Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kisan ƴan Shi'a Alawiyyawa a gidajensu ke tayar da hankalin ƴan Syria
- Marubuci, Lina Sinjab
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Middle East correspondent
- Aiko rahoto daga, Damascus, Syria
- Lokacin karatu: Minti 7
Shugaban riƙo na Syria ya yi kiran a samu haɗin kai a lokacin da ake ci gaba da rikici da kashe-kashen ramuwa a yankunan da ke goyon bayan hamɓararren shugaban ƙasar Bashar al-Assad a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗaruruwan mutane sun tsere daga gidajensu da ke lardunan Latakia da Tartus da ke gaɓar teku- yankunan da magoya bayan Assad su ka fi yawa.
Mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya haɗa da sace-sace da kashe-kashe, ciki har da na ƙananan yara.
A unguwar Hai Al Kusour, wadda akasarin masu zama cikinta ƴan ƙabilar Alawi ne da ke birnin Banias a gaɓar ruwa, mazauna yankin sun ce titunan birnin na cike da gawarwaki da aka yi wa jina-jina.
An harbe maza masu mabanbantan shekaru a kan titin, a cewar shaidu.
Ƴan ɗarikar Alawi, wani ɓangare ne na mabiya Shi'a, kuma su ne kashi 10 cikin ɗari na mutanen Syria waɗanda akasari mabiya aƙidar Sunnah ne. Assad ɗan wannan ɗarikar ne.
Mutane sun tsorata da har ba sa iya kallon waje ta tagar gidajensu a ranar Juma'a.
An katse intanet, sai dai bayan dawowar intanet ɗin, sun samu labarin mutuwar makwaftansu ta shafin sada zumunta na facebook.
Wani mutumi mai suna Ayman Fares ya shaida wa BBC cewa kulle shi da aka yi a gidan yari a baya-bayan nan ne ya cece shi.
Ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook a watan Agustan 2023 yana sukar mulkin Assad.
Jim kaɗan bayan haka aka kama shi, ba a sake shi ba har sai lokacin da ƙungiyoyin da suka ƙwace mulki suka sako shi bayan korar da aka yi wa Assad a Disamban da ya gabata.
Mayaƙan da suka kai samame kan titin Hai Al Kusour sun gane shi, saboda haka ba su kashe shi ba, amma kayansa ba su tsira daga wawushewa ba. Sun ƙwace motarsa sannan suka ci gaba da ɗiban kaya a cikin gidajen al'umma.
"Ba mu san su ba, ba zan iya gane yarensu ko kuma inda suka fito ba, sun yi kama da mutanen Uzbek ko kuma ƴan Checheniya," kamar yadda Fares ya faɗa wa BBC ta wayar tarho.
"Akwai kuma wasu ƴan Syria a cikinsu, amma ba daga cikin jami'an tsaron gwamnati ba ne. Haka nan ma akwai wasu fararen hula da suka shiga cikin masu kashe-kashen" In ji shi.
Mista Fares ya ce ya ga yadda aka kashe iyalai a cikin gidajensu, an bar mata da yara kwance a cikin jini. Wasu iyalan sun haye kan rufin gidajensu sun ɓuya amma ba su tsira ba. "Abin ya yi muni," in ji shi.
Ƙungiyar da ke sanya ido kan hakkokin bil'adama mai zaman kanta a Birtaniya ta ce sama da fararen hula 740 ne aka kashe a biranen Latakia da Jableh da kuma Banias da ke bakin ruwa.
Sannan an ruwaito cewa wasu mutum 300 daga cikin dakarun tsaron da kuma gyauron jami'an gwamnatin Assad na daga cikin waɗanda suka mutu a tashin hanklalin.
Sai dai zuwa yanzu BBC ba ta tabbatar da adadin waɗanda suka mutun ba.
Mista Fares ya ce lamura sun daidaita a lokacin da sojojin Syria da dakarun tsaro su ka iso birnin na Banias.
''Sun kori sauran ƙungiyoyin daga cikin birnin kuma suka samar da wata hanya da iyalai za su bi domin isa yankunan da ke da tsaro, in ji shi.
Ali, wani mazaunin Banias wanda ya buƙaci ka da mu bayyana cikakken sunansa, ya tabbatar da abin da mista Fares ya faɗi.
Ali wanda ya yi rayuwa a Kusour da matarsa da ƴarsa ƴar shekara 14, sun bar gidansu da taimakon jam'ian tsaro.
''Sun zo gidanmu. Mun tsorata sosai a lokacin da muke jiyo harbe-harbe da kuma ihun mutane a cikin unguwar. Bayan mun sami intanet ne muka sami labarin mutuwar mutane a Facebook. Amma a lokacin da su ka zo ginin da gidanmumu ya ke, mun yi zaton ta kare mana,'' in ji shi.
'' Kuɗi suke nema. Sun ƙwanƙwasa wa makwafcina suka kwace motarsa, da kuɗinsa da zinare da duk wani abu mai daraja da ya ke gidan. Amma ba su kashe shi ba.''
Wasu makwaftansu ƴan aƙidar Sunnah ne suka ɗauki Ali da iyalinsa, waɗanɗa ke bin ɗarika ta daban da su, kuma a yanzu suna zama tare da su.
''Mun yi rayuwa tare na tsawon shekaru, ƴan Alawi, masu aƙidar Sunna da ma Kiristoci. Ba mu taɓa fuskantar haka ba,'' ya shaida min.
