An zargi dakarun Syria da kashe ɗaruruwan fararen hula

Lokacin karatu: Minti 1

An zargi dakarun Syria da kashe ɗaruruwan fararen hula ƴan Alawi tsiraru, a ci gaba da rikicin da ake yi a kasar.

Kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria ta ce sama da mutum 1,000 aka kashe tsakanin Juma'a zuwa Asabar, a rikici mafi muni tun kifar da gwamnatin Assad a watan Disamba.

Rahotanni sun ce daruruwan mutane sun bar gidajensu a yankin na ƴan alawi tsiraru a Syria, bayan kashe mutum sama da 1,000 kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria ta bayyana duk da cewa BBC ba ta tabbatar da gaskiyar ikirarin ba.

Sai dai an bayyana adadin ya ƙunshi dakarun gwamnati da kuma mayakan da ke goyon nuna baya ga Assad, wadanda ke gwabza fada a yankin Latakia tun ranar Alhamis.

Kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria ta ce mambobin gwamnatin musulunci 125 da kuma mayakan da ke goyon bayan Assad 148 aka kashe a rikicin.

A wani sakon bidiyo, mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Syria Kanal Hassan Abdel Ghani ya yi kira ga mayakan su ajiye makamansu.

Ya ce duk wanda ya ki ajiye makamansa zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Rahotanni sun ce daruruwan mutane ne suka nemi mafaka a wani sansanin Rasha a Latakia, wani hoton bidiyo ya nuna yadda mutane da dama ke yayata cewa suna neman Rasha ta kawo masu dauki.

Wasu da dama kuma a cewar rahotanni sun tsere zuwa Lebanon.

'Yan alawi wadanda mabiya Shi'a ne, ba su wuce kashi 10 ba na al'ummar Syria.