Ukraine za ta iya sallama wa Rasha Crimea - Trump

Asalin hoton, Ukrainian Presidential Press Service
Shugaba Trump na Amurka ya ce yana ganin a shirye takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky yake ya amince ya sallama yankin Crimea ga Rasha don cimma zaman lafiya.
A baya shugaban na Ukraine ya sha nanata cewa ba zai sallama yankin da Rashar ta kwace a 2011 ba.
Kazalika shugaba TrumP ya kuma roki Shugaba Putin na Rasha ya dakatar da bude wuta ya dawo teburin sulhu da kulla yarjejeniya, wani abu da ya ce ana iya cimmawa cikin makwanni biyu.
Trump ya yi wadannan kalamai ne a lokacin ganawa da manema labarai bayan ya koma Amurka daga Vatican, inda ya yi wata 'yar ganawa da takwaran nasa na Ukraine, Shugaba Zelensky kafin jana'izar Fafaroma Francis.
Trump ya ce wannan ganawa ta wakana da kyau, kuma sun tattauna ma a kan batun Crimea, yankin da Rasha ta mamaye shekara 11 da ta wuce.
Ita dai Ukraine ba sau daya ba ba kuma sau biyu ba ta sha nanata kin yardarta tare da yin watsi da maganar sallama wani yankin kasarta ga Rasha, tana mai jaddada cewa duk wani batu da ya shafi kasa za a tattauna shi ne kawai bayan an amince da dakatar da bude wuta.
Ba dai wanda ya ce komai game da kalaman na Trump – tsakanin Shugaba Zelenskyn na Ukraine da kuma Shugaba Putin na Rasha.
Tun da farko a ranar Lahadi ministan tsaro na Jamus Boris Pistorius, ya gargadi Ukraine da kada ta sake ta yarda da wata yarjejeniya da ta kunshi sallama wasu yankunan kasarta, domin kawai a dakatar da bude wuta.
Ministan na Jamus ya gaya wa kafar yada labarai ta kasarsa ARD, cewa a kada a raya, kada Kyiv ta sake ta amince da shawarar shugaban Amurkan ta yanzu – wadda y ace amincewar tamkar mika wuya ne Ukraine din ta yi – wanda idan ta sake ta yi shikenan sai buzunta.
To amma kuma Mista Pistorious, ya ce, Ukraine daman ta kwan da sanin cewa za ta iya rasa wasu yankunanta, don cimma yarjejeniyar dakatar da yakin.
Amma ya ce kada ta sake ta zura jiki a kan hakan ta yarda da shawarar da shugaban na Amurka ya gabatar ta yanzu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A makon da ya gabata Trump ya ce, na amince da yawancin muhimman batutuwan da yarjejeniyar ta tanada.
Rahotanni na nuna cewa kila a bukaci Ukraine ta hakura da yankuna da dama da Rasha ta kwace, ciki har da yankin Crimea.
BBC dai ba ta ga ainahin cikakken bayanin da shirin na Amurka na yanzu ya kunsa ba.
To amma a ranar Juma'a kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya bayar da rahoton cewa, shi ya ga bayanan na Amurka – wadanda suka hada da amincewa a hukumance da kwace mata Crimea da kuma yarda da ikon Rasha a kan sauran yankunan da ta mamaye, da suka hada da dukkanin kasar Luhansk da ke gabashin kasar.
Kamfanin da Reuters ya kuma ce ya ga yarjejeniya ta martanin Turai da Ukraine – da ke cewa bangarorin za su tattauna ne kawai a kan makomar yankuna da Rasha ta kama bayan an dakatar da bude wuta.
Haka kuma shawarar ta Amurka ta kawar da maganar Ukraine shiga kungiyar tsaro ta NATO, da kuma kasancewar hadakar da za ta kasance karkashin jagorancin Birtaniya da Faransa a matsayin wadda za ta bayar da kariyar tsaro – da Zarar an cimma dakatar da yakin, amma ba tare da shigar Amurka hadakar ba.
To amma kuma a halin da ake cikin kasashen Turai na son Amurka ta yi alkawari tare da bayar da tabbacin cewa lalle za ta taimaka wa Ukraine muddin aka kai mata hari.
Haka kuma rahotanni sun ce yarjejeniyar da Amurka ta gabatar ta kuma kunshi cewa , ita Amurkar za ta karbi iko da katafariyar tashar nukiliya ta Zaporizhzhia, wadda Rasha ta karbe iko da ita daga Ukraine, inda daga nan za ta rika samar da wutar lantarki ga Ukraine da kuma Rasha.
Amma kuma a tsarin daya bangaren na Turai da Ukraine babu maganar bai wa Rasha lantarki daga wannan tasha.
A wata tattaunawa da ya yi da mujallar Times, a baya-bayan nan Shugaba Trump ya sake dora alhakin barkewar yakin a kan Ukraine – saboda abin da ya kira burinta na shiga kungiyar Nato.
A wanannan tattaunawa Trump ya ma ce Crimea za ta ci gaba da kasancewa a hannun Rasha.
A jiya Lahadi Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya bukaci Rasha da Ukraine su kara azama domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Yana mai kara nanata cewa Amurka za ta fice daga yarjejeniyar idan ta ga ba wani ci gaba.
A shekara ta 2022 ne Rasha ta kaddamar da cikakken yakin mamayar Ukraine kuma a yanzu haka tana rike da kusan kashi 20 cikin dari na kasar ta Ukraine.











