Wasannin Champions League da za su ja hankali

Asalin hoton, EPA
Zuwan Liverpool filin wasa na San Siro domin taka leda da AC Milan wani wasa ne da ake yi wa kallon mai zafi da zai ɗauki hankalin ƴan kallo a daren nan.
Ƙungiyoyin biyu dai sun haɗu har sau biyu a wasan ƙarshe, inda Liverpool ta doke AC Milan a dukkan daga kai sai mai tsaron gida a Istanbul a 2005, kafin ita kuma Milan ta ɗauki fansa a 2007 inda ta ci Liverpool ɗin da 2-1 a Athens.
To sai dai wani abin sha'awa shi ne yadda kungiyoyin biyu suka kai wasanni ƙarshe a gasa 21 na Gasar wasannin Turai da ta Zakarun Turai wato Champions League, inda Milan ta ɗauki kofi sau bakwai ita kuma Liverpool ta ɗauka sau shida. Kuma dukkannin ƙungiyoyin sun zo na biyu a lokuta huɗu daban-daban.
Sauran wasannin da za a buga ranar Talata:
Real Madrid v Stuttgart
Real Madrid ta kara da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Jamus 15 a wasannin gasar Turai kawo yanzu to amma wannan ne karon farko da za su taka leda da ƙungiyar Stuttgart.
Ita kuma Real Madrid ta taɓa rashin nasarar a wasanninta na ƙarshe guda 21 da ta buga da kungiyoyin ƙwallon Jamus (W14 D6), kuma ɗaya daga cikin rashin nasarar shi ne tsakanin Real Madrid ɗin da RB Leipzig a gasar UEFA Champions League a watan Oktoban 2022 inda aka tashi wasan 2-3.
Juventus v PSV
Wannan ne zai zama karo mafi zafi tsakanin Juventus da PSV Eindhoven, tun bayan da Juventus ɗin ta yi na ƙarshe da Ajax a gasar UEFA Champions League 2018-19 inda aka tashi wasa 1-2.
Bayern Munich v Dinamo Zagreb
Wannan ne zai zama karo na biyar da Bayern Munich ke haɗuwa da Dinamo Zagreb a wata gasar Turai.
Ƙungiyoyin biyu sun haɗu a 1962-63 a gasar wasanni ta Inter-Cities Fairs Cup inda Dinamo ta samu nasara da ci 4-. A baya-bayan nan kuma sun sake haɗuwa a gasar wasan rukuni na UEFA Champions League ta 2015-16, inda Bayern ta samu nasara a kan Dinamo a gida da waje.
Young Boys v Aston Villa
Wannan ne karon farko da Young Boys za ta kara da Aston Villa. Young Boys na Swiss ta samu nasara sau bakwai a haɗuwa 24 na baya-bayan nan da ta yi da ƙungiyoyi daga Ingila a gasar UEFA Champions League, kuma Basel ce ta samu ɗaya daga cikin nasarori guda bakwai (sannan Young Boys ta samu ɗaya).
Sporting Lisbon v Lille
Su kuwa Sporting CP da Lille sun taɓa haɗuwa sau biyu kacal a wasannin gasar Turai inda kulon ɗin na ƙasar Portugal ya samu nasara da ci 1-0 a gida da kuma ci 2-1 a waje a wasan rukuni na gasar Europa League ta 2010-11.
Lille ta ci wasanta na farko a waje a lokacin haɗuwarsu da Sporting CP a gasar Turai ta EUPA Intertoto Cup a watan Agustan 2004 inda aka tashi 2-1. To amma dukkannin ƙungiyoyin ba su yi nasara ba a wasannin da suka buga ba a gidansu ba inda kowane ɓangare bai saka ƙwallo ko ɗaya ba.











