa.

Gwamnatin Najeriya ta yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ya saurari koke-koke da ƴan Najeriya ke yi, musamman talakawan ƙasar waɗanda ke fama da matsalar tsadar rayuwa sakamakon manufofin gwamnatin na gyara tattalin arzikin ƙasar, wanda ya sa dokar ta bayar da damar cire harajin VAT a kan kayayyakin abinci, kayayyakin asibiti, da Ilimi, da kasuwancin sufuri.

Misali, kuɗin makaranta ko hayar da masu gida ke biya ko siyayyar da masu makaranta suka yi don kasuwancin ilimantar da ƴan Najeriya ba za su kasance daga cikin waɗanda ake biyan harajin VAT akansu ba. Haka abin yake ga masu asibitoci, da masu sana’ar noma, da masu siyan ababen hawa na sufuri.

Amma dokar ta ce za a ƙara kason da ake karɓa a matsayin VAT daga kashi 7.5 cikin ɗari zuwa kashi 15, wanda hakan kamar yadda Dr Zaid ya yi bayani yana iya ƙara farashin kayayyakin da ƴan Najeriya ke saya a kasuwa sakamakon ƙarin harajin da masu sarrafa kayayyakin za su fuskanta.

Ya ce: ''Duk abin da ake biyan harajin a kai yana iya ƙara kuɗi, manyan misaial giuda biyu su ne kuɗin wutar lantarki da kuma amfani wayar salula, mutane za su rage watyar da suke bugawa kuma har farashin data ma zai ƙaru wanda hakan na iya kawo cikas a rayuwar mutane.''

Dr Zaid ya ƙara da cewa idan aka ƙara farashin lantarki, dole ne kamfanoni masu sarrafa kaya su ƙara farashin kayayyakinsu wanda daga ƙarshe ƴan Najeriya ne za su cike giɓin da aka samu a ribar da kamfanoni ke nema kan kayayyakinsu.

Harajin bunƙasa ayyukan ci gaba

Batun harajin da ake amfani da shi domin bunƙasa ayyukan da ke kawo ci gaba a al'umma wanda aka fi sani da ‘Development Levy’ wanda shi ne ake amfani da shi wurin gudanar da ayyuka da shirye-shirye na wasu hukumomin gwamnati da suka haɗa da asusun tallafawa ɓangaren ilimi (TETFUND) da hukumar kula da ci gaban fasahar sadarwa (NITDA) da kuma hukumar inganta ɓangaren kimiyyar injiniyoyi (NASENI).

Sabuwar dokar za ta nemi a rage kuɗaɗen da ake bai wa waɗannan hukumomi daga shekara ta 2025 zuwa shekara ta 2030 inda za a dakatar da ba su duk wasu kuɗaɗe. hakan na iya gurgunta ayyukan da waɗannan hukumomi ke gudanarwa wanda suka shafi ɓangarorin ilimi da kimiyya wanda ke matuƙar tasiri a rayuwan ƴan najeriya baki ɗaya.

Farfesa Ahmed Bello Dogarawa malami ne a tsangayar nazarin akanta da ke jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ya bayyan cewa dokar za ta buƙaci a mayara da harajin da ake bai wa waɗannan hukumomi ya zama guda ɗaya a madadin yadda ya ke a yanzu da kowace hukuma tana da na ta.

''Za a mayar da harajin ya zama guda ɗaya a tsakanin waɗannan hukumomin, amma inda matsalar ita ce a wurin rabo. Ttsakanin shekarar 2025 zuwa 2027 idan aka karɓi wannan harajin za a riƙa bai wa hukumar TETFUND kashi 50 kowace shekara, sannan a 2027 za a dakatar da bai wa NITDA da NASENI ko kwabo, ba su da wata hanya da za su samu kuɗin gudanar da al'amuransu.

"Daga shekara ta 2030, ita ma TETFUND za a dakatar da kuɗaɗen da ake ba ta, kuma za a fara amfani da duka kuɗin da aka samu wurin bai wa ɗalibai bashi."

A halin da ake ciki yanzu dai ba a cimma matsaya kan waɗannan sauye-sauyen da ake neman yi a ɓangaren harajin ƙasar ba, yayin da ƙudirorin ke gaban majalisun dattawa da ta wakilai.