Ana taƙaddama kan sunan masallaci a jihar Oyo

Oyo state governor

Asalin hoton, SEYIMAKINDE/FACEBOOK

Kungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya, (MURIC), ta yi watsi da matakin da gwamnatin jihar Oyo ta ɗauka na sauya sunan wani shahararren masallacin tsakiyar birnin Ibadan da ke kan titin Iwo, da Gwamna Seyi Makinde, wanda ta ce ba Musulmi ba ne ya yi.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci a gaggauta mayar da sunan masallacin tun na asali.

MURIC ta zargi Gwamnan na jihar Oyo da wuce gona da iri musamman kan ɗabi’unsa da ta ce yana yin shisshigi cikin harkokin addinin Musulunci – wani abu da MURIC ta ce sanya sunansa a bangon babban masallacin alhali yana a matsayin Kirista bayan kammala babban masallacin Adogba cin fuska ne ga al’ummar Musulmi a jihar.

A don haka ta buƙaci Gwamnan da ya bayar da umarni cikin gaggawa a cire sunansa daga bangon masallacin.

Ƙungiyar ta gabatar da buƙatar hakan a cikin wata sanarwa da Babban Daraktanta, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar.

MURIC ta ce matsalar ita ce Gwamnan ya sanya wa masallacin sunansa, kuma ba abin da za su amince da shi ba ne.

"Dalili ba da kuɗinsa aka sake gina masallacin ba, ya yi amfani da kuɗin gwamnatin jihar Oyo ne wajen sake gina masallacin.'' A cewarta

Bugu da ƙari, shi ba Musulmi ba ne, ya yi hakan ne kawai a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe. Wannan masallacin da ke bayan babban masallacin da ke tsakiyar birnin ya shafe shekaru aru-aru yana nan, kuma Musulmai na sallah a cikinsa ba tare da wata matsala ba. Mu Musulmi mun ji takaici da faruwar wannan lamari," in ji sanarawar.

Ta ƙara da cewa : "Tabbas wannan yana da matuƙar tasiri a kan Musulmi, domin waɗanda ba Musulmi ba za su nuna cewa wani gwamna Kirista ne ya gina mana Masallaci.

Yanzu muna cewa a cire sunansa daga masallaci, duk da sun cire sunan gwamnan daga babbar kofar shiga, sun bar sunansa a babban bangon ginin masallacin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan kun kasance masu tawali'u har ka cire sunan daga babbar kofa, me zai hana a cire sunansa daga bangon babban ginin masallacin?

Mu Musulmi, wannan ba abu ne da za mu yarda da shi ba." In ji Farfesa Ishaq Akintola

Kungiyar ta bayyana sauya sunan masallacin da sunan gwamnan a matsayin ɓatanci ga wurin ibadar Musulmi bisa la’akari da cewa Gwamna Makinde ba Musulmi ba ne.

A shekara ta 2019, Gwamnatin jihar Oyo ta rusa babban masallacin Adogba da ke kan titin Iwo, Ibadan, domin fitar da hanya ga tashar motocin Bus da ta ƙudurta ginawa a shekarun baya.

Inda a yanzu ta sake gina wani Masallaci a madadin tsohon masallacin da aka rushe.

A cikin ɓangarorin masallacin akwai makarantar koyon Larabci, da Cibiyar Bincike da ɗakin littattafai da karatu da ɗakin taro da filin ajiye motoci da wadatattun hanyoyin sadarwa. Kuma ƙungiyar ta yaba da samar da duka waɗannan.

Sai dai tun bayan sauya sunan masallacin da sunan Gwamna Makinde, lamarin ya fusata kungiyar MURIC, tare da zargin cewa Gwamnan ya yi haka ne don neman suna.

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar Oyo sai dai haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.

A baya a yayin wani taro ranar Jumu'a a watan Oktoban 2019, Gwamna Makinde ya ce za a rusa babban masallacin tare da wani katafaren coci da ke a Adogba Iwo cikin birnin Ibadan domin share fagen gina tashar mota.

To amma Musulmi na cewa ba sa adawa da sake gina masallacin amma suna neman a cire sunan Gwamna Seyi Makinde a bangon masallacin ɗungurungum.