Wane tasiri matakin Amurka na daina bai wa Ukraine makamai zai yi?

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na dakatar da bayar da tallafin soji ga Ukraine babban abin damuwa ne ba ga Ukraine ɗin kawai ba, har ma da ƙawayenta na nahiyar Turai waɗanda suke ta bibiyar Amurkar domin shawo kanta ta ci gaba da taimakon da take yi.

Wannan ba shi ne karo na farko da Amurka ke ɗaukan matakin daina bayar da tallafin soji ba. Ƴaƴan jam'iyyar Republican a majalisar wakilan Amurka sun taɓa daƙile yunƙurin tsohon shugaban ƙasa Joe Biden na tuira makamai zuwa Ukraine a shekarar 2023.

A wancan lokaci sai dai Ukraine ta yi amfani da abin da ke hannunta na makamai da kuma ɗan tallafin da ta samu daga ƙasashen nahiyar Turai.

Sai a cikin 2024 ne majalisar dokokin ta Amurka ta amince da tallafin kayan aikin sojin na fam biliyan 60.

Faɗuwa ta zo daidai da zama a lokacin, inda Ukraine ke ƙoƙarin ganin ta kare kanta daga samamen da Rasha ta ƙaddamar kan birnin Kharkiv. Isar makaman na Amurka sun taimaka wa Ukraine a wancan lokacin.

Kamar a 2024, zai iya ɗaukan watanni kafin matakin Amurka na dakatar da bai wa Ukraine makaman ya yi tasiri sosai - musamman a ɓangaren bindigogi da makamai.

Ƙasashen Turai sun haɓɓaka ƙera makaman atilare a hankali.

A jimilla, Ukraine na samun kashi 60% na tallafi ne daga ƙasashen Turai - fiye da Amurka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai tallafin Amurka na da matuƙar muhimmanci ga Ukraine.

Ƙarfin da Ukraine ke da shi na kare kanta daga hare-hare ta sama ya dogara ne kan na'urorin kariyar sararin samaniyana Amurka.

Amurka ta bai wa Ukraine ikon kai har-hare masu nisa - ta hanyar amfani da makaman HIMARS da ATACM.

Amurka ta taƙaita yadda za yi amfani da makaman a cikin Rasha, to amma sun taimaka wajen kai farmaki kan muihimman wurare a cikin yankunan da aka mamaye.

Baya ga inganci akwai kuma batun yawa. A matsayinta ta ƙasa mafi ƙarfin soji a duniya, Amurka ta tura wa Ukraine motocin sulke da tankokin yaƙi masu matuƙar yawa - irin waɗanda ƙasashen Turai da dama ba su da su.

Za a ɗauki lokaci kafin matakin na Amurka ya shafi abin da ke faruwa a fagen daga, amma akwai wani abin damuwar da za a iya fuskanta a yanzu, ɗaya daga ciki shi ne raguwar bayanan sirri.

Babu wata ƙasa da ta ƙai Amurka ƙarfin kariya ta sararin samaniya, da tattar bayanan sirri, kuma ba Amurka kaɗai ke samar da waɗanan ba har ma da wasu ƴan kasuwa.

...

Asalin hoton, Reuters

Misali, samar da intanet na kamfanin Starlink na Elon Musk. Kowane fage daga da Ukraine ke fafatawa akwai farantin intanet na Starlink.

Ana amfani da su wajen isar da saƙonni kan abubuwan da ke faruwa a fagen daga. Sun taimaka sosai wajen tsara hare-haren atilare da na jirage marasa matuƙa.

A baya, ma'aikatar tsaro ta Amurka ta bayyana cewa tana zuba kuɗi a ɓangaren. Ganin cewa yanzu Elon Musk amini ne ga Trump, zai yi wahala ya ci gaba da aikin. Sannan kuma shi kansa Musk ya kasance yana sukar shugaban na Ukraine.

Ko Amurka za ta hana ƙasashen Turai tura makamansu da aka ƙera a Amurka zuwa Ukraine?

A lokacin da ƙasashen Turai suka yi niyyar tura wa Ukraine jirgin yaki ƙirar F-16, ba su yi hakan ba sai da suka nemi izinin Amurka.

Sannan kuma me zai faru da kulawa da kuma gyare-gyaren kayan yaƙin Amurka da ta bai wa Ukraine a matsayin tallafi? Haka nan Amurka ce ta riƙa horara da sojojin Ukraine kan yadda za su kula da irin waɗannan makamai.

Fatan ƙasashen Turai shi ne wannan dakatarwa ta zama ta wucin-gadi. Matuƙar babu tallafi daga Amurka, ci gaba da wanzuwa zai zama wani babban ƙalubale ga Ukraine.