Ƙaura mai hatsari da ba a cika dawo ba

Asalin hoton, bbc
Adama da Moussa Sarr sun rasa sanin iya adadin kwanakin da suka yi a cikin teku.
Waɗannan ’yan’uwa biyu sun yi tafiya ne zuwa wani wuri da ke gabar tekun Afirka ta Yamma, a cikin wani kwale-kwalen kamun kifi na Senegal da ake kira da pirogue. Suna cikin fasinjoji 39, wadanda dukkansu ke fama da rashin abinci mai gina jiki, inda da yawa ke daf da mutuwa.
Adama mai shekara 21, wanda da kyar yake magana ya bayyana cewa akwai wani lokaci da Moussa mai shekara 17 ya fada cikin tekun don ya ga wani jirgin kamun kifi ya bayyana a nesa, ruwa ya kusan cinye shi ba dan ma'aikatan kamun kifi da suka gan shi ba kuma suka ceto shi.
Yayin da jirgin kamun kifin ya matsa kusa da kwale-kwalen su Adama, masu kamun kifin sun ce yanayin da suka gan wadanda suka tsira abu ne mai ban tausayi tare kuma da gawarwaki 7.
Kwale-kwalen Pirogue din ya tashi ne daga Senegal makonni biyar da suka gabata, tare da mutum 101.

Asalin hoton, bbc
Waɗanda suka tsira sun yi nisan tafiyar daruruwan mil a kan daya daga cikin hanyoyin bakin haure mafi hatsari a duniya - mashigin tekun Atlantika ta Arewa daga Senegal zuwa tsibirin Canary, tsibiran kasar Spain mai tazarar mil 1,000.
Sun fara tafiyar ne a ranar 10 ga watan Yuli, daga ƙauyen Fass Boye da ke bakin teku.
Adama da Moussa sun fito ne daga iyalen masunta a kauyensu inda suka koyi kamun kifi kuma da yin aiki tare.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma kamar yawancin matasa a Senegal, hankalinsu ya karkata zuwa Turai. "Kowa yana son tafiya a cikin kwale-kwale zuwa Turai," in ji Adama. "Abin da ya kamata ayi kenan."
Yayin da Adama ke zaune a farfajiyar gidan su bayan ya dawo Senegal lami lafiya, amma kuma a rame, ya ce tafiyarsu ta fara da yamma ne, inda ya ce da shi da Moussa da kuma wasu 'yan uwan su guda biyu, Pape da Amsoutou, masu shekaru 40 da 20 ne suka shiga cikin kwale-kwalen pirogue.
Ba kamar Bahar Rum ba, babu ‘yan sintiri da ke kula da hanyar Arewacin Tekun Atlantika. Babu wanda ke neman jiragen ruwan da ke cikin matsala. Idan aka rasa hanya a tsibirin Canary ko Cape Verde, za a iya ɓacewa cikin babban Tekun Atlantika kuma.
A cikin kwanaki ukun farko na tafiyarsu, kwale-kwalen Adama da Moussa ya yi fama da iska mai ƙarfi amma a rana ta hudu, iskar ta lafa sai kwale-kwalen ya ci gaba da aiki a cewar Adama.
Ya ƙara da cewa a wannan lokacin ne fasinjojin suka fara fargaban cewa 'yan kwanaki kadan ne kawai ya rage musu a tekun.
Bayan kwana na shida a kan tekun, ba tare da hango wani fili ba, sai gardama ta barke tsakanin fasinjojin game da ko za a ci gaba da tafiyar ko kuma a juya a koma in ji Adama.
"Kyaftin din ya yanke shawarar cewa za mu ci gaba da tafiya saboda muna da isasshen abinci da ruwa kumababu iska mai ƙarfi."
Shawarar kyaftin din ya ƙara wa fasinjojin kuzari, sai suka fara cin abinci da yawa, har ma suke yin amfani da ruwan sha wajen wajen yin alwalla domin suyi sallah.
A wajen kwana na shida ne, kayan abinci da ruwa suka fara raguwa. Akwai yara hudu a cikin jirgin, wasu daga cikin manyan fasinjojin suka ba da abincinsu na ƙarshe ga ƴan yaran, wasu mutane kuma suka fara ɓoye abinci duk da cewa akwai waɗanda suka fara mutuwa kuma wasu suna cikin mawuyacin hali.
Adama ya ce ya kasa tantance ainihin ranar da akayi mutuwar farko, amma ya ce ya faru ne jim kadan bayan cika makon farko inda wanda ya fara mutuwa wani gogaggen kyaftin na kamun kifi ne, bayar mutuwan sa da kwana shida ne wani ya sake mutuwa, tun daga lokacin kuma kullum sai an mutu.
“Da farko, za mu yi wa kowane mamaci sallar gawa sai mu jefa gawar cikin tekun amma daga baya sai muka dingi jefa gawarwarkin cikin teku kawai saboda ba mu da karfin yi sallar gawa ka duk wanda ya mutu” in ji Adama.