''Masu bin aƙidar Sunna sun yi gaggawan kare ƴan ɗarikar alawi daga kashe-kashen, a yanzu kuma jami'ai sun shigo birnin za su tabbatar da doka da oda.''
Ali ya ce an kai iyalai wata makaranta a wata unguwa da akasari mutanen unguwar masu bin aƙidar sunnah ne, a inda za a kare su har sai an fitar da ƙungiyoyin da sukayi kisan daga Banias.
Tashin hankalin ya soma ne a ranar alhamis bayan magoya bayan Assad- waɗanda suka ƙi ajiye makamansu- suka yi wa jami'an tsaro kwantar ɓauna a biranen Latakia da Jableh da ke gaɓar teku inda su ka kashe gwammai.
Ghiath Dallah, tsohon birgadiya janar a sojojin Assad, ya sanar da sabuwar ƙungiyar tawaye mai hamayya da gwamnati mai ci a yanzu, inda ya ce ya na ƙoƙarin kafa ''sabuwar gwamnati domin ƴantar da ƴan Syria'
Wasu rahotanni na nuna cewa tsoffin jami'an tsaron gwamnatin Assad waɗanda suka ƙi ajiye makamai na kafa wata ƙungiyar tawaye a kan tsaunuka.
Mista Fares ya ce mafiya yawan alummar Alawi sun ƙi amincewa da su kuma sun ɗaura wa Dallah da wasu magoya bayan Assad ma su tsatsaurar ra'ayi laifi kan tashin hankalin.
''Suna amfana da zub da jinin da akeyi. Abin da muke buƙata a yanzu shi ne jami'ai a hukumance su rinjaye su su kuma hukunta masu kisan daga kungiyoyin da sukayi kashe-kashen saboda ƙasar ta dawo da tsaronta,'' in ji shi.
Sai dai wasu na ɗaura laifin kan shugaban riko Ahmad al-Sharaa, inda su ka ce shi ya rushe jam'ian tsaron Syria na sojoji da ƴansanda, ba tare da wata ƙwaƙwarar dabara kan yadda za ayi da dubban jam'ian da za a bari babu ayyukan yi.
Wasu daga cikin waɗannan mutanen, musannan ƴansanda, ba su da hannu cikin kashe kashen da akayi a lokacin gwamnatin Assad.
Sabbin hukumomin sun kuma sallami dubban ma'aikatan gwamnati daga aiki.
A yayin da kashi 90 cikin 100 na alummar Syria ke rayuwa a cikin talauci, kuma dubbai ba su da hanyar samun kudin shiga, hakan ya samar da yanayin da za a yi tawaye.
Ana samun banbancin ra'ayi a Syria kan abin da ke faruwa. Akasarin alumma na sukar kisan fararen hula, kuma an fara shirya zanga zanga a Damascus domin ta'aziyya ga waɗanɗa su ka mutu da kuma yin alawadai da tashin hankalin.
Sai dai a kwanakin da su ka gabata, an samu kiraye kirayen yin Jihadi a ɓangarori daban daban na Syria.
Mazauna birnin Banias sun ce akwai wasu fararen hula da suka shiga cikin kungiyoyin su ka ɗauki makamai su ka shiga dakarun wajen yin kashe kashen.
Mabiya aƙidar Sunnah masu rinjaye a Syria sun fuskanci zalunci a hannun dakarun gwamnatin Assad a cikin shekaru 13 da su ka gabata.
Hakan ya rura wutar ƙiyayya kan ƴan ɗarikar Alawee marasa rinjaye, waɗanda ake alaƙanta mabiyansu da laifukan yaƙi.
A cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama, akwai shaidu da ke nuna jam'ian tsaron Alawee na da hannu a kisa da kuma azabtar da dubban ƴan Syria, akasari kuma Musulmai mabiya aƙidar Sunni a lokacin mulkin Assad.
Sojoji da jam'ian tsaron da aka kashe mafiya yawan su mabiya aƙidar Sunni ne, kuma a yanzu wasu mutane a cikin alummar ƴan Sunni na kiran yin ramuwa, sai dai shugaban ƙasar ya yi kiran a kwantar da hankali.
A yanzu, wajibi ne Sharaa, wanda dakarunsa su ka hamɓarar da Assad watanni uku da su ka gabata, ya daidaita samar da tsaro ga kowanni ɓangare da kuma ƙoƙarin samar da adalci kan laifukan gwamnatin Assad.
A yayin da ya ke da iko kan wasu dakarun da suka taimaka mishi hawa karagar mulki, wasu ɓangarorin sun fi karfinsa.
Waɗannan ɓangarorin sun haɗa da mayaƙan ƙasashen waje masu tsatsaurar ra'ayin addinin musulunci.
Domin kai Syria ga mulkin dimokraɗiyya da tabbatar da zaman lafiya, wasu da dama na ganin sai Sharaa ya kawo ƙarshen duk wasu mayaƙan ƙasar waje, ya kuma kawo tsarin mulkin da zai kare haƙƙin dukkanin ƴan Syria ba tare da la'akari da addinsu ko inda su ka fito ba.
A yayin da ake ganin yana aiki wajen samar da tsarin mulkin, kula da ƙungiyoyin da ke tayar da hankalin da kuma korar mayaƙan ƙasar waje zai iya zame mishi abu mai wahala.