Yadda yaƙi a ƙasashen Larabawa ya hana miliyoyin yara zuwa makaranta

    • Marubuci, Suha Ibrahim
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Arabic
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da aka shiga sabuwar shekarar karatu, miliyoyin yara ne a ƙasashen Larabawa ba za su koma makarantun ba kamar sauran takwarorinsu na ƙasashen duniya.

BBC ta ga rahoton asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef) da ya bayyana tasirin da yaƙi ya yi kan karatun yaran a Lebanon da Libya da yankunan Falasɗinawa da Sudan da Syria da kuma Yemen.

Rahoton ya yi gargaɗi game da matsalar ta tsawon lokaci da hakan zai haifar idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba.

Sama da rabin yaran yankin na fama da matsalar "ƙarancin ilimi", ta yadda ba su iya karanta litattafan yara 'yan ƙasa da shekara 10.

An yi ƙiyasin cewa yara miliyan 15 da suka isa zuwa makaranta (shekara 5 zuwa 14) ba su zuwa makarantar, sannan wasu miliyan 10 na cikin haɗarin daina zuwa.

"Manyan yaƙe-yaƙe biyu a Gaza da Sudan sun jawo babbar buƙatar gaggawa ta kai agaji game da koyo da koyarwa, ciki har da lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma tunanin ɗan'adam," a cewar Averda Spahiou, ƙwararre kan ilimi na Unicef a yankin Gabas ta Tsakiya cikin wata sanarwa.

Gaza: Ƙarni guda maras ilimi

Tsawon shekaru, ɗalibai a Falasɗinu sun sha fama da ƙalubale wajen samun ilimi mai inganci, amma ƙaruwar tashin hankali bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023 kan kudancin Isra'ila ya ta'azzara matsalar koyo da koyarwa zuwa matakin da ba a taɓa gani ba, kamar yadda ƙungiyoin agaji ke bayyanawa.

A cewar wani rahoto a watan Agustan 2024 da cibiyar International Education Cluster ta fitar, akwai buƙatar ƙaddamar da wani shiri da hukumomi za su bi wajen shawo kan matsalar.

Matsalar a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye ta ƙunshi "kai wa malamai da ɗalibansu hari da ayyukan soji na rundunar sojin Isra'ila da samamen da rundunar ke kai wa a kai da kuma kusa da makarantu, da hare-haren Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna, da lalata wuraren karatu, da hana zirga-zirga, da kuma tsaikon da tsare-tsaren gwamnati ke kawowa".

Zirin Gaza na fuskantar "yanayi mai muni game da ilimi, yayin da yaƙi ya hana yara 625,000 da suka isa zuwa makaranta da sauran wuraren koyar da ilimi," a cewar rahoton Unicef da BBC ta gani.

Kusan kashi 93 na makarantu 564 aka lalata, inda kashi 84.6 ke buƙatar a sake gina su baki ɗaya, in ji rahoton.

Ya ƙara da cewa tasirin da yaƙin ke yi ya munana.

Aƙalla ɗalibai 39,000 ne ba su rubuta jarabawar Tawjihi ba ta kammala sakandare, sannan malamai fiye da 21,000 ba su iya gudanar da ayyukansu ba saboda matsalar tsaro a wuraren koyarwar.

Rahoton ya nuna cewa dukkan yara miliyan 1.2 a Gaza na buƙatar kulawar gaggawa game da tunaninsu.

Ilimi na shirin ɓalɓalcewa a Sudan

Shafin Unicef na dandalin X - wato Twitter a baya - ya wallafa bidiyon da ke ɗauke da mai magana da yawunsa a cikin wata makaranta da ke Khartoum babban birnin Sudan, inda aka gan shi yana tafiya a tsakiyar wasu yara suna barci a ƙasa a gefe guda kuma ana jin ƙarar harbe-harbe.