Asalin hoton, bbc
Labari ya fara bazuwa cikin ƙauyen su cewa jirgin bai iso ba.
Mahaifiyar Adama, Sokhna, ta bayyana cewa "Dukkanmu mun san cewa kwanaki biyar ko shida ya kamata jirgin ruwa ya yi ya isa Spain, amma su sati daya ya wuce babu labarin su, lamarin da ya jefa ni cikin yanayi na damuwa da ƙunci da rashin cin abinci da rashin lafiya."
Kusan duk fasinjojin da ke cikin jirgin su fito ne daga Fass Boye ko kuma yankunan da ke kusa, kuma da alama kowa da kowa a ƙauyen yana da alaƙa da aƙalla wani a cikin jirgin.
Iyalai da dama sun yi duk abin da za su iya, sun tuntuɓi hukumomin gida da ƙungiyoyin ƙaura, in ji mahaifiyar Adama.
Wani Mutum da ya kafa wata kungiya mai zaman kanta ya taɓa yin wani gargadi a kan jirgin da ya bata makonni biyu bayan tafiyarsa, amma babu wanda ya yi la'akari game da hakan har sai da kwale-kwalen ya ƙara makonni uku da ɓata.
A kan kwale-kwalen, wasu maza huɗu daga gida ɗaya sun hadu tare amma saboda da matsalar da suke ciki, babban su Pape ne ya fara mutuwa in ji Adama
Bayan wannan kuma sai ƙanin Adama, Amsoutou kawai aka wayi gari babu shi, ya ɓace in ji Adama.
Adama da Moussa sun dogara kan junan su, ruwan tekun ya zama ruwan shan su tare da jure zafin rana. Kowace dare, suna duba sararin samaniya don ganin wata alama daga tsibirin Canary, amma babu abin da ke bayyana.
Fiye da kashi uku na kasar na fama da talauci, a cewar bankin duniya. Matasa suna ganin ƙarancin damar samu a gida wanda hakan ya sa mutane ke tafiya mai hatsari don neman samun abun ciyar da iyalan su.
"Macky Sall ya gama sayar da tekun," in ji Assane Niang, wani kyaftin din kamun kifi mai shekaru 23, yana magana kan shugaban kasar Senegal.
Masunta a Fass Boye sun yi imanin cewa gwamnatin ƙasar ta ba da lasisi da yawa ga masu safarar jiragen ruwa na kasashen waje, wanda suke kame musu yawancin kifayen su.
Akwai matsin lamba na al'umma akan matasa da suyi tafiya a cikin waɗannan kwale-kwale, kuma akwai kyama ga waɗanda suka gaza ko ba su yi ƙoƙari ba.
Kwale-kwalen Pirogues da masu fasa-kwauri ke amfani da su ba su dace da tafiyar ba, yawanci ba a ƙera su da kyau, kuma man fetur na saurin ƙarewa Amma duk da haka, adadin bakin hauren da ke amfani da waɗannan kwale-kwalen don isa Spain yana karuwa a kowace shekara.

