Golan Bayern Munich Neuer zai yi jinyar makonni

Neuer ya lashe Champions League sau biyu tare da Bayern

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Neuer ya lashe Champions League sau biyu tare da Bayern
Lokacin karatu: Minti 1

Kyaftin ɗin Bayern Munich Manuel Neuer zai yi jinyar makonni bayan ya ji rauni a tsokar ƙafarsa ta dama.

Tsohon mai tsaron ragar na Jamus mai shekara 38, ya ji raunin ne a wasan da Champions League da ƙungiyarsa ta buga da Bayer Leverkusen a ranar Laraba da dare.

Jonas Urbig ne ya maye gurbinsa a wasansa na farko a minti na 59, inda Bayern ɗin ta cinye wasan da 3-0 a gidanta.

Manuel Neuer ya ji rauni a tsokar ƙafarsa ta dama.

"Tawagar likitoci ta FC Bayern Munich ce ta tabbatar da hakan. Saboda haka zai yi jinya na wani lokaci."

Neuer na buga wasan da aka fara da shi na 150 a gasar kafin ya fita, inda ya zama ɗanwasa na huɗu a tarihi da ya kai wannan matsayin bayan Cristiano Ronaldo (178), da Iker Casillas (176), da Lionel Messi (150).

Shi ne ɗanwasa na farko kuma da ya buga wasanni 150 a gasar, waɗanda duka aka fara da shi.

Neuer, wanda ya buga wa Bayern jimillar wasanni 554 tun bayan komawa can daga Schalke 04 a 2011, wasa 33 ya buga a kakar bana.