An kama manyan jami'an Ukraine kan zargin cin kuɗin makamai

Asalin hoton, Getty Images
An kama wani dan majalisar dokokin Ukraine da wasu sauran jami'ai bayan da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasar suka bankado abin da suka kira wata babbar badakalar almundahana wajen sayen kananan jiragen yaki na sama marassa matuka da wasu kayayyakin yaki na laturoni.
A wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X, Shugaba Volodymyr Zelensky, ya bayyana lamarin a matsayin babban abin kunya.
Ya ce an bankado danmajalisa, da shugabannin gundumomi da birane da jami'an rundunar tsaron cikin gida ta kasar kan irin hannun da suke da shi a badakalar, da ta kai ana kara kudin kwangilar da wajen kashi talatin cikin dari.
Zelensky ya ce ko kadan ba za a lamunta da rashawa ba a Ukraine, yana mai godiya ga hukumomin da suka bankado cuwa-cuwar.
A ranar Alhamis ne aka mayar wa da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasar ta Ukraine 'yancin kansu bayan korafi da zanga-zangar da aka yi ta yi a fadin kasar.
Gwamnatin Shugaba Zelensky ta sha suka bayan da ta bullo da wani kudurin doka da zai raba hukumomin yaki da rashawa na kasar 'yancin kansu.
Shugaban ya yi ikirarin cewa hukumomin na bukatar kawar da su daga tasirin Rasha, kuma ya nemi bai wa babban mai gabatar da kara na kasar ikon yanke hukunci kan wanda za a gurfanar gaban shari'a a manyan batutuwan da suka shafi rashawa.
'Yan kasar da dama sun kalli hakan a matsayin wani koma-baya kan yaki da rashawa a Ukraine, abin da ya kai ga gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati, tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar kasar a shekarar 2022.
Wannan ya sa shugaban ya yi la'akari da koken na jama'a, inda ya gabatar da wani kudurin da ya mayar wa da hukumomin 'yancin zaman kansu, wanda majalisar dokoki ta amince da shi.
Babbar hukumar ma'aikatar kula da harkokin leken asiri ta kasar ta yaba da matakin shugaban kasar na jin koke da korafin jama'a a kan ikon hukumomin yaki da rashawar.
Haka su ma kawayen Ukraine na Tarayyar Turai wadanda suka nuna damuwarsu kan yunkurin raba hukumomin da 'yancin kansu, sun yaba da matakin shugaban.
Batun yaki da rashawa abu ne da yake da muhimmanci sosai a yunkurin kasar na shiga Tarayyar Turai.
Kirkirar hukumomin wani sharadi ne da hukumar gudanarwar kungiyar ta EU da Asusun bayar da lamuni na duniya – IMF suka gindaya a 2014, domin samun sassauta sharudan bayar da biza.
A sanadiyyar hakan kungiyar ta Turai ta bai wa Ukraine matsayin mai neman shiga kungiyar a shekara ta 2022, wanda hakan ya kara kusantar da ita ga kasashen Yamma.