Asalin hoton, bbc
A cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya, kimanin mutane 68,000 ne suka samu nasarar isa tsibirin Canary ta jirgin ruwa daga yammacin Afirka tun daga watan Janairun 2020 kuma kusan 2,700 ne aka rubuta sun mutu ko kuma suka bace.
Sai dai akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu na iya ƙaruwa matuƙa, domin ba a iya samun iya adadin waɗanda suka mutu ko ɓace ba a rubuce.
Safa Msehli, mai magana da yawun hukumar ta IOM ta ce "Muna kiransu da tarkacen jirgin da ba a iya gani."
Wani bangare na matsalar shi ne yadda mutanen da ke barin Fass Boye, musamman masunta, ke da kwarin gwiwa kan damarsu, in ji Abdou Karim, wani masunci kuma mahaifin Pape Sarr, wanda ya mutu a cikin jirgin ruwa.
"Masunta suna tunanin cewa, idan sun shiga matsala, za su iya yin iyo," in ji shi. "Amma akwai iyaka, ba za ku iya yin iyo har abada ba. Teku ba zai riƙe ku ba."
Amma duk da haka, matasa masunta a Fass Boye sun ce har yanzu a shirye suke su dauki kasadar.
"A yanzu haka, ina tunanin tafiya a jirgin ruwan," in ji Niang, mai kamun kifi a bakin teku. "Masifun da ke biyo baya ba za su hana mu yin kokari ba."
Kimanin wata guda da tafiyar Adama da Moussa, wani babban jirgi ya bayyana a sararin inda mutane sama da 20 suka yanke shawarar yin amfani da wannan damar in ji Adama. Amma kuma tsakanin su akwai nisa.
Ya ce da yawa daga cikin wadanda suka tsira da kyar suke iya motsi. Sai kuma a ranar 14 ga Agusta, daidai makonni biyar bayan tafiyarsu, suka hango jirgin kamun kifi na Spain da zai kubutar da su.
Ma'aikatan jirgin na Spain suka taimaka musu hawa cikin jirgin kuma suka sanya gawarwakin bakwai a cikin robobi. Adama da Moussa suka kwanta tare a saman jirgin ruwan.
Sun tsira daga kwale-kwalen, amma Moussa ya kasance mai rauni sosai wanda shi ne na karshe a cikin mutum 63 da suka mutu a wannan tafiya.
"Ya mutu a kan jirgin ƴan Spain din da suka ceto mu, a kan ido na," in ji Adama.

Asalin hoton, bbc
An kai waɗanda suka tsira da ransu zuwa Cape Verde kuma sun shafe kwanaki shida suna jinya, kafin aka mayar da yawancinsu zuwa Dakar.
Wadanda suke iya tafiya, an ba su takardun magani kuma an mayar da su zuwa Fass Boye.
Lokacin da aka samu labarin adadin mutanen da suka mutu, an tafka kazamin zanga-zangar suka a kauyen wanda ya kai ‘yan sanda garin. An kama wasu dangi ciki har da wani daga dangi Adama da Moussa.
Iyalai sun ce mazauna garin da kuma dangin wadanda suka mutu sun tursasa wadanda suka tsira a gidajensu dalilin da ya sa aka kai su wani wurin daban da Fass Boye mayar don su warke gaba daya.
Adama da mahaifiyarsa Sokhna sun tafi su zauna da danginsu na kusa, suna gujewa tambayar Adama halin da suka shiga.
Iyalin sun yi hasarar ’ya’ya maza uku amma daya ya dawo da ransa.
Mutum 101 ne suka bar Fass boye don zuwa tsibirn Canary amma kuma 37 ne kacal suka dawo gida da ran su.










