Wace ce Ghazala Hashmi, Musulma ta farko da ta zama gwamna a Amurka?

Lokacin karatu: Minti 3

Nasarar da ɗantakarar jam'iyyar Democrat Zohran Mamdani ya yi ta lashe zaɓen magajin garin New York ta fi jan hankali, amma ba shi kaɗai ne Musulmi da ya kafa tarihi ba a ranar Talata.

Takwararsa Ghazala Hashmi ma ta yi nasarar cin zaɓen ƙaramar gwamna wato Lieutenant Governor, inda ta zama mace Musulma ta farko da ta samu nasara a zaɓen jiha baki ɗaya a faɗin Amurka.

"Mun samu nasara ne saboda damarmakin da ake da su a ƙasar nan," in ji ta cikin jawabin nasarar da ta yi.

Hashmi ta doke ɗan jam'iyyar Republican John Reid, wanda tsohon mai gabatar da shiri ne a kuma ɗan luwaɗi na farko da ya yi takara.

Daga farfesa zuwa 'yarsiyasa

Matar da aka haifa a jihar Hyderabad ta Indiya a shekarar 1964, Hashmi ta koma Amurka tana 'yar shekara huɗu tare da mahaifiyarta da ɗan'uwanta.

Sun sauka a Georgia tare da mahaifinta, wanda malami ne a jami'ar Georgia Southern University.

Ta girma a daidai lokacin da ake fama da wariyar launin fata a makarantun gwamnati. Ta kammala sakandare da sakamako mafi kyawu kafin ta yi karatu jami'o'in Georgia Southern University da Emory University da ke Atlanta.

Ta shafe kusan shekara 30 a matsayin farfesar adabi da kuma jami'ar mulki a Virginia, kafin manufar Trump ta hana wasu 'yan ƙasashen Musulmi shiga Amurka ya ƙarfafa mata gwiwar neman takara a 2019.

'Lokuta masu ƙalubale'

Hashmi ta siffanta yadda ta fuskanci "lokuta na ƙalubale" a matsayinta na Musulma a Amurka lokacin mulkin Trump na farko.

"A lokacin na ji akwai buƙatar na samu damar fitowa bainar jama'a domin mayar da martani kan waɗannan lamurra," kamar yadda ta bayyana a wata hira da ta yi a 2020.

A 2019, ta nemi kujerar sanata ta jihar, wadda ɗan Republican ke riƙe da ita, kuma ta yi nasarar da ba a tsammata ba. Ta zama mace Musulmi ta farko a majalisar dattawan jihar Virginia.

A wannan shekara kuma, nasarar tata a matsayin ƙaramar gwamnan Virginia ta samu ne bayan alƙawurran inganta ilimi, da faɗaɗa inshorar kiwon lafiya, da kuma kare haƙƙin zubar da ciki.

Yayin jawabin samun nasara ranar Talata, Hashmi ta sake tuna wa magoya baya dalilin da ya sa ta tsunduma siyasa.

"Na so ne na mayar da martani ba wai kawai na zauna kallo ana ƙala wa wasu al'ummomi sharri ba."

Mene ne ƙarfin ikonta?

Babban aikin Lieutenant Governor ko kuma ƙaramin gwamna a Virginia shi ne shugabancin majalisar dattawan jihar.

Sai dai ba shi da ƙuri'a a majalisar har sai a lokacin da aka samu kunnen doki kan wani lamari, inda za ta kaɗa tata ƙuri'ar domin samun rinjaye.

A jiharsu ta Virginia, Hashmi ce za ta gaji gwamnan jihar duk lokacin da tsautsayi ya sa ya mutu, ko ya sauka daga muƙaminsa.

Sannan za ta zama muƙaddashiyar gwamnan idan ba shi da lafiya, ko ya yi balaguro fiye da kwana 20.