James Elder ya ce: "Abubuwan da ke faruwa a Sudan masu tayar da hankali ne. An tilasta wa miliyoyin yara guduwa daga Sudan, kuma ana ta kai musu hare-hare a kullum tsawon wata 16 yayin da ƙasashen duniya ke ji suna gani."

Fannin ilimi a Sudan na fuskantar rushewa gaba ɗaya, inda sama da yara miliyan 19 ne ba su zuwa makaranta, miliyan 12.5 daga cikinsu na gudun hijira.

Idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, asarar kuɗi da ta ilimi da wannan ƙarnin zai yi za ta kai dala biliyan 26 duk shekara, in ji Averdita Spahiou.

Ta ƙara da cewa lamarin kan ƙara ta'azzara sauran abubuwa kamar bautar da yara, da auren wuri da saka yaran aikin soja.

Mazauna Sudan na cikin matsanancin yanayi na talauci musamman saboda yaƙin da ake tafkawa tsakanin ƙungiyar Rapid Support Forces da kuma sojin gwamnatin ƙasar sama da shekara ɗaya.

Tsarin ilimi a Yemen ya girgiza

Rahoton ya siffanta tsarin ilimi a Yemen a matsayin wanda ya ɗaiɗaice, yana mai cewa yara miliyan 2.7 ne ba su zuwa makaranta, sai kuma 8.6 da ke buƙatar tallafi don ci gaba da zuwa makarantar, da makarantu 2,800 da aka rusa ko aka lalata ko aka mayar da su wurin yin wani daban.

Tsawon shekaru, Yemen na cikin yaƙin basasa da ya kashe dubun dubatar fararen hula. A cewar MDD, halin matsin da ake ciki a Yemen na cikin mafiya muni a duniya, inda fiye da rabin 'yan ƙasar miliyan 33 ke buƙatar agaji.

Wani rahoto na ofishin tattara tallafi na MDD ya ce duk da raguwar tashin hankali da kuma raguwar mutuwar fararen hula, yawan mutanen da aka raba da muhallansu da zalinci na cigaba da taɓa rayuwar 'yan ƙasar baki ɗaya.

Halin da yara ke ciki a Libya

A Libya, rashin zaman lafiyar da ake ciki ta jawo matsaloli kan koyo da koyarwa, musammana tsakanin yara.

Rahoton ya ce lamarin ya jawo ƙarancin yaran da ake sakawa a makaranta musamman tsakanin masu gudun hijira, inda aƙalla kashi 11 na iyalai suka ce yaransu da suka isa ba su zuwa makaranta a shekarar karatu ta 2021/2022.

Bugu da ƙari, akwai yara sama da 175,800 da ke cikin haɗari da kuma neman agaji, yayin da kusan 111,400 ke gab da rasa ilimin gaba ɗaya idan ba a ɗauki mataki ba cikin gaggawa.

Libya ba ta sake ganin zaman lafiya ba tun bayan tarzomar da ta kawo ƙarshen mulkin Muammar Gaddafi a 2011, wanda hakan ya jawo rabuwar ƙasar gida biyu zuwa gabas da yamma a 2014.

An kawo ƙarshen yaƙin ne da yarjejeniyar tsagaita wuta a 2020, kuma har yanzu ana ƙoƙarin haɗa kan ƙasar amma hakan bai yiwu ba.

Buƙatar gaggawa

Unicef ya jaddada buƙatar samar da hanyar koyar da yara a yankunan da lamarin ya shafa.

Ya kuma ba da shawarar gina azuzuwa, da samar da ruwan sha mai tsafta, da ba da tallafi game da lafiyar ƙwaƙwalwa domin taimaka wa ɗalibai da malamai wajen yaƙi da wahalhalun da yaƙi ya jefa su.

Yayin da ake ci gaba da tashe-tashen hankalin, rahoton ya nanata buƙatar gaggawa ga ƙasashen duniya domin kauce wa rushewar ɓangaren ilimi gaba ɗaya da zai iya yin mummunan tasiri ga miliyoyin yara da yankunansu.