Dalilin da ya sa Trump bai ƙaƙaba wa Rasha sabon haraji ba

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Vitaliy Shevchenko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Russia editor, BBC Monitoring
- Lokacin karatu: Minti 2
Wata ƙasa da ba ta cikin jerin ƙarin ƙarin harajin Donald Trump ita ce Rasha.
Kafar yaɗa labarai ta Axios a Amurka ta ambato wmai magana da yawun fadar White House, Karoline Leavitt, na cewa hakan ta faru ne saboda takunkuman da Amurka ta saka wa Rasha a yanzu "sun hana yin kasuwanci" tsakaninsu.
Ta ƙara da cewa babu ƙasashen Cuba, da Belarus, da Koriya ta Arewa ba su cikin jerin.
Sai dai kuma, akwai ƙasashen da ba su yin wani kasuwancin kirki da Amurkar - kamar Syria da ta kai kayan dala miliyan 11 kacal a 2024 - na cikin jerin.
Amurka ta ƙaƙaba wa Rasha takunkumai bayan mamayar da ta yi wa Ukraine a 2022. Trump ya fara nuna abota a kan Rasha tun bayan da ya koma mulki wa'adi na biyu.
Ya ci alwashin kawo ƙarshen yaƙin na Ukraine kuma wani babban jami'in Rasha na birnin Washington domin tattaunawa kan hakan yayin da ake lalubo hanyoyin sasanta rikicin.
A watan da ya gabata, Trump ya yi barazanar lafta wa ƙasashen da ke sayen man Rasha ƙarin haraji na kashi 50 cikin 100 idan Shugaba Putin ya ƙi amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.
A ranar Alhamis, wata kafar yaɗa labarai a Rasha ta ce ba a saka ƙasarsu cikin jerin ba ne saboda takunkuman da ke kan ta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ba a saka ƙarin haraji ba kan Rasha, amma ba wai saboda wani dalili na musamman ba ne. Sabda da ma can akwai takunkuman ƙasashen Yamma a kan ƙasarmu," a cewar tashar talabijin ta Rossiya 24 TV mallakin gwamnatin Rasha.
A cewar wata tashar ta Rasha, Rossiya 1, ƙasashen Yamma da yawa "ba su ji daɗin rashin ganin Rasha a cikin jerin ba".
Kafofin yaɗa labarai da gwamnatin Rasha ke iko da su na yawan ambato kalaman sakataren kasuwanci na Amurka, Scott Bessent, wanda ya faɗa wa Fox News cewa: "Rasha da Belarus ba mu kasuwanci da su. Akwai takunkumai a kansu."
A cewar hukumar kasuwanci ta Amurka, Amurka ta sayo kaya daga Rasha da suka kai darajar dala biliyan 3.5 a 2024. Akasari takin zamani ne, da man tafiyar da nukiliya, da wasu ƙarafa, a cewar alƙaluman Trading Economics da kuma kafar yaɗa labaran Rasha.
Wasu kafofin labaran kuma sun dinga tsokanar Amurka ne, inda NTV - wadda ke goyon bayan gwamnati - ta ce Trump ya mayar da ƙawayen Amurka a Turai kamar "leburori" waɗanda ba su iya komai ba "sai gunaguni".
Kafar talabijin ta Zvezda TV da ma'aikatar tsaro ke gudanarwa ta yi magana ne kan tsibiran Heard Island da McDonald Islands da aka saka a jerin, waɗanda babu mutanen da ke rayuwa a can.
"Da alama dabbobi ne za su biya wannan harajin na kashi 10," in ji Zvezda.
Ita kuwa Ukraine, an ƙaƙaba wa kayan da take shigarwa Amurka ƙarin kashi 10 cikin 100.
Mataimakiyar firaminista ta farko na Ukraine, Yulia Svyrydenko, ya ce harajin zai fi shafar ƙananan 'yan kasuwa.
A 2024, Ukraine ta shigar da kayan da suka kai darajar dala miliyan 874 Amurka, kuma ta sayo kayan dala biliyan 3.4 daga can, in ji mataimakiyar firaministan.
"Ukraine na da abubuwan da za ta bai wa Amurka a matsayinta na babbar ƙawa," a cewarta.
Duk da ƙarancin kasuwancin, Amurka ta bai wa Ukraine tallafi mai yawa game da yaƙin da take yi da Rasha.











