Shin ko Turai za ta iya kare kanta ba tare da Amurka ba?

Shugaba Volodymyr Zelensky da takwaransa na Amurka Donald Trump

Asalin hoton, Ukraine Presidential Press Service

Bayanan hoto, Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi kira a kafa rundunar soji ta Turai.
    • Marubuci, Rebecca Thorn
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce ya zama dole ƙasashen Turai su samar da kaso mai tsoka na tallafin da ake bai wa Ukraine domin ta kare kanta daga mamayar Rasha a ziyararsa ta farko da ya kai wasu ƙasashen duniya tun bayan da ya fara aiki. Sai dai ko me hakan yake nufi ga turai?

Kalaman na Mista Hegseth na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattaunawa tsakanin wakilan Rasha da Amurka a ƙasar Saudiyya, wanda wani abu ne da ke haska yadda tsarin Trump na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine zai kasance.

Mataimakin shugaban ƙasar Amurka JD Vance ya jadada buƙatar ganin cewa nahiyar Turai ta ƙara ƙaimi wajan ɗaukar nauyin tsaronta a taron ƙoli kan tsaro da aka yi a Munich a ranar Juma'a 14 ga watan Fabrairu, inda ya ce dole ne Turai ''ta tashi tsaye wajen tsare kanta''.

Yadda Amurka ta sauya manufarta ya tayar da hankalin shugabannin turai kuma wannan ne ya sa aka shirya taron gaggawa a ranar 17 ga watan Fabrairu a birnin Paris domin tattauna rikicin Ukraine da tsaron nahiyar.

Abun tambaya a nan shi ne -yaya Turai take dogaro da Amurka wajen tsaronta, kuma shin za ta iya kare kanta?

Dalilin da ya sa Amurka ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da Turai

Mambobin kasashen Nato

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wakilan mambobin ƙasashen NATO a taron ƙoli da aka yi a 1957 a birnin Paris

An kafa ƙungiyar tsaro ta NATO ce a shekarar 1949 domin hana tsohuwar Tarrayar Soviet faɗawa a Turai .

Amurka dai na ganin idan aka samu nahiyar turai mai ƙarfin tattalin arziki da ƙarfin soji, to wannan zai sa daƙile duk wani yunƙuri na faɗaɗa, kuma samar da tallafi ga ƙasashen Turai zai taimaka wajan sake gina nahiyar bayan ɓarnar da yaƙin duniya na biyu ya haifar.

A yanzu mambobin ƙasashen sun kai 32, ciki har da wasu ƙasashen gabashin Turai kuma sun amince da cewa idan aka kai wa wani daga cikinsu hari ya kamata sauran su tashi tsaye wajan kare ta.

Kawo yanzu Amurka na cikin Nato sai dai shugabannin turai na fargabar cewa ba za su iya dogara a kan Amurka wajan kawo mu su ɗauki ba.

Shin wani kaso ne ƙasashen Turai ke ba tsaro a kasafin kuɗinsu?

Sojojin Poland na sintirin tsaro a filin jirgin sama na Warsaw
a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2023

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Poland na cikin masu ba da tallafi mai tsoka a kasafin kuɗi domin tsaro na yankin

A yanzu ƙawancen na Nato ya nemi mambobinsa su kashe aƙalla kashi biyu na kuɗaɗen shigarsu domin samar da tsaro.

Alƙaluman Nato na shekarar 2024 sun nuna Poland ce a gaba a ƙasashen da suka fi bada da tallafi a shekara biyu a jere .

Estonia ita ce ta biyu da kashi 3 da ɗigo 4 inda Amurka ita ce ta uku da kashi uku da da ɗigo huɗu.

Birtaniya ita ce ta tara da kashi biyu da ɗigo uku

Shin ko Turai za ta iya kafa rundunar soja ta nahiyar?

Firayim Ministan Burtaniya Keir Starmer da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer ya ce a shirye yake ya tura dakarun ƙasarsa zuwa Ukraine.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dangane da yiwuwar janye tallafin na Amurka, shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi kira da a kafa rundunar soja ta Turai.

"Shugabani da dama sun yi magana a kan buƙatar ganin cewa Turai ta kafa rundunar sojinta," in ji shi.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya daɗe yana goyon bayan sojojin ƙungiyar don rage dogaro da Amurka, amma shugabar kula da harkokin wajen EU Kaja Kalas ta yi watsi da ra'ayin.

Richard Whitman, wanda farfesa ne a fannin siyasa da hulɗar ƙasa da ƙasa a jami'ar Kent, ya shaida wa BBC cewa, a daidai lokacin da mambobin ƙungiyar Nato na Turai ke da arzikin samar da wani gagarumin kariya daga ƙasashe irinsu Rasha, amma yadda za a tabbatar ne babban ƙalubale.

Tun bayan kafa Nato, babban hafsan sojan Amurka ne ke jagorantar ayyukan sojojin ƙungiyar, wanda wani abu ne da ya ba su damar samun ƙwarewa a ayyukan da suka shafi yaƙi.

Manyan sojojin Turai ba su da irin wannan ƙwarewar, in ji Farfesa Whiteman, sannan ya ce ''abu ne da zai sa a samu gibi a ayyukan rundunar ta turai."

Sojan Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojan Ukraine a fagen daga

Akwai kuma gibin da za a samu a bangaren siyasa idan Amurka ta janye.

"A bayyane ta ke cewa bayan kayan yaki da mu ke samu daga hannun Amurka tana kuma da karfin fada a ji ta fuskar siyasa , ba mu da irin wannan a turai . in ji shi

Abu ne da ake ganin zai iya haifar da gwagwarmayar iko da kuma wanda zai jagoranci tsarin tsaro na Turai

Faransa da Birtaniya a matsayinsu na manyan aminan tsaro na turai za su iya zama kan gaba wajan amfani da wannan dama tare da jagoranci a cewar Farfesa Amelia Hadfield malama a jami'ar Surrey.

Amma akwai bukatar ganin cewa sun yanke shawara a kan yadda za a raba kuɗin da ake kashewa kan tsaro tsakanin ƙasashe da kuma wanda zai ɗauki alhaki mafi girma.

Me hakan yake nufi ga makomar Turai

 Shugaba Emmanuel Macron da Firai Ministar Denmark Mette Frederiksen a taron gaggawa da aka yi a birnin Paris

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Emmanuel Macron da Firai Ministar Denmark Mette Frederiksen a taron gaggawa da aka yi a birnin Paris

Gibin da ke cikin tsarin sojin turai ya sa wasu na nuna damuwa kan barazanar ficewar Amurka daga ayyuikan tsaro na Nato.

"Abu ne mai wuya ayi tunanin tsaron turai ba tare da Amurka ba ," in ji Farfesa Whitman.

Wasu sun nuna damuwa matuka kan ko Rasha za ta gwada anniyar Amurka na maida hankalinta zuwa wasu wurare.

"Abin takaici ne a ce mutane za su saba da tunanin da ake yi a kan cewa za a yi kaca-kaca da Ukraine kuma dole su sake ginata, amma ba sa tunanin cewa Rasha kan iya kai wa Sweden ko Poland ko Ingila hari ba''. in ji Farfesa Hadfield.

"Ya zama dole kuma cikin gaggawa Nato ta fahimci makomarta ba tare da wata mamba da suka kafa kawancen tare ."