Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na nadama kan Rashford, AC Milan ba ta son rabuwa da Modric
Manchester United na nadama kan matakin amincewa ta sayar wa Barcelona Ɗanwasan gaba na Ingila Marcus Rashford kan fam miliyan 26 inda take ganin yanzu darajarsa ta kai fam miliyan 50. (Star)
Ɗanwasan baya na Bournemouth da Argentina Marcos Senesi, mai shekara 28, na son zuwa Barcelona a wannan bazara bayan yanke shawarar ba zai tsawaita kwangilar shi ba. (Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Ingila Liam Delap, mai shekara 23, akwai alamun zai bar Chelsea a wannan bazara matakin da ya sa Manchester United da Newcastle da Everton ke rubibinsa. (Caughtoffside)
Manchester United a shirye take ta raba gari da ɗanwasan gaba na Ingila Jadon Sancho idan an kammala kaka. (Sun)
Tottenham za ta kashe kuɗi a wannan bazara domin cefanen yanwasa ciki har da ɗanwasan tsakiya na Aston Villa da Ingila Morgan Rogers. (Football Insider)
Amma ɗanwasan gaba na Tottenham Richarlison zai iya tafiya inda Flamengo da Atletico Madrid ke farautarsa. (Fichajes - in Spanish)
AC Milan na da ƙwarin guiwar ɗanwasan tsakiya na Croatia Luka Modric mai shekara 40 zai amince ya tsawaita yarjejeniyarsa zuwa shekara ɗaya. (Calciomercato - in Italian)