Masu wasan lanƙwasa jiki da 'yar ƙwallon Najeriya cikin hotunan Afirka

    • Marubuci, Natasha Booty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zababbun hotunan wannan mako daga sassan nahiyar Africa da ma wasu kasashen duniya:

Mutum biyu suna iyo sanye da kayan su a Siwa Oasis da ke arewa maso yammacin Masar a ranar Litinin.

Asalin hoton, FAREED KOTB / ANADOLU / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Masu su na iyo a saman tafki a Siwa Oasis da ke arewa maso yammacin Masar a ranar Litinin.
Wasu nau'ikan halittun ruwa na wasa cikin ruwa yayin da fitila mai haske ta mamaye ruwan.

Asalin hoton, TAHSIN CEYLAN / ANADOLU / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A can gabashin yankin washe garin ranar, an dauki hoto daga karkashin ruwa na hasken da halittun ruwa ke fitarwa a Bahar Maliya...
Kunkurun ruwa yana wasa a ruwan da ke zagaye da wuri mai launin kore.

Asalin hoton, TAHSIN CEYLAN / ANADOLU / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Bioluminescence kalma ce a Turancin Ingilishi da ke nufin hasken da wasu halittu ke fitarwa daga jikinsu galibi idan suka fuskanci barazana sakamakon motsi ko daga halittun da ke iya halaka su.
Daruruwan masu son wake-wake sun halarci Bikin Ranar Masu wasan kaho a Nairobi, babban birnin Kenya.

Asalin hoton, FREDRIK LERNERYD / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Daruruwan masu son wake-wake sun halarci Bikin Ranar Masu wasan kaho a Nairobi, babban birnin Kenya a ranar Asabar.
Wasu yara mata uku sanye da fararan kaya suna wasan lankwasa jiki.

Asalin hoton, PHILL MAGAKOE / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar ne kuma, wasu kananan yara masu wasan lankwasa jiki suka yi atisaye a makarantar horar da matasan yan wasan lankwasa jiki a Thembisa da ke Afirka ta Kudu.
Tsuntsayen jimina na tafiya a wani fili bayan faduwar rana.

Asalin hoton, GIANLUIGI GUERCIA / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A Afirka ta Kudun kwanaki bayan nan, an ga tsuntsayen jimina cikin wata gona a Oudtshoorn.
Wasu maza uku sanye da manyan kaya da dogayen huluna launin ja sun yi hoto kusa da bakin ruwa.

Asalin hoton, PATRICK MEINHARDT / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Yayin da damina ta fadi a Senegal, wasu malaman addini daga al'ummar Lebou sun taru a wani wajen biki a ranar Lahadi inda suke hasashen abubuwan da za su iya faruwa a shekara mai zuwa.
Yarwasan tsakiyar Najeriya Rinsola Babajide tana gudu a filin wasa rike da tutar Najeriya bayan da suka yi nasara.

Asalin hoton, ABDEL MAJID BZIOUAT / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Asabar, Najeriya ta lashe gasar kwallon kafa ta Mata ta Afirka inda ta doke mai masaukin baki Morocco 3 - 2 a wasan karshe.
Alkalin wasa yana tabbatar da kowane danwasa ya bi ka'idar wasan kafin su fafata.

Asalin hoton, MARVELLOUS DUROWAIYE / REUTERS

Bayanan hoto, Yanwasa daga Kamaru (Hagu) da Najeriya suna shirin fafatawa a gasar zakaru ta masu gwada kwanji a Abuja ranar Juma'a. A nan, alkalin wasa yana tabbatar da kowane danwasa ya bi ka'idar wasan kafin su fafata.
Washegarin ranar a Tunisia, mutane sanye da kayan al'ada suna daga hannu a bikin al'adu na Aoussou da ke Sousse.

Asalin hoton, MOHAMED MESSARA / EPA

Bayanan hoto, Washegarin ranar a Tunisia, mutane sanye da kayan al'ada suna daga hannu a bikin al'adu na Aoussou da ke Sousse.
Yansanda sanye da kayan sarki sun tare wani titi.

Asalin hoton, AMPE ROGERIO / EPA

Bayanan hoto, Haka nan a ranar Asabar, yansanda sun fantsama titunan babban birnin Angola inda mutane ke zanga-zangar tsadar man fetur. Zuwa yanzu, fiye da mutum 1,200 aka kama cikin kwanakin da aka shafe ana zanga-zangar.
Wani mutum na matsar da jakunkuna da aka daure a saman motar din.

Asalin hoton, AFP via GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Fasinjojin da ke wannan babbar motar mai komawa Khartoum a ranar Litinin na cikin fiye da mutum miliyan 12 da aka tilastawa barin gidajensu tun bayan barkewar yakin basasa a Sudan fiye da shekaru biyu da suka gabata. Yunwa da kisan kiyashi sun yi tasiri sosai a wasu yankunan kasar, a cewar Majalisar Dinkin duniya da Amurka.
Mutane na iyo a cikin teku bayan faduwar rana. Ana iya ganin wata mata sanye da doguwar riga da hijabi tsaye cikin ruwan da ya kai har kaurin kafafunta.

Asalin hoton, MAHMUD TURKIA / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Yayin da rana ta fadi a gabar ruwan Libya a ranar Juma'a, mutane suna wanka a tekun Tripoli